An Cafke Mai Gyaran Takalma Bisa Zargin Yi Wa Mai Tabin-Hankali Ciki
An Cafke Mai Gyaran Takalma Bisa Zargin Yi Wa Mai Tabin-Hankali Ciki
Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Jigawa tace ta yi nasarar cafke wani matashi mai sana’ar shushaina mai suna Abdulhamid Abbas bisa zargin dirkawa wata yarinya mai tabin hankali ‘yar shekaru 16 da haihuwa ciki a kauyen Adachuwa dake karamar hukumar Miga a jihar Jigawa.
Kwamandan hukumar ta NSCDC reshen jihar ta Jigawa Dakta Muhammad Gidado ne ya tseguntawa ma nema labarai wannan al’amari a babban birnin jihar dake Dutse cikin makon da ya gabata.
Comments
Post a Comment