whats app
YADDA ZAKA KARA ADMIN A WHATSAPP
Kamar yadda masu amfani da dandalin WhatsApp suka sani, shi ne mutum yana iya bude group, ko kuma wata kungiya ta bude Group acikin WhatsApp, amma mafi yawa basa sanin yadda zaka kara admin fiye da daya a dandalin, ga hanyar da ake bi ka kara admins fiye da daya.
1. Dole ya zama kana da WhatsApp account
2. Dole ya zama kana da Group wanda zaka kara admin.
Idan ka cika wannan ka'ida ta sama saika bi wadannan matakan na kasa dan kara admin ko abokin aiki acikin group din
1. Ka bude WhatsApp dinka
2. Ka bude Group dinka na WhatsApp, wanda kasan kaine admin dinsa.
3. Saika latsa ''Option''
4. Ka zabi ''Show Group Info''
Anan zai nuna maka duk yawan members da suke cikin Group dinka, saika je kan wanda kake son ka sa shi a admin, saika latsa ''Option'' akan sunansa, saika zabi. ''Make Group Admin'' shi kenan wanda kasa ya zama admin zaka iya sa admin fiye da biyar a WhatsApp.
Comments
Post a Comment