KOSAN FULAWA

KOSAN FULAWA


KAYAN DA ZA KI TANDA


1. Fulawa
2. Kifin gwangani
3. Albasa
4. Attaruhu
5. Yis (yeast)
6. Mai
7. Gishiri
8. Dunkulen knorr

YADDA ZA KI HADA

Ki sami fulawarki ki tankade, sai ki zuba yis a ciki, ki sami ruwan dumi ki zuba domin ki kwaba, za ki yi kwabin ne amma ba da tauri ba, kamar dai kwabin fanke. Sai ki saka shi a rana ko kuma waje mai dum,i idan lokacin sanyi ne domin ya tashi. Idan ya tashi za ki ga ya kumburo ya ninka kwabin da kika yi yawa. Sai ki kawo kifin gwangwani mai mai ki zuba, ki yanka albasa ki jajjaga attaruhu da gishiri da dunkulen knorr ki zuba, Sai ki saka cokali ki juya sosai. A gefe daya kuma kin dora man ki a kan wuta , idan ya yi zafi sai ki ringa diban wannan kwabin da hannu ko da cokali kina soyawa a cikin mai, idan ya yi sai ki kwashe daga cikin man ki bar shi ya tsane.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH