Kura-kuren da mata ke yi wajen zaben miji

Kowace mace burinta ta samu miji nagari, wanda
zai kula da hakkinta, ya rike mata amana, ya kuma
kare mata mutunci. To amma mafi yawan mata
sukan tafka kuskure yayin da samari suka nuna
suna son su da aure, a karshe su yi biyu-babu,
lamarin ya sukurkuce saboda halin da suka nuna
tun farko.

Wadansu matan da zarar sun samu saurayi,
maimakon su fada masa gaskiya sai dai karya. Tun
daga farko idan ya tambaye su sunansu, sai su fada
masa sunan karya.

Wata sai tafiya ta yi tafiya sannan ta fito ta fada
masa sunanta na gaskiya, daga nan rashin yarda ya
shiga tsakaninsu, saboda karyar da ta yi masa tun
farko.

Wata kuwa sai ta kasa fada masa gaskiya, daga
bisani idan ya gano sunanta na gaskiya sai ya guje
mata ya nemi wata.

Wata budurwar ko bazawara maimakon ta fada wa
saurayin gaskiyar yadda danginsu yake, sai ta rika
nuna masa cewa su masu arziki ne, kuma iyayenta
masu daukaka ne, daga bisani idan saurayin ya
gane sai ya guje ta saboda karyar da ta yi masa.

Wadansu matan kan nuna wa saurayi karanta, idan
suna so su yi magana da shi, sai su rika yi masa
filashin, don ya kira su, ba za su taba kiransa a waya
ba. Wannan halayyar kuskure ce, don takan sanya
saurayi ya tsani budurwarsa, saboda mutane da
yawa ba sa so a rika yi musu filashin.

Saurayi ko wanda zai kara aure ba ya so mace ta
rika nuna kwadayinta a fili. Duk macen da ke nuna
wa namiji kwadayi, to babu shakka ta yi kuskure.
Idan kina son wani abu sai ki tambaya ta hanyar
ladabi da biyayya, sannan kada ki nuna masa kina
son abu a fili har ya gane kin zaku. Mafi yawan mata
da zarar sun ga wani abu sai su gallabi mutum har
ta kai ya daina zuwa wurinsu.

daya daga cikin dabi’un da mai neman aure ba ya so
shi ne, mace ta rika yi masa shisshigi da iya-yi.
Muddin kina yi wa mai neman auren ki haka, babu
shakka zai tsane ki. Mata da yawa ba su gane
lokacin da ya kamata su shiga wani sha’anin mai
neman aurensu da kuma lokacin da bai kamata ba.
Galibi wasu matan sukan wuce gona da iri wajen
danginsa da abokansa har ta kai an fara samun
gutsuri-tsoma daga bisani rai ya baci.
Wani kuskure da mata ke yi shi ne, da yawansu ba
sa nuna damuwa da irin son da ake yi musu. Duk
abin da ya same shi, na murna ko na bakin ciki, ba
za su nuna wata damuwa ba. Babu shakka wannan
dabi’a tana sa mace ta fita daga ran namiji. Ya
kamata a kiyaye.

boye so da kauna: Wannan dabi’a tana daga cikin
manyan abubuwa da ke bata neman aure. Ya sanya
a rika gudun mata, yakan kasance saurayi na so a
rika fada masa ana son sa fiye da kowa kirikiri. Don
shi ba zai iya fahimtar jirwaye mai kamar wanka ba.


Shi kuwa wanda ya taba aure yakan fahimci inda
mace ta sa gaba. Shi ba sai ta fito kiri-kiri ta gaya
masa ba, amma shi ma idan ya lura ba a bayyana
son ta hanyar da ta dace ba, to zai daina zuwa.

Kamata ya yi ’yan mata da zawarawa su fahimci iya
mu’amala da ladabi da biyayya da gaskiya da rikon
amana su ake bukata.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH