KOSAN SHINKAFA
KOSAN SHINKAFA
KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Shinkafa
2. Nama
3. Kwai
4. Attaruhu da albasa
5. Sikari
6. Kwakwa
7. Gishiri
8. Dunulen knorr
YADDA ZA KI HADA
Ki wanke shinkafa, ki zuba ruwa a cikin tukunya ya tafaso, sai ki zuba shinkafar ta dahu. Idan ta dahu sai ki sauke ki bar ta ta huce. Idan ta huce sai ki zuba a cikin babban kwano, ki fasa kwai da dan dama ki zuba a kan shinkafar, ki zuba gishiri da dunkulen knorr, ki yanka albasa ki zuba,ki jajjaga attaruhu ki zuba, sai ki kawo fulawa kadan ki zuba, sai ki juya domin ya hade jikinsa. Sai ki cuccura kamar kwallo ki soya a cikin mai mai zafi.
Idan kuma kina son mai zaki ne to sai ki zuba sikari da gurjajjiyar kwakwa a kwabin sannan ki cuccura ki soya.
To Uwargida kadan kenan daga cikin irin kayan soye-soye da za ki ringa soyawa yaranki ‘yanmakaranta domin tafiya da shi. Ko kuma don ci a gida, ko kuma idan kin yi bakin bazata nan da nan sai ki hada wannan kayan soye-soye domin tarbar baki.
Haka kuma Uwargida ya kamata ki san cewa ba kullum ba ne za ki ringa sakawa yaranki lemon kwali ko na gwangwani domin zuwa makaranta, don duk wadannan lemunan dankare suke da sikari kawai da zabibi. Don haka ya kamata ki dage ki ringa hada naki da kanki kina bawa yara idan za su tafi makaranta, ko kuma don sha a gida. Lemo irin lemon fata da kankana da abarba da karas da gwanda da mangwaro da gwaiba da sauran kayan itace suna da yawa. Sai ki zabi wanda ki ke so, domin Allah ya hore mana ‘ya’yan itatuwa da dama da za mu ringa sha. Don haka sai ki zabi wanda ki ka san iyalinki sun fi so ki ringa hadawa ko da yaushe. Kuma za ki iya zuba zuma maimamkon sikari. Ba wani abu bane yake jawo siyan na kanti illa kwuiya da lalaci da ya yi mana yawa. Amma idan kika saba yi yau da gobe sai ki ga ba wani abu bane mai wahalar yi ba, idan dai har kina da kayan da zaki yi amfani da shi, wani lemon bai fi ki yi shi a cikin minti biyar ba.

Comments
Post a Comment