Ni Na Kawo Buhari Siyasa —Maryam Abacha
Ni Na Kawo Buhari Siyasa —Maryam Abacha
Ba kasafai take magana da ‘yan jarida ba. Tun daga lokacin da maigidanta ya rasu a shekarar 1998 rayuwarta ta kasance cikin tsanaki, da farko a Kano yanzu kuma a Abuja. A wannan tattaunawar da ta yi da Mujallar TELL wadda aka buga a jaridar PM NEWS (Mallakin TELL) ranar 4 ga Afrilun 2014, Hajiya Maryam Abacha ta yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi kasa da ma kasashen waje tare da yn waiwaye kan rayuwar marigayin Shugaban Kasan Saliyo, Tejan Kabbah wanda maigidanta Janar Sani Abacha ya maida shi kan mulki a 1998. Wakilinmu Abdulrazak Yahuza Jere ya fassara tattaunawar kamar haka:
Hajiya, yaya rayuwa take kasancewa tun bayan rasuwa maigidanki?
Alhamdulillah, muna godiya ga Allah bisa ni’imar da ya yi mana. Muna kuma godiya ga wadanda suka kasance tare da mu lokacin da muke cikin alhini. Har yanzu kuma ba mu yi fushi da kowa ba; muna sauraren wadanda suka guje mu su fahimci kuskurensu su dawo. Ba mu gaba da kowa, kowa namu ne. Muna rokon Allah ya ba mu hakurin jure rashin da muka yi. Rayuwa na gudana cikin kwanciyar hankali, iyalai a dunkule suke kuma kowa na cikin farin ciki da annashuwa.
Comments
Post a Comment