AWARAH ‘YAR DUBAI

awara-yar-dubai.jpg



AWARAH ‘YAR DUBAI


Awarah wani nau’i ne na gurasar kwai wanda aka fi yi a kasar
Hausa. Yawanci a kan yi amfani ne da kwai da kayan miya
domin hada shi, kusan an fi yin sa a cikin karkara. A yau za mu
kalli wani salo na yinsa a zamanance.


Wanda za mu dan yi bayaninsa shi ne Farko, uwargida za ta
samu kwai daidai buatar da take so.


Bayan kin samu kwanki, sai ki fasa shi daidai kamar yadda ake
amfani da shi yau da kullum, ki sa Maggi da Gishiri kadan,
sannan ki samu dakakken kayan miya, Attarugu, da Albasa, ki
dan sa mai kadan, sai ki buga shi ya kadu sosai.


Mataki na biyu shi ne ki zuba a leda ki yi kullin Alala, sannan ki
dora bisa murhu a tukunya, ki zuba ruwa, ki dora a wuta.
Bayan kin yi wadannan duka, sai a bar shi ya dahu, sannan ki
sauke, bayan kin tabbatar ya nuna.


Mataki na uku shi ne ki sauke shi, sannan ki dan bude idan ya
sha iska, ki yanka yadda kike so, sai ki kuma dorawa a dorawa
a wuta, amma a wannan karon a cikin tukunyar suya za ki
dora, bayan kin zuba mai.
Idan ya hadu, ya soyu, sai a sauke a kuma yi amfani da shi
yadda ake so.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH