YADDA ZAKA GOGE VIRUS A WAYARKA DA MEMORY CARD TA HANYAR AMFANI DA BLUEFTP.

YADDA ZAKA GOGE VIRUS A WAYARKA DA MEMORY
CARD TA HANYAR AMFANI DA BLUEFTP.

Viruses kowa ya san shi wajen bata waya, memory
card da kuma PC saboda hakane ake da hanyoyi da
dama wajen goge shi.

Zaka iya amfani da BlueFTP wajen goge duk wani virus
akan waya da memory card ba kamar yadda kuka
sanshi kawai wajen tura da karbar file ba daga wata waya zuwa wata.

Za iya amfani dashi wajen goge
virus kamar: AUTORUN.EXE, wanda shine ya zama
ruwan dare daya dabai-baye memory card, flash
drives kai harma da PC. Wannan virus yana da
matukar hadari kuma yana kai farmakin sane a
hankali a hankali kuma ya kasance boyayyen virus ne ba zaka iya ganinsu ba,(hiddenvirus). Domin cire ko goge irin wadannan virus ta hanyar
amfani da blueFTP to sai nutsu ka biyoni a wadannan
matakan.

>>Idan baka da blueFTP, sai kayi download dinshi.
>>Ka bude blueFTP dinka, sai ka nufi memory card/E;/
sai kayi kasa a cikin memory card din, to idan kana da
virus akan memory card dinka, zaka nuna maka su a
matsayin:
INDEX.
TR
AUTORUN.
EXE
USB VAULT
AUTORUN.
INFO
ACHE.EXE

da sauransu.
>>Sai kaje wurin nasu, saika danna 9, sai kuma 3, daga
nan sai kayi marking din wadansu akwatuna wadanda
zasu bayyana, wadanda sune:

READ FLAG

HIDDEN FLAG

WRITE FLAG.
Abinda zakayi kawai kayi mark din WRITE FLAG amma
karda kayi marking din(unmark) HIDDENFLAG sai kuma
kabar READFLAG a mark dinshi sannan kayi saving.

>>Sai kazo ka rika bi kana zabansu daya bayan daya
ta hanyar danna * akan duk virus din daka gani,bayan
ka gama sai ka danna menu/option domin gogewa
zaka delete sai ka shiga, bayan ka gama gogewar sai
ka rufe BLUE FTP dinka.
>>Kaje memory card dinka, zaka ga cewa duk wani
virus ya goge, daga nan zaka zo kayi restorefactory din
settings din wayarka.
>>Amma kafin kai restore factory na wayar, kayi
moving din duk wani file naka mai muhimmanci akan
wayarka zuwa memory card,
wadanda suka hada da lambobin wayarka wadanda
suke kan waya zuwa sim card.

Domin komai zai goge nakan wayar. Shikenan wayarka da memory dinka sun dawo daidai duk
wani virus ya fita.

Shawara: ya kamata ka rinka yin irin wannan akalla
sau daya duk wata domin kare wayarka da memory
card dinka da kamuwa da virus din da zai iya
sanadiyar rasa wayarka ko memory card dinka.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH