Ilimin mata a wannan zamani
Ilimi gishirin zaman duniya. Idan babu ilimi, babu
rayuwa mai kyau. Kamar yadda aka sani a
Musulunci, ilimi wajibi ne ga namiji ko mace. Mace
kamar namiji, akwai bukatar ta yi ilimi domin ita
uwa ce, ita ke renon ’ya’ya, kuma halaye da
dabi’unta abubuwan kwaikwayo ne ga ’ya’yanta.
A lokutan baya, ba a ba mata damar neman ilimi
sosai ba, hasali ma, ilimi ba a damu a ba su iliminn
addini ballantana na zamani. Har ana cewa “Sabbi
saukar Mata”. Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke
nan sun bar karatu da neman ilimi. Suratul Sabbi
kuwa ita ce Surah ta 97 a Alkur ‘ani, kuma ita ce Izifi
na daya daga cikin Izifi Shittin na Alkur’ani.
Mace a wancan zamanin, idan ta kai shekara 14 ko
15 sai a yi mata aure. Hakan yana da kyau kamar
yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya hana
ilimin mata ba. Abin takaicin sai a bar su a gida ba
su san yadda ake tsarki ba.
Daga baya da ilimin boko ya fara shigowa kasashen
Hausa, sai aka dauki karatun Boko a matsayin wani
abu marar amfani. Ba a ba ’ya’ya maza da mata
damar su yi karatun ba. Bayan an fara gane
muhimmancin karatun boko ne, aka fara ba maza
damar yin karatun sosai.
A manyan makarantun boko akwai sashi daban-
daban, wadanda dalibi zai iya yin karatu. Akwai
kamar Likitanci da karatun zama Injiniya da na
harsuna irinsu Turanci da sauransu. A bangaren
karatun likitanci da Unguwarzoma, wadannan sashi
ne da mata za su fi mayar da hankali, domin hakan
zai amfani al’umma. A wasu asibitocin, maza ne
wadanda ba muharramai ba ke duba mata. To a
maimakon haka, zai fi kyau a ce mace ta duba ’yar
uwarta.
Mafi yawancin tsokacin mutane a kan karatun ’ya’ya
mata a kan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada
maza da mata, yadda tsarin sanya tufafi yake da
sauransu. Idan har gwamnati na so ta habaka ilimin
mata a Najeriya, musamman a arewa, ya zama dole
ta yi la’akari da halayya da addini da zamantakewa
da kuma al’adun mutune wajen tsara makarantu da
kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka sosai
wajen bunkasa ilimi sosai a Arewacin Najeriya.
Ina so mata su sani neman ilimi wajibi ne, sai dai su
sani ya zama dole su tsare kansu daga aikata
dukkan ayyuka marasa kyawu, iyaye su sanya idanu
wajen lura da yadda ’ya’yansu mata suke karatu.
Kwamared Abdulbaki Aliyu Jari

Comments
Post a Comment