Lokacinda Annabi (s a w) yana dan shekara daya yaci gaba da nunawa al'umma abun al'ajabi.

Lokacinda Annabi (s a w) yana dan shekara daya yaci gaba da nunawa al'umma abun al'ajabi.

Watarana halimatu sadiya tagoyashi abayanta suka fita cikin jeji gurin neman itacen da zatayi girki dashi,
sai yahudawa suka zagayesu sukace wannan yaron yau sai mun kasheshi suka zare takobinsu a hannun su.

Halimatu sadiya zata fara rusa kuka sai Annabi (s a w) yabuda bakinsa yace karkiyi kuka ajiyeni akasa,
hakan kuwa akayi tana ajiyeshi sai yadaga kansa sama bakinsa yana motsi nan take sai wuta mai tsananin zafi tasauko daga sama ta kashe dukan yahudawan.

Wannan dalilin ne hankalin halimatu sadiya yayi matukar tashi tace zata maidashi a gurin mahaifansa,

wannan lokacin yana cikin al'adar garin makka cewa koda kai dan asalin garin makka ne idan kayi wata uku baka cikinsa to idan kadawo sai kayi dawafi kafin kashiga garin.

Halimatu sadiya taje tafara yin dawafi sai ta ajiye Annabi (s a w) akan wani dutse, lokacinda takarasa dawafi tadawo tarar cewa Annabi bayanan sai tafara kuka sai tahadu da wani tsohon mushiriki yace mike daminki kike kuka tagaya masa cewa jariri ne yabata,
sai yace taje tasamo gumba dakuma tasa abawa gunki yasha agayamasa bukatarki zai gaya miki inda jaririnki yake.

Hakan kuwa akayi taje ta nema gumba ta tasa aka shafawa gunki sai wannan tsohon yace kigaya masa bukatarki zai gaya miki inda jaririnki yake.

Halimatu sadiya tace jariri ne nazo dashi na ajiye ya bata sunan sa MUHAM kafin takarasa cewa MADU sai kawai gunki ya tarwatse ya guntu-guntu.

Watarana Annabi (s a w) yana dan shekara 3 suka fita kiwo shida sauran yara 'yan uwansa sai akaje gindin wata bishiyar dabino sauran yaran kowa sai ya dauki sandar sa yajefa dabino yafado adauka aci haka kowa yakeyi sai akace kai MUHAMMADU Kajefa mana.

Annabi (s a w) yadauki hannunsa mai daraja yana jefawa sai dukan reshen dabino ya karye yafado kasa.

Watarana Annabi (s a w) yana dan shekara 7 sukafita kiwo shida sauran yara 'yan uwansa suka zauna akarkashin wata bishiya shikuma Annabi (s a w) yana can gefe zaune acikin rana sai akaga wannan bishiyar dukkan rassanta suka malkwaya suka koma inda RASULLAHI sukayi masa inuwa sukuma sauran yaran akabarsu acikin rana.

Shikadai akalamuncewa komai tun yana da kananan shekaru.

Ubangiji ne yareneshi kima yake kareshi tun yana karami har girmansa.

Shine Allah yayi kira da suna masoyin sa.

Mukuma muke kiransa da masoyinmu kuma wanda zai cecemu aranar alqiyama dani dakai da duk wanda yaga wannan postin din kuma yaji farin ciki.

Allah yahada fuskokinmu a aljannah fiddausi ameen.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH