ALALEN DANKALI

ALALEN DANKALI

INGREDIENTS:

•Dankalin turawa

•Hanta da sauran kayan ciki/ko kaza, ko naman sa ko na rago

duk wanda kike dashi

•Curry, Maggi, gishiri

•Tattasai, tarugu, albasa, tafarnuwa

•'Kwai

•Mai, citta.

PROCEDURE


Ki wanke dankali, ki sa a ruwa ki dafa shi, idan ya dahu sai ki
barshi ya huce, idan ya huce sai ki 'bare bawon ki farfasa
dankalin.


Daga nan sai ki sami tattasai da tarugu da isasshen albasa da
tafarnuwa ki daka sosai, sai ki sa a frying pan ki soya shi, ki
sa mai maggi, gishiri, curry da sauran su.


Daga nan sai ki sami tafasasshen kayan cikin nan ki yayyanka
su 'kanana, sai ki juye a kan dankalin, nasan akwai ragowar
ruwan tafasan da kika dafa naman, sai ki zuba kamar ludayi
biyu, za ki iya zuba mangyada rabin ludayi a cikin ruwan
tafasar, kafin ki zuba.


Shi ma kayan miyan ki juye akan dankalin, sannan ki sami
'kwai kamar biyu ki dafa su, idan sun dahu sai ki yayyanka su
'kanana ki juye a cikin dankalin.


Daga nan sai ki sami 'kwai wanda zai sa kwabin yayi ruwa-
ruwa, ba fa yayi ruwa tsululu ba yayi kauri sosai, sai ki kada
'kwan a kwano, ki sami citta wanda yayi lukui-lukui ki zuba
kadan a ciki ki juye a cikin hadin dankalin.


Zaki iya 'dandana maggin da gishirin kafin kisa 'kwan idan
bai ji ba sai ki 'kara, sai ki juya kwabin sosai ya hadu.


Sai ki sami leda santana ki rinka sawa kadan-kadan kina
'kullawa, sai kisa ruwan idan yayi zafi sai ki zuba su dahu,
bayan ya dahu sai ki sami ruwa mai sanyi ki zuba a ciki, zaki
ga yayi 'karfi, sai ki kwashe, kada fa ki barshi ya dade a
ruwan saboda kada ya huce.

Yana da dadi sosai, musamman bayan Maigida ya dawo
sallar Isha, kun san basa bukatar abinci mai nauyi sosai,
saboda an riga anyi ciye ciye da Magrib. Sai ki gabatar masa
wannan danasha.

Hajiya da kanki zaki bani labarin kallon soyayyar da kika sha
sanadiyyar wannan girkin. Lol!

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH