Siffofi 20 na mace tagari
Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar
muhimmanci a zamantakewar iyali, shi kuwa gida
ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wacce
take tattare da siffofi abin koyi da za su taimaka
mata wajen tafiyar da gidan yadda ya kamata.
Siffofin sun hada da:
1. Ta kasance mai riko da addini, ba mai saka ci da
shi ba.
2. Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a
kodayaushe.
3. Ta sanya Allah a ranta a duk al’amuranta na yau
da kullum
4. Ta zama mai shigar mutunci, misali sanya hijabin
da zai rufe mata jikinta yayin da ta fita zuwa
unguwa.
5. Ta kasance mai kamanta iyaye da ’yan uwa da
abokan mijinta.
6. Ta kasance mai yawan kwalliya da ado ga mijinta
7. Ta kasance kwararriya wajen iya girki.
8. Ta kasance mai godiya ga abin da mijinta zai
kawo mata, kada ta rika rena abin da mijinta zai
kawo mata .
9. Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da
maigida ya kira ta zuwa shimfidarsa.
10. Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu
kayayyaki da yake amfani da su.
11. Ta kasance mai rufa wa mijinta asiri, ba mai
watsa sirrinsa ba.
12. Ta kasance mai ba shi hakuri cikin lalama yayin
da ta yi masa laifi.
13. Ta kasance mai nuna farin ciki idan abin farin
ciki ya same shi, da nuna bakin ciki idan abin bakin
ciki ya same shi.
14. Kada ta yabi mijin wata alhali tana tare da
mijinta.
15. Ta kasance mai kwantarwa mijinta hankali yayin
da yake cikin damuwa.
16. Kada ta ba wata ko wani dama ya ji sirrinsu (ita
da mijinta).
17. Ta kasance mai kokarin neman ilimi da aiki da
shi.
18. Ta kasance mai nisantar abin da ba ya so, ta
kuma rika kusantar abin da yake so.
19. Ta kasance mai bin umarnin yi ko bari wajen
nuna masa so da kauna a fili, ba a boye ba.
20. Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa
bukatun da ba zai iya biya mata ba.
Babu shakka da bincike na tsanaki ne ake samun
mace mai siffofi nagari abin koyi, gaggawa da
kwadayi kuwa a harkar neman aure, babu abin da
suke jawowa face da na sani, ita kuwa da na sani
aka ce keya ce. Allah Ya agaza mana.

Comments
Post a Comment