ANNABI MAI HASKEN ASALI (SAW).
ANNABI MAI HASKEN ASALI (SAWW).
Lokacin da Allah (swt) ya halicci Annabi Adam (as) sai ya nuna masa dukkanin Zuriyarsa, yana kallonsu, yana ganin irin fifikon da sukayi ma Junansu (ta dalilin hasken jikinsu)
Sai ya hangi wani haske mai mutukar Kyalli daga chan Qarshe. Don haka sai ya tambayi UBANGIJI cewa:
"YA RABBI WANNAN KUMA WANENE HAKA? "
Sai Allah yace masa "Wannan 'Danka ne mai suna AHMADU. shine na farko kuma shine na Qarshe. Kuma shine zai yi ceto (aranar Alkiyamah).
Isnadin Wannan hadisin mai kyau ne. don Qarin bayani aduba:
★ Dala'ilun Nubuwwa na BAIHAQY : juzu'i na 5
shafi na 483.
★ ALMIRQAT SHARHUL MISHQAT na Allamah
Aliyul Qary : juzu'i na 1 shafi na 289).
Ya Allah yi salati da tasleemi ga Annabinka mai asalin haske, Mai tsarkin asali, ka hada da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka, gwargwadon Soyayyar da kake masa.
Albarkacin wannan salatin ka dawwamar damu acikin sahun gaba na manyan Masoyansa, mabiyansa wadanda zai yi alfahari dasu aranar Alkiyamah.
Ameeen.

Comments
Post a Comment