Posts

Showing posts from October, 2014

TUN KAFIN ZUWAN MUSULUMCI

1)Tun kafin zuwan Musulunci Mushirikkan Makkah suna azumin ashura, Annabi SAW ma ya azumce shi a Makkah ( Bukhari) 2) Da Annabi SAW yayi hijira zuwa Madinah ya sami Yahudawa a Madinah suna azumtar shi ya azumce shi ya umurci Musulmi su azumce shi (Bukhari) 3) Annabi SAW yace game da azumin Ashurah ina tsammanin Allah ya karkare zunubban shekarar da ta wuce (Muslim) 4) Yace : idan na rayu zuwa shekara mai zuwa zan azumci tara gawata (Muslim) 5) Azumi kawai aka sani a lokacin Annabi SAW da Abubakar da Umar da Usman da Ali da Muawiya Allah yayarda da su. Daga baya yan shia suka kashe Husaini a Karbala ranar ashura sai mutane suka kasu uku: (a) Yan shiar da suka kashe shi suka riki ranar ranar makoki da bakinciki (b) Nawasib suka rike ta ranar murna da cika ciki (c) Ahlussunnah suka cigaba da azumi kamar yadda ya tabbata a lokacin Annabi SAW. 6) Don haka duk Hadissan da sukazo gameda falalar cika ciki basu inganta ba (Tamamul Minnah) 7) Tara ga wata (Tasu'ah) zai kasance Lahadi goma ga...

DAN ALLAH KADA SHAIDAN LA'ANANNE YA HANAKA TURAWA DA YIN WANNAN ADDU'AR"

_"Allaahumma anta Rabbiilaa ilaha illa anta khalaktani wa ana'abduka wa ana alaa ahdika wawa'adika mastada'atu, a'uzu bika min sharri ma sana'atu abuu'u laka bi ni'imatika alayya wa'abuu'u bi zambii, Fagfirlii innahuu laa yagfiruz Zunuba Illaa Anta.Allaahumma salli alaa Muhammadin wa ala aali Muhammadin warham Muhammadan wa'ala Muhammadin, wa baarik ala Muhammadin wa'alaa ali Muhammadin kama sallaita waRahimta wabarakta alaa Ibrahima wala'ali Ibrahima innaka hamidun majiidun.Attahiyyaatu Lillahi Azzaakiyaatu Lillahi Addayyibaatus Salawaatu Lillahi, Assalamu Alaika Ayyuhan Nabiyyu, wa Rahamatullahi, waBarakatuhu, Assalamu Alaina wa'ala Ibaadillaahis Saalihina, Ashhadu an laa Ilaaha Illallahu wahdahu la Sharika Lahu wa Ashhadu anna Muhammadan Abduuhuu wa Rasuuluhu.Allaahumma inna Nasta'inuka wa Nastagfiruka wa Nu'uminu bika, wa Tawakkalu Alaika, wa Nusnii Alaikal khaira kullahuu, Nashkuruka walaa Nakfiruka, wa Nakhna'u ...

Hausa kenan ba dabo ba Mai wuyar koyo ,Karin maganar HAUSAWA kenan,wasu subaka mamaki wasu subaka dariya.

Hausa kenan ba dabo ba Mai wuyar koyo ,Karin maganar HAUSAWA kenan,wasu subaka mamaki wasu subaka dariya. 1.Abin rabone auren mace da ciki. 2.Duk inda jirgi yaje idan akai hakuri kunkuru ma zaije saidai yadade bai jeba. 3.Daga uhm sai uhm wai uwar gulma tayi cikin shege. 4.Ina ruwan wani da wani wai mahaukaci yayi bako. 5.yau da gobe mai sa amari Suruka. 6.Sara da sassaka baya hana gamji tofo 7.Mai hankali shi yake gane din'gishin kwado......! 8.Mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi.... 9.Mai hankali shi yake gane Baccin makaho... 10.WANDA YA GANI shiya ji kunya KALLON FITSARIN MAKAHO 11.Da zaman banza gara aikin kishiya 12.Allah kadai yasan karatun kurma, 13.RUWA a chokali ya i'shi mai hankali wanka,,,,. 14.ko yaushe kare ya samu daman mike kafa 15.Abu yayi dai dai ankama ango da uwar amarya 16.Gani yakori ji.... 17.Albarkacin kaza gadan gare yakansha ruwan kasko... 18.Da zaman banza gwamma aikin uwar kishiya.

Idan kaine yaza kai ?

Wata mata ceke tafiya a motar haya tare da mijnta a dokar daji sai barayi suka tare su aka sassauka kasa Can sai shugaban barayin ya kyallara ido yaga matar mutumin nan sai yace ta taso tazo gabansa ta tsaya Jikin ta na rawa ta tafi saiya dubi mutanen nan yace ina mijin wannan mata? Kowa yayi shiru yana tsoro Ya sake kwala ihu da ina mijin wannan mata shiru kake ji Sai yace har inna kirga uku bai fito ba zan harbe ta Kawai sai Ya fara kirga daya , biyu , amma miji Qus shiru kakeji yaki fitowa Kafin ya fadi ukun sai wani fasinja daga cikin motar ya mike yana rawar jiki ya daga hannu sama Yace gani nan nine mijinta Barawon ya kwashe da dariya yace shege don ubanka a ina ka samo mata mai kyau haka? Mutumin yana rawar jiki yace unguwarmu daya ne aka hada mu aure da ita Sai 6arawo yace chaf toh jaa matarka ku koma can ku tsaya kunci Albarkacin AURE Ku kuma da bakuda Aure duk xamu kasheku ko dame magana ?

MUSHA DARIYA

Wani bakauye ne mai son yawon duniya, wata rana yana zaune, sai yaji wasu mutane suna hira, suna cewa ai more bariki sai birni, kayi iskanci iya sonka babu ruwan kowa dakai, a bariki zaka ga mata masu kyau, ga kayan shaye shaye kala kala, sai yaji dadin wannan maganar tasu, yayi ta murna, gari na wayewa, yaje ya tattaro yan kayanshi da yan kudin shi daya tara, ya nufi tasha sai birni, aka sauke shi a tasha, yasamu mai tasi yace ya kaishi bariki, mai tasi ya dauke shi bai zame dashi ko inaba, sai babbar Barikin sojoji, yana zuwa ya nuna masa yayi gaba, yana shiga sai sojoji suka taso da gudu suna masa tsawa, sukace kai mahaukacin inane Ina zaka? Sai yace yazo barikine zaiyi iskanci, suka ce to zakaga iskanci, suka sashi a guad room suka ringa bugun sa kamar suna bugun kayan wanki saida yayi kashi da fitsari, baya iya tashi, suka kuma tambayar sa, me kazo? Sai yace dan ALLAH ku nuna min inda massallaci yake Sallah nazo yi....... wai shin wannnan mutumin dan inane.... A Kano B kaduna C jo...

Al-imamul Bukharin

Al-imamul Bukharin Da Al-imamu Muslim Sun rawauti Hadisi Daga Abdullahi Dan mas'ud رضي الله عنه Yace: Manzon Allah S.A.W Yace: عليكم بصدق فإن الصدق يهدي الي البر وإن البر يهدي الي الجنة ولا يزال الرجل يصدق ويتحر الصدق حتي يكتب عند الله صدي قا (((Ma'ana))) Inayimuku umarni da yin gaskiya domin gaskiya tanasa mutum yazama mai kyawa-wan hali shikuma kyan hali yanakai mutum ga shiga ALJANNA mutum banzai gusheba yana fadar gaskiya da aiki da gaskiya har sai Allah ta'ala yasa anrubta sunanansa cikin masu gaskiya. Manzon Allah yaci gaba da cewa: واياكم والكذب فإن الكذب يهدي الي الفجور وإن الفجور يهدي الي النار ولا يزال الرجل يكذب ويتحر الكذب حتي يكتب عند الله كذابا. (((صدق رسول الله))) (((Ma'ana))) Inayimuku gargadi kudaina qarya domin qarya tanasa mutum yazama mai sabon Allah shikuma Sabon Allah yanakai mutum ga Shiga WUTA mutum banzai gusheba yana fadar qarya da aiki da qarya har sai Allah yasa an rubuta sunansa cikin jerin maqaryata. Mazon Allah yayi gaskiya. Allah yabamu i...

SHUGABAN MATASAN AREWA YACE JONATHAN ZASU BA KURI'AR SU DON YA KARASA AYYUNKAN DA YA SOMA.

SHUGABAN MATASAN AREWA YACE JONATHAN ZASU BA KURI'AR SU DON YA KARASA AYYUNKAN DA YA SOMA. Yayin da yake hira da manema labarai jajibirin da JONATHAN zai yanki fom din takarar shugaban kasa na PDP shugaban matasan arewa Alhaji Yanko Yakasai ya bada tabbacin cewa matasan arewa suna goyon bayan JONATHAN dari bisa dari kuma shi zasu dangwalawa kuri'ar su lokacin zabe mai zuwa don ya karasa ayyukan da ya fara yi wa kasa. MATASAN AREWA KUN AMINCE DA KALAMUN SHUGABAN KU ALHAJI TANKO YAKASAI???

HUKUNCIN GAISAWA DA MATAR DA BA MUHARRAMA GAREKA BA.

alamu alaikum malam barka da himmah Allahu (S W A) ya kara ma hazakah. Dan Allah malam muna neman sani game da sallama wato ( السلام عليكم ) tsakanin mata da maza musamman ma matan aure ko ya halitta namiji yayi wa macce ta aure sallama wacce take ba muharraminshi ba? ko kuma mace ta aure tayiwa wani namiji sallma wanda yake ba muharaminta ba, Malam dan Allah kayi hakuri in da hali ka amsa muna wannan tambayar AMSA * *** Wa alaikumus salam wa rahmatullah. Hakika Malam Muhammad kayi tambaya mai muhimmanci. Kuma insha Allahu zamu amsa maka gwargwadon abinda Allah ya sanar damu. Da farko zamu fara tambayar kanmu: MENENE MATSAYIN ITA KANTA SALLAMAR? Ita dai sallama atsakanin Musulmai, Abu ne mai mutukar muhimmanci wanda Allah da Manzonsa yayi umurni da ita. Allah (swt) yana cewa: "IDAN AKA GAISHEKU DA WATA GAISUWA, TO KUMA KU (AMSA) GAiSUWAR DA WACCE TAFI KYAWU DAGA GARETA, KO KUMA KU MAYAR DA ITA". (Suratun Nisa'I ayah ta 86). Sayyiduna Abu Huraira (ra) ya ruwaito daga Manzo...

Jerin Wasu Mutane Da Kungiyoyin Da Suka Tallafa Wa Jonathan Da Kudi Domin Sake Fitowa Takara A 2015

Jerin Wasu Mutane Da Kungiyoyin Da Suka Tallafa Wa Jonathan Da Kudi Domin Sake Fitowa Takara A 2015 1. Mr. Kennedy Ikenna Odoeme – N5, 000 2. Mr Ezemagu Sunday Nnamdi – N10, 000 3. Gwamnonin PDP – N22 Million 4. Transformation Agenda of Nigeria (TAN) – N22m 5. Jigogin Karamar Hukumar Ogbia, Bayelsa – N5m 6. Al'ummar Garin Otuoke – N2m 7. Jigogin Karamar Hukuma Brass, Jihar Bayelsa – N50, 000 8. Jigogin PDP na Jihar Bayelsa- N5m 9. Northern Youths Forum – N2m 10. Central Market Traders Union, Kaduna State – N1m 11. Jigogin PDP Na Karamar Hukumar Zaria – N500, 000 12.Jigogin PDP na jihar Yobe – N500, 000 13. Jigogin PDP Na Jihar Kaduna- N2m 14. Miyetti Allah Kautal Hore – N5m 15. Kungiyar Magoya Bayan Goodluck, A Jihar Gombe – N1m 16. Jigogin PDP na jihar Adamawa– N3m 17. Jigogin PDP na jihar Ebonyi - N2m 18. Jigogin PDP na jihar Kogi– N5m 19. Jigogin PDP na jihar Rivers– N5m 20. The 2015 Project – N1m 21.Team Goodluck, Mazabar Ondo Ta Arewa– N5m 22. Kungiyar Mata Magoya Bayan PDP Na...

ALLURA FAH

ABU 4 SUNA CUTAR DA JIKI 1- yawan magana 2- yawan barci 3- yawan jima'i 4- yawan cin abinci ABU 4 YANA RUGUZA JIKI 1- bakin ciki 2- bacin rai 3- rashin barci 4- yunwa ABU 4 YANA JANYO ARZIKI 1- yawan istigfari 2- tsayuwar dare 3- yawan sadaka 4- Zikirin safiya da yammaci (irin wanda Annabi SAW ya koyar) ABU 4 YANA HANA ARZIKI 1- baccin asuba 2- karancin sallah 3- kasala 4- Ha'inci ABU 4 YANA BUSAR DA FUSKA DA TAFIYAR DA HASKENTA 1- karya 2- bushewar zuciya 3- yawan tambaya ba akan ilimi ba 4- yawaita fajirci ABU 4 YANA KARA HASKEN FUSKA 1- tsoron Allah 2- cika alkawari 3- yawan kyauta 4- kame kai

KANKA TSAYE BATARE DA WATA FARGABAVA Yanda zaka tsara mace a karin farko."

Idan kaga 'yar baby tana tafiya sai kaga tashiga zuciyarka kuma kanason yi mata magana.. (1)dafa rko dai ka tabbata kaima kahadu ma'ana kadau wanka mai kyau saboda wanka yana daya daga ckn abunda ke sato maka zuciyara mace..sai karka yi mata magana sai ka tabbata tazo dai dai gurin da babu mutane sosai don wata tana da alkunya. (2)daka karasa gurinta dakaje sai kafara yi mata sallama kamar yanda addininmu yatanadar nasan indai ta cika musulma zata amsamaka kaga kasamo hankalinta kenan. (3)sai kace ranki yadade kiyi hakuri fah nasan ba mutuncin kyakkyawar mace mai haiba da asali bane tatsaya ta kula namiji a yayin datake tafiya izuwa wani guri,amma kiyi hakuri nima bayin kaina bane wani sashen bangaren jikinane ya uzuramin dole sai nayi hakan tun yayin da idanuwana sukai arba da wannan kyakkyawar surar taki. (4)kar dai incikaki da surutu nasan kina sauri ne saboda haka nake neman wata alfarma guda 2 zuwa 3 agunki.zata cema inajinka. (5)don Allah menene sunan hajiyar ne? Zata iya...

KAFIN KA YANKEWA MUTUM HUKUNCI YA KAMATA KAYI NAZARI KAN MAGANARSA KO KAI WAYE.

Wata Rana Sayyidina Umar (rta) Ya Fito Daga Masallaci Sai Yaga Wani Mutum A Zaune Gefen Masallachi. Sai Yai Mai Sallama Yace: Bawan Allah ko zaka iya gaya min yadda ka tashi a Rayuwarka? Sai Wannan Bawan Allah Yace wa Sayyidina Umar Na Tashi Ina Son Fitina Kuma Ina Kin Gaskiya Kuma Ina Sallah Ba Tare Da Arwala Ba Kuma Ina Da Abinda Allah Baidashi. Rufe Bakinsa Ke Da Wuya Sai Sayyidina Umar Ya Zaro Takobi Yace Sai Ya Kashe Shi Suna Wannan Hali Sai ga Sayyidina Aliyu Ya Biyo Wurin Sai Ya tambayi Sayyidina Umar ko meke faruwa? Sai Sayyidina Umar yaGaya Masa, Sai Sayyidina Aliyu Yayi Murmushi Yace: To Ai Koni Na Tashi Ina Son Fitina Kuma Ina Kin Gaskiya Kuma Ina Sallah Batare Da Alwala Ba Kuma Ina Da Abin Da Allah Bai Dashi. Sai Sayyidina Umar Yace To Ina Jinka me Wannan ke nufi? Sai Sayyidina Aliyu Yace Abinda Yake Nufi Da Ya Tashi Yana Son Fitina Shine, Umar hala ka mance Allah Yace "Lallai Dukiyoyinku da Diyan Ku Fitina Ne?" Kuma Kaga Ni Ina Son 'Ya'ya Da Dukiya Kuma K...

Labarin wani yaro da mai taxi

wani mai gida ne, Ya kirawo mai taxi yace, Kullim ka ringa zuwa kana daukar yayana. Su uku. Kana kaisu makaranta zan ringa biyanka. Sai yace to. Aka kirawo yara suka fito. Suka shega mota. Suna tafi. Sai wani yaro acikinsu. Mai surutun jaraba. Yace idan babana yazama sarki ni kuma sai na zama dan gata mai girmankai. Kuma babata ta zama sarauniya. Kenan. Ashe ya dame mai taxi da surutu. Mai taxi yace. Da yaran . Idan babanka ya zama dan giya. Babarka ta zama karuwa. Kaikuma me zaka koma? Sai yaran yaye dariya yace. Sai na zama dan taxi hahaha hmm idan kaine me zakace dashe kuma wani mataki zaka dauka akansa

LABARINA Kashi na farko

You are under arrest, shine maganarda na faraji sunyimin lokacinda suke kokarin samin ankwar a hannuna.. Na daga kai na dubesu a tsorace hankalina ya gama tashi da naga yan sanda ne da bakaken kaya sama da goma sun zagayeni nai saurin magana bakina na rawa nace dasu me..ke..f..ar..uwa..ne? Marin da naji ya sauka a fuskata shine abinda ya dakatar dani daga maganar da nake sannan daya daga cikin yan sandan mai jajayen ido da gashin baki yace dani ba kaine muhammadu ba mai dandalin soyayya? Nai sauri na daga kaina na dubesu da naji ya ambaci dandalin soyayya sannan nace eh nine muhammadu me nayi muku kuma?? A lokacin ne mahaifiyata ta fito daga cikin daki itada kanwata liliane lokacin da sukaji hayaniya tana tashi a cikin gidan suna zuwa suka iske yan sanda sun kewayeni sun samin ankwa a hannuna bayin Allah me dana yayi muku? Kukazomin har gida kuke shirin kamashi ku tafi dashi? Yan sandan suka dubeta sannan suka dubeni lokacinda idanunana ya ciko da kwalla ina shirin fashewa da kuka nace...

WAI CIKINSU WAYE BARAWO

wani mutum ne zai yi tafiya sai ya hagi wata mata mai siyar da bush meat,sai ya tsaya da motar sa zai siya,sai yace mata nawa-nawa? Sai tace #7500 sai ya nemi ragi sai tace masa ya bada #7000 last,ya amince a hakan, da ciniki ta fada,sai yace mata ta saka masa a but,tana zuwa bayan but din sai ta raya a ranta ina ma ta ajiye naman a kasa tayi kamar ta sa a but din? Hakan kuwa akayi sai ta rufe bud din kirif sho ko mutumin na jin haka alamun an saka masa nama an rufe masa bud! Sai ya fizgi motar sa a guje ya gudu! Tunaninsa ya cuce ta! To wai waye barawo a cikinsu ?

LBRN WATA mata DA mijinta

Wata mata ce tanason ta gwada mijinta, taga inhar suka rabu yaya zaiyi?. Sai tadauki takarda tayi rubutu kaman haka, "mijina gaskiya bana sonka yanzu jinake na tsaneka bana bukatar kallon fuskanka gara na kalli fuskan goggon biri da na kalli fuskan ka, bana burin jin muryanka gara na saurayi wakar shata da naji muryanka, dan haka nayi tafiyata ka auro wata"....... Sai ta ajiye akan kujeran da yake falon sannan takoma bayan kujeran ta buya... Mijinta yana zuwa yasamu bakowa a falon yana kokarin zai kirata sai yaga takarda akan kujera sai yadauka yakaranta... Nan take yafashe da dariya sannan yadauko wayansa ya sa akunnensa yafara cewa,''hello masoyiyata abun da muka dade muna addu'ar shi yau yazo. Yanzu nadawo daga wajen aiki na samu wannan lalatacciyar matan nawa tabar gidana kinga sati mai zuwa kawai sai adaura mana aure... Sai yafashe da dariya ya kara da yawe kijirani yanzu ina zuwa zamu tafi hotel muci abinci.....'' Bayan yagama maganganunsa sai yajuya...

LABARI

Wani Bawan ALLAH Ne ALLAH Ya Azurta Shi Da 'Yaya Mata Har Guda Shida. Shi Kuma ALLAH Ya Sanya Mashi Son Ya Samu Yaro Namiji. Sai Matar Shi Ta Samu Ciki, Aiko Sai Ya Shiga Damuwa Tsoron Kada Ta Haifi Mace. Hakan Yasa Shi Yayi Azama a Cikin Zuciyar Shi, Lallai a Wannan Karon Idan Matar Nan Ta Haifi Mace, To Sakinta Zai Yi. ALLAH Mai Iko a Cikin Wannan Daren Ya Kwanta Barci Sai Yayi Mafarki Al-Qiyama Ta Tsaya, Kuma An Halarto Da Wutar Jahannama Mai Ruruwa. Duk Lokacin Da Aka Dauke Shi Za'a Shigar Da Shi Ta Daya Daga Kofofin Wuta, Sai Daya Daga Cikin 'Yayan Shi Matan Nan Ta Zo Ta Tare Kofar Ta Hana a Shigar Da Shi. Har Sai Da Aka Karade Kofofi Shida Na Wutar Jahannama Sai Kofa Daya Kawai Ta Rage. Sai Mutumin Nan Ya Farka Cikin Firgici, a Tsorace, Kuma ALLAH Ya Ganar Da Shi Kuskuren Shi Bisa Abinda Ya Kudurta Zaiyi a Zuciyar Shi. Ya Daga Hannu Ya Roki ALLAH Ya Azurta Shi Da Samun 'Diya Ta Bakwai MACE. Ya ALLAH Ka Azurta Mu Da Masu Albarka Masu Jin Kai Kuma Masoya ANNABI(sall...

An Cafke Wani Dan Sanda Yana Saida Bindigogi A Kaduna

Wani dan sanda mai suna Nanbol Audu ya shiga hannu a yayin da yake kokarin saida wa wasu mutane su biyu 'yan jihar Filato bindigogi. Mutanen dai su ne Zingkur Joseph da Samuel Adamu wadanda dukkansu ma'aikata ne a jihar Filato. Miyagun sun shiga hannu ne a lokacin da suke kokarin fita daga ofishin 'yan sandan tare da Nanbol Audu wanda dan sanda ne shi. Kawo yanzu dai dukkansu suna hannu. Kuma sun bayyana cewa sun sayi bindigogin ne a kan kudi naira dubu dari hudu (N400,000).

11 WAYS ON GETTING YOUR DUAS ACCEPTED

1. Always have full faith in Allah and do all ibadath for his pleasure only 2. When making dua to Allah say"YA ALLAH ACCEPT MY DUA WITH THE WASEELA OF MUHAMMED(SAW)" 3. Give thanks to Allah for what he has given you and he will give you more Insha Allah! 4. Beg Allah with his 99names or isme azam or dua asma-al-husna,which is very effective 5. Make istagfaar to Allah or ask for forgiveness with sincerity and try to refrain from sins 6. Read atleast 3 durood shareef when beggining dua and ending 7. Make dua for your parents which is very important 8. Make dua with alot of feeling.Tear and cry in your duas,if this not posible then make like u tearing and beg Allah for what you desire 9. Praise and glorify Allah and reading surah Fatiha is very effective too 10. Try to remember Allah all the time and not only when in need and distess. 11. After making dua/prayer read "ya Wahaabo" 7 times - Insha Allah it will be granted! May Allah accept our good prayers!

Shin dan Nigeria zai rayu ko shima aljani zai kashe shi?

Wata rana wani dan Nigeriya yahau Jirgin Sama da niyyar zuwa wata Kasa , sai suka hadu da Turawa guda biyu shi kadai ne Baki dan Africa ana cikin tafiya sai Aljani ya bayyana a cikin Jirgi sai kowa ya firgita , Sai Aljani yace zan kasheku duka amma zanbar mutum daya Duk wanda ya jefa wani abu a cikin Kogi (Ruwa) idan na shiga ruwan bansamu abun ba to shine kawai zai rayu Sai Baturen farko ya cire Ma6allin rigarsa ya jefa Aljani ya shiga ruwan saiya dauko saiya kashe Baturen Bature na biyu ganin an kashe dan uwansa sai shi kuma ya jefa Allura Aljani ya shiga saiya dauko sai shima ya kashe shi , Sai gogan naku dan Nigeriya shi kuma daya tashi saiya bude robar ruwa (swan water) da aka basu a cikin jirgin saiya juye ruwan nan acikin kogin ,

Shawarwari 52 daga bakin Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam Kano zuwa ga ma'aurata.

Da sunan ALLAH mai gamammiyar rahama mai jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama, da alayansa, da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar tashin al-kiyama. Bayan haka, shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda aurensu yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani. Ga wasu Shawarwari wadan da idan mata sukayi la'akari da su insha ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure. Muna addu'ar ALLAH ya bada ikon kiyayewa. 1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba. 2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure. 3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa. 4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki. 5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki. 6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki. 7- Ki za...

labarin wani barawo

watarane wani Barawo yaje wani gida yin sata cikin dare, bayan yashiga cikin gidan sai ya lallaba yashiga wani daki a hankali saiyaji alamar da mutane a cikin dakin suna barci, shikuwa Barawo harda yin murmushi yana murna, kawai saiyasaki jiki xaiyi satarshi a tsinake tunda yaga duk suna barci, abinka da barawo saiya rasa abinda zai fara dauka a dakin tunda akwai duhu kuma gashi yamanta baitaho da fitilar haskawaba dazai haska da ita, kawai saiya jawo kofa ya kulle yafara lalubar inda zaiji makunnar wuta domin ya kunna, cen saiyaji makunnar wuta, saiyayi ajiyar zuciya yafara murna. Kunnawarshi keda wuya kawai sai Unguwa ta kaure da karar injin markade kararararararararararara. Ashedai makunnar injin markade ce bata wutaba, aikuwa kafin kace tak duk jama'ar gida kowa yafarka suka nemi Madoki kuma gashi dama duk samarine gardawa majiya karfi a gidan. Towai shin idan kaine yazakai???

wani bakauye da inyamuri

Wani bakauyene yayi abota da wani iyamiri. Duk sa'adda ya shigo gari sai ya je wurin abokinsa sun yi fira, haka shima iyamirin yakan je kauyen abokinnasa su sha fira su ci abinci. Rannan sai shi iyamirin ubansu ya mutu a can garinsu, sai ya shirya ya tafi garinnasu don burial ceremony amma bai sanar da wannan abokin nasa ba (bakauye). Sa'adda shi bakauyennan ya shigo gari ya je shagon abokinsa sai ya tarad da shagon a rufe. Koda ya tambaya sai aka fada masa abinda ya faru ga uban abokinsa, sai ransa ya baci kwarai ya koma gida. Bayan iyamirin ya dawo, da bakauyennan ya shigo gari karo na biyu sai ya iske abokin nasa ya komo. Da suka gaisa sai ya ce wa iyamirin, "WATO BABANKU YA MUTU A GIDA KUNJE GARINKU KUN YI WASA KUN CI ABINCI KUN SHA GIYA KUN MORE AMMA BAKA GAYYACENIBA, TO BAKOMI AI MUMA BABANMU YANA ASIBITI"

ALBARKACIN HANNAYEN ANNABI (SAWW).

SAYYIDUNA ABU-HURAIRA (RTA) YACE: "Watarana nazo wajen Manzon Allah (saww) da wani dabino dan kadan, Sai nace Masa : "YA RASULALLAHI YI MIN ADDU'A MANA, KA ROQA MIN ALBARKA ACIKIN WANNAN DABINON NAWA" Sai ya kar'ba, ya sanya shi atsakanin hannuwansa, sannan yayi addu'a. Sannan yace min: "KAR'BI, KA SANYA SHI ACIKIN JAKAR DA KAKE ZUBA GUZURINKA ACIKI. KUMA DUK LOKACIN DA ZAKA CI DABINON, KA SANYA HANNUNKA KA DEBO DAGA CIKIN JAKAR, AMMA KAR KA JUYE". Sai nace "to". "Wallahi Sai da na rika ciyar da mutane masu yawa, kuma ina yin sadaqah daga cikin wannan dabinon.. Kullum aciki nake ci nake sha. Ban ta'ba rabuwa da wannan jakar ba. Duk inda zanje tana nan a kwuibi na." Na ci-gaba da cin Wannan dabino (Babu yankewa, babu Qarewa), Har Manzon Allah (saww) yayi wafati, Har Tsawon lokacin Khalifancin Sayyiduna Abubakar Da Sayyiduna Umar, da Sayyiduna Uthman. (Allah ya yarda dasu)" Yayin da Aka kashe Sayyiduna Uthman (ra), Sai...

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA AZZALUMAI

Idan kana tsoron cutarwa daga wani mutum, ko kana fuskantar cin mutunci daga gareshi, ko daga Jama'arsa, to ga addu'ar da zaka karanta domin samun kariya daga Allah. Kuma aniyarsu zata koma kansu in sha Allah. Ga addu'ar nan kamar haka: اللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَاراً مِنْ (اِسمُه) وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ، أَن يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ وَجَلَّ ثَنَائُكَ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا أَنْت Allaahumma Rabbas-samaawaatis-sab'i, wa Rabbal-'Arshil-'Azeem, kun lee jaaran min (Sai ka ambaci sunansa), wa 'ahzaabihi min khalaa'iqika, 'an yafruta 'alayya 'ahadun minhum 'aw yatghaa. 'azza jaaruka, wajalla thanaa'uka, wa laa 'ilaaha 'illaa 'Anta. Ya Allah, Ya Ubangijin Sammai bakwai! Ya Ubangijin Al'arshi mai girma! (Ina rokonka) Ka zama Mafaka agareni daga sharrin wane (Sai ka ambaci sunansa) dashi da jama'arsa daga cikin halittunka. ...

TARIHIN MAGABATA NA KWARAI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Shugaban dukkan bayin Allah, wanda Allah ya kebanceshi daga cikin Dukkan Annabawa da Manzanni, kuma ya kebanci al'ummarsa daga cikin al'ummatai, Kuma ya kebanci Sahabbansa da iyalan gidansa da girma da kusanci mafifici. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalansa da Sahabbansa. Yau insha Allahu zamu dora ne daga inda muka tsaya acikin Darasinmu mai suna: TARIHIN MAGABATA NA KWARAI. Mun riga munyi tarihin Sayyiduna Abubakar da Sayyiduna Umar (Allah shi Qara musu yarda). Yanzu kuma insha Allahu zamu shiga cikin tarihin Khalifa na Uku wato Sayyiduna Uthman bn 'Affaan (ra). Acikin jerin darussan da zasu biyo baya, insha Allahu zamuyi magana akan tarihin nasabarsa, da Martabobinsa, da ayyukansa, da Siffofinsa, da Khasa'isunsa wato abunuwan da ya kebantu dasu. Ga wasu Daga cikin Martabobinsa agurguje: 1. Shine kadai mutumin da ya taba aurar 'Ya'ya biyu daga cikin 'ya'yan wani Annabi daga c...

RANAR DA MUMINI ZAI BAR DUNIYA

----------------------------------------- Ita ce rana mafi alkhairi agareshi,, ita ce ranar da Allah zai cika masa alkawarinda yayi masa. Ita ce ranar da zai fita daga wannan Quncin na duniya, izuwa yalwar arziki da ni'ima da farin ciki marar yankewa. Za'a turo masa Mala'iku cikin kyawawan suffofi tare da Qamshin yanayi. Suna murmushi suna rarrashinsa suna gayamasa irin kyawawan sakamakon da Allah ya tanadar masa. Zasu nuna masa ainihin masaukinsa na Aljannar ni'imah. Yana cikin kallo za'a zare masa ransa ahankali cikin nutsuwa zai ciki da kalmar LA'ILAHA ILLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI (sallahu alaihi wa sallam)"

“Daga cikin Suffofin Masoya MANZON ALLAH s.A.w ”

جاء في حديث : ' Yazo Acikin Hadisi: ﺟﻠﺲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﻣﻊ ﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﻭﺳﺄﻟﻬﻢ ﻣﺒﺘﺪءا ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ : ' Watarana Manzon Allah s.A.w Yazauna acikin Sahbbansa R.t.A, Yana Tambayansu acikin Lamauran Duniya. Sai Yafara da Syyna Abubakar As-Saddeeq R.t.A: « ﻣﺎﺫﺍ ﺗﺤﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ؟ » ' « ME KAKESO DAGA (Lamuran ) DUNIYA» ﻓﻘﺎﻝ أﺑو ﺑﻜﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : « ﺃﺣﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺛﻼﺙ : _ ﺍﻟﺠﻠﻮﺱ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻳﻚ _ ﻭﺍﻟﻨﻈﺮ إﻟﻴﻚ – ﻭﺇﻧﻔﺎﻕ ﻣﺎﻟﻲ ﻋﻠﻴﻚ » ' Sai Syydna Abubakar R.t.A Yace: " Ya Rasulallah ! Ni acikin Duniya Inason Abubuwa Uku(3): (A) Inason Nariga zama a Gabanka. (B) Inson Naringa Kallonka. (C) Inson Nakashe Dukiyata a Gareka. قال : « ﻭأﻧﺖ ﻳﺎ ﻋﻤﺮ ؟ » ' Sai Manzon Allah s.A.w Yace: « KAI KUMAFA ? YA UMAR» قال : « أﺣﺐ ﺛﻼﺙ : _ أﻣﺮ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺳﺮﺍ – ﻭﻧﻬﻲ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺟﻬﺮﺍ – ﻭﻗﻮﻝ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻣﺮﺍ » ' Sai Syydna Umar R.t.A Yace:" Ya Rasulallah ! Nima Inason Abubuwa Uku(3): (A) Inson Naringa yin Umarni da Aiki Mai Kyau, koda a Boye ne. (B) Inason Naringa yi...

HALACCIN AURE BAYAN ZINA

ASLM.malan da fatan kana lafiya kuma Allah ya kyautattama da kyakkyawan alkhairi ga bisa kokarin da kakke muna kulun, muna godiya kwarai ga wanan zauren saboda mafificiya karuwa dake ciki.. Muna so malan ka warware muna wata gardama. mutun ne da budurwarsa sai kaddara ta samesu SUKA YI ZINA har suka aifi daa guda ko biyu a tsakanin su. shin aure ya halatta tsakanisu daga bayan aihuwar da sukayi..dan Allah muna jiran amsa nagode... (Daga wani bawan Allah). AMSA * **** Mafiya yawan Jamhurin Malamai sun tafi akan cewa Haramun ne Mazinata su auri junansu, ko wani dabam. Har sai bayan sun tuba, cikakkiyar tuba wacce take Qunshe da nadama abisa laifukan da suka aikata, tare da daukar niyyar cewa ba zasu saje aikatawa ba, da kuma bear n aikata wannan mummunan aikin da kuma dukkan dangoginsa. da abubuwan da zasu iya kaiwa izuwa aikatawar. Hujjah anan ita ce Ayah ta 3 aciin Suratun Nuor, Allah madaukakin Sarki yana cewa: "MAZINACI BA ZAI AURA BA SAI DAI MAZINACIYA KO MUSHRIKA, KUMA BABU MA...

SUNAYEN ALQIYAMAH

1. RANAR TUHUMA. 2. RANAR QWANKWASAR ZUKATA. 3. RANAR TARUWA. 4. RANAR RARRABUWA. 5. RANAR TASHI. 6. RANAR TSAYUWA. 7. RANAR FIRGITA. 8. RANAR DAKE SANYA JARIRAI FURFURA. 9. RANAR DA KE SANYA MAI SHAYARWA TA JEFAR DA JARIRINTA. 10. RANAR DA KE SANYA MAI CIKI TA HAIFE BATA SAN A HAIFE BA. 11. RANAR DA MUTUM ZAI GUJE WA 'DAN UWANSA, DA UWARSA DA UBANSA, DA MATARSA DA 'YA'YANSA. 12. RANAR KARBAR SAKAMAKO. 13. RANAR GANGARAWA. 14. RANAR TONUWAR ASIRAI. 15. RANAR RARRABA TAKARDU. 16. RANAR KARBAR SAKAMAKO. 17. RANAR CIKAR ALKAWARI. 18. RANAR DA SAMA ZATA TSATSAGE TA KEKKECE. 19. RANAR DA SAMA ZATA ZAMA KAMAR NARKAKKIYAR DALMA. 20. RANAR DA DUWATSU ZASU NIKE SU ZAMA KAMAR AUDUGA. 21. RANAR DA MUTANE ZASU ZAMA KAMAR FAARI. 22. RANAR DA IDANUWA ZASU KAKKAFE. 23. RANA MAI AFKUWA. 24. RANAR NADAMA. 25. RANAR DA BABU WAJEN GUDU, BABU MAFAKA, BABU MATSERA. Ni dai na fake da Manzon Allah (saww). Ya Allah ka sanyamu acikin cetonsa, ka tashemu karkashin Tutarsa don matsayinsa gareka, don ...

WASU MAZAN ZAMANI DA HALAYENSU

1. Akwai Dangata wanda bai damu da bin karantarwar addini ba, Sannan bai dauki Iyayen matarsa abakin komai ba. Nasa iyayen ma, Sai abinda yake so suke yi masa. Kuma idan sukayi rikici da matarsa, Iyayensa sukan goya masa baya ALWAYS. 2. Akwai kuma wanda yana da kokarin kula da iyalinsa daidai gwargwado. Sai dai kuma Akwai fada!! babu sassauci. Idan ya fara masifa, gara ma kiyi shuru ki saurara. 3. Akwai Kuma KAZGE wanda bai iya komai na addini ba, Sai girman kai awajensa kamar Sarki!! Sallah ma bata dameshi ba, Sak yaga dama yakeyi. Kuma idan kikayi masa nasiha sai yace miki "KABARINKI DABAN, NAWA MA DABAN". 4. Akwai SOLOLO wanda shi bashi da wani ra'ayi nasa na kansa. Sai abinda abokansa suka gaya masa. Yawancin sirrin gidansa ma, sai ya kwashe ya kai dandalin abokansa ya baje koli.. 5. Akwai kuma MAI HALIN MATA, wato Gulma, Qananan maganganu, Annamimanci, duk halayensa ne. Yawancin irinsu basu damu da tsafta ba, kuma basu cika shiga mutane ba. 6. Akwai kuma GIZO wanda b...

INA KUKE GWANAYEN IYA TSARE YAM MATA?

IN KAI NE YA ZAKAYI? Wani saurayine yana zaune, sai yaga wata budurwa yar dai-dai, yar duma-duma, ta dan dire ta baje... Nan danan yawun bakinsa ya tsinke, baikoyi kasa a gwiwa ba tana wucewa ya bita. Yana zuwa yai sallama yana murmushi yace," yammata adon gari, naganki da wata katuwar jakace kamar wanzamiya, ko wanzanci kikeyine?". Ta daure fuska tace," eh yanzuma daga wajen babanka nake naje nayi masa kaciya!" in kaine shin zaka barta ta wuce lafiya ko qaqa? Ko kuma akwai hanyar da zakabi ka shawo kanta kucigaba da buga soyyy! Gareku gwanayen iya tasan yam mata...!

ASHE KARUWANCI BA SANA'AR YI BACE! Karuwanci sana'ar banzace ba uwar kudi bare riba.

INA MATA MASU YIN? (Social Network) don karuwanci ku saurara kujini wata budurwa ce ta nemi izinin mahaifiyarta domin ta amince mata ta dinga neman maza wato (Zina) sai uwar tace zata amince mata amma sai taci wata Jarrabawa da zatayi mata. Uwar tace tanaso taje kofar Fada idan SARKI ya fito ta yanke jiki ta FADI ta sansandare, Aikuwa haka akayi da SARKI ya fito yarinya ta fadi tayi kamar ta suma, sai ko SARKI da kansa ya sauka daga DOKI ya dagata data bude Ido ya tabbatar ta tashi sai yakoma kan doki sukaci gaba da tafiya, bayan ta koma gida sai ta gayawa Uwar abinda ya faru. Sai Uwar tace washegari taje ta maimaita abinda tayi arana ta 2 ko data fadi sai SARKI ya wuce sai WAZIRI ne yatsaya, bayan ta koma sai Uwar tace taqara komawa washegari ta maimaita haka. Da taje a wannan karon na 3 ba wanda yakulata sai SARKIN DOGARAI ne ya tsaya yarinya bata fasa ba tana maimaita abinda Mahaifiyarta take umartar ta da shi, har wata rana ta je sai Yarane suka korota da Jifa suna mata iihu. Anan ...

HAUSA SAI DAN HAUSA KARANTA KASHA MAMAKI

2015: Kifi yace wa kwado mukam mun shiga uku kwado yace malam kifi me kagani ne? kifi yace kugiya naga an jefo mana cikin ruwa ana kama mu ana kashewa lallai shugaban mu Dorina azzalumi ne kwado yace ai harda mu kwadi ake kamawa yanzu domin ko jiya ma naji a labarai ana cewar duk wanda bai zabi Dorina ba a 2015 za'a masa suyan gyadar Basakkwace kifi yace to kaga dole mu zabe shi kuwa kwado yace a'a kam ai da girma ya fadi gara jari ya karye, to menene mafita kwado yace a 2015 zamu fita aruwa mu hau tudu wurin su Kura da Damisa in zasuyi zabe mu zabi Biri ko babu komai daji zai wadata da amfanin gona, kifi yace "Sadaqta" kayi gaskiya, kwado yace lokacin da 'Yar bishiya tayi mulkin daji an samu Mangoro da ganyen ci amma tunda 'yar bishiya ta mutu muka shiga wahala Dorina sai duka,kifi yace Dabbobin daji ne suke taimaka masa ai irin su Shaho,Dila,Hankaka da Zomo kwado yace naji Kace harda Dila shi ba mai sarauta bane? meye ya hadashi da siyasa, kifi yace hmm ai d...

UWA-UWACE WALLAHI

Wata rana wani yaro ya tafi makaranta to dab da za'a tashe su sai aka fara ruwan sama, shi kuma yaron yana jin yunwa idan ya tsaya be san sanda za'a gama wannan ruwan-ba. Ya dan tsagaita ya jira kadan yaga ruwannan babu alamar tsayawa, kawai sai ya kutso kai ya taho gida da gudu. Yana zuwa gida ya shiga cikin daki, nan ya tarar da yayar-sa, da yayyen-sa maza guda 2 da baban-sa da babar-sa a zaune a daki suna cin abincin rana. Kawai ya shigo cikin daki kayan jikinsa a jike. Babansu ne ya fara yi masa magana da tsawa; ~--► "Wawa, me yasa baka tafi da Lema ba? "Umbrella" Sannan babban yayansu; ~--► Mtsewww! Yai tsaki se kaje mura ta kama-ka. Sannan yayarsa; ~--► To me yasa baka tsaya an gama ruwanba? Sannan dayan yayan nasa; ~--► Dallacan tsaya daga bakin kofa kar ka jika kafet "Carpet" Nan take se yaron ya fashe da kuka... Babarsa ce kawai bata hantareshi ba ta dauko tsumma ta goggoge masa fuskarsa, ta bashi wasu kayan ya saka. Kayi alfahari da mahaifiyar...

BARI KUJI IRIN AZABAR DA AKEYIWA MASU YIN ZINA

Hadithin da samurata dan jundub ya ruwaito, cewa Manzon ALLAH (S.A.W) Mala'ika Jibril da Mika'il sun zo maSa, Ya ce (S.A.W):"Mu ka tafi, sai Mu ka isa gun wani abu kamar tukunya, samanta tsukakke qasarta mai fadi, ihun muryoyi na fita daga ciki, sai Mu ka leqa, Muka ga maza da mata babu tufafi, sai ga wuta na zuwa musu ta qasa, idan wutar ta ta6esu sai su qwala ihu, sai Na ce(S.A.W) Ya Jibril su waye wa'ennan? sai Ya ce:"su ne mazinata maza da mata." hadithin na cikin sahihul bukhari YA ALLAH KA yi mana tsari daga wannan mummunan laifin

LABARIN WANI MUTUM DA MUTUWA TA RISKESHI

Wani daga cikin magabata, wanda ma shiba musulmi bane. Dayazo mutuwa yasa aka kira masa manyan sojojinsa sai yace musu, yanason su cikamar wasu wasiyoyi gudu uku, idan mai yanke kauna ta daukeshi. Wasiyoyin kuwa sune kamar haka: 1. Likitocin da sukafi kowa kwareya a fadin kasarsa, su yakeso sudauki akwatin gawarsa sufito da'ita bainar jama'a kafin aje a binneshi. 2. Dukkan abin daya mallaka na kudi dana zinari ko azurfa, yanason a tattarasu a watsasu a hanyar daza'a bi da gawarsa zuwa makabarta. 3. Hannayensa kuma yace yanason a barsu a wajen akwatin suna Lilo inda kowa dake wajen zai iya gani. Wani daga cikin sojojin nasa sai yayi mamakin wannan abun saiya tambayeshi karin bayani shi kuma sai yace: 1. Inason likitoci su dauki gawatane domin na nunawa mutane cewa yayinda mutuwa tazo ko da likitocin da sukafi kowa kwarewane, baza su iya warkadda mutum ba. 2. Inason a watsa dukiyata akan hanyane domin mutane susan cewa duk abinda aka samu a duniya, a duniya ake barinsa. 3. In...

LABARI MAI BAN AL'AJAB DAURE KA KARANTA,TABBAS ZAI AMFANE KA

Wani mutum ne yashirya yin wata tafiya. Ya dauki matarsa da ’ya’yansa cikin motarsa suka kama hanya. Ba su yi nisa ba suka hadu da wani mutum tsaye a bakin hanya.Ya daga musu hannu suka tsaya, ya nemi su dauke shi. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce, “Ni ne dukiya.” Nan take iyalin suka dau sowar cewa ga abokin tafiya, maganin takaicin duniya. Suka ce lallai a dauke shi su tafi tare. Dama motar irin babbar Jif din nan ce mai yalwar mazaunai, sai suka dauke shi suka tafi. Suna yin gaba kadan sai suka tarar da wani mutumin, shi ma a bakin hanya yana daga musu hannu, sai maigida ya tsaya. Ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne sarauta da matsayi.” Iyalan na jin haka suka ce a dauko shi, domin babu abin da yin sa zai gagari mutum a duniya, muddin yana da sarauta da matsayi. Shi ma suka dauke shi suka wuce. Suna kara gaba kadan sai ga wani mutumin tsaye a gefen hanya, shi ma ya daga musu hannu suka tsaya. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne Addini.” Maigida ...

DAGA SHEIKH HAMBALI YUSUF (HAFIZAHULLAH).

SABUWAR SHEKARA TA MUSULUNCI * ADDU'AR KARSHEN SHEKARA*** Duk wanda ya karanta wannan addu'ar a yau, duk barna da tabargazarar da shedan ya sanya shi yayi cikin wannan shekarar, ta ruguje, watau an yafe mashi, in sha Allahu. Yau Alhamis ne 29 ga watan Zulhajji shekara ta 1435, yau ne rana ta karshe a wannan shekarar ta musulunci. In sha Allahu gobe Juma'a ne 1 ga Muharram na Shekara ta 1436. Ya kamata duk musulmi ya kula, ya gane wannan lissafi na shekarar musulunci shine ya samo asali tun daga Annabi SAW, kuma dashi Annabi SAW ya bada umurnin a rika lissafi ba wancan na miladiyya watau na turawa da ake amfani dashi ba. Akwai addu'ar da ake yi ranar karshe ta shekara, da kuma rana ta farkon shekara. A duba MUJARRABATUL DAIRABIYL KABIYR, Ta'alifin Asshaikh Ahmad Addairabiy, za'aga cikakken bayanin. Ga addu'o'in kamar haka: * ADDU'AR KARSHEN SHEKARA*** Zaka ce: "Bismillahir Rahmanir Rahim. Sallallahu Ala Sayyidina Muhammadin Wa'ala Alihi Wasah...

Jihar Jigawa Zata Goyi Bayan Shugaba Jonathan A 2015- Walin Dutse

A firar da yayi da wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari, Alhaji Bashir Dalhatu, Walin Dutse yace ya gana da shugaba Jonathan kuma zasu goyi bayansa domin ya nunawa jihar da mutanenta kauna. Alhaji Bashir Dalhatu yace ya fadawa shugaban kasa cewa ya ziyarci jihar kaman sau hudu ke nan tunda ya kama mulki abun da ya nuna cewa yana kaunar jihar. Duk lokancin da ya zo jihar yana yi masu alkawura kuma yana cikasu. Ya yiwa jihar ayyuka. Misali ya gina makarantu da jami'a da tituna da bunkasa ayyukan harkokin noma da kuma sabon filin saukar jiragen sama da ma wasu abubuwa da dama dake kara inganta jihar.

CIWAN SANYI

Cutar sanyi. Ita cutar sanyi a manya ana kamuwa da ita ta hanyar saduwa ne.duka maza da mata suna kamuwa da ita.sannan a yara kuma abun yakan zama tsautsayi misali su kwayoyin cutane dake haddasa ma yaro karami ciwon sanyi.sannan akwai ciwon sanyi na yara mata kamun su balaga wadanda basu ta6a saduwa dana maji ba. a bayyane ita cutar gonorrhoea a maza tana sa bututun dake dakko fitsari ya kumbura, kuma ya dau ruwa,sannan se mutm ya rinka jin zafi wajen fitsari Cutar kuwa a mata bututun dakko fitsarinta zai kumbura sannan tsokar cervix dinta zata kumbura sannan falofiyan tube shima zai iya kumbura. Ita wannan cuta ta gonorrhoea ma.ana sanyi ba data shigake zaka fara jin alamu ba. A.a takan kyankyashe kwanta ne daga kwana 2 zuwa 5. Hanyoyin maganin wannan cuta a. Kada a sadu da macen da ba'a santa ba. B. Tsaftace gaban yara mata da kanan yara. C. Yin amfan da kwanda yayn saduwa. Allah kare mu

Harsashe uku-uku akan mantan mu na AREWA

1. Idan kana son mace mai abu uku (ILMIN ZAMANI, WAYEWA DA RASHIN TARBIYYA) Tafi KADUNA. 2. Idan kana son mace mai (SHAN SIGARI, DURA ASHARIYA DA MALLAKAR MIJI) Garzaya KATSINA. 3. Idan kana son mace (GAJERA, KAKKARFA-KIRAR DOYA DA BIYAYYA KAMAR TA YI MAKA SUJJADA) maza hanyarzata zuwa NEJA 4. Idan kana son mace wadda ba ta (IYA GIRKI BA, RASHIN IYA HIRA AMMA AKWAI TA DA TSAFTA) Ta fi KANO. 5. Idan kana neman mace wadda ta (IYA SOYAYYA, KYAU DA KUMA RASHIN ILMI) Tafi ADAMAWA 6. Idan kana son mace mai abu uku (GIDADANCI, KAUYANCI DA RASHIN KUNYA) Tafi ZAZZAU 7. Idan kana neman mace mai (HAKURI, LADABI DA BIYAYYA) Tafi YOBE 8. Idan kana neman mace mai abu uku kamar (MASIFA, SON KUDI, KAUYANCI) Tafi SOKOTO 9. Idan kuma kana neman mace (‘YAR GAYU, RASHIN IYA SOYAYYA DA SON TARA ABIN DUNIYA) tafi GOMBE 10. Idan kana neman mace wadda take abubuwa uku kamar (SON KUDI, AUREN KARYA DA KYAU) Tafi MAIDUGURI 11. Idan kana son mace mai abu uku (RASHIN IYA WANKA, RAINA AURE, KAUYANCI) Tafi JIGAWA 12...

MAGANIN HANA ZINA

HANYOYI 12 DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA AIKATA ZINA. Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine: 1. tsayuwa abisa tafarkin Allah da gaskiya. 2. Cikakken Tsoron Allah a zuciya. Tare da kwadayin samun Rahamarsa. 3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar. 4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe. 5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki. Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba’irar 6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA a lahira. 7. Tuno wa shaitan da kuma kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam. 8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba. 9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki da hotunan batsa. 10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya. 12. Addu’ar neman tsari daga munanan ayyuka, da mummunan tunani. “Allahumma inni a’uzu bika min Mun...

HARAMUN NE YAYI AURE

Duk wanda zaiyi aure, wajibi kafin ya fara neman aure yaje wajan malamai ya karanta, yadda aure yake, kuma yasan matsayin sa, a wajan aure, domin an kasa mutane masu bukatar aure kashi biyar, 1- Wanda ya zama wajibi yayi aure, shine wanda idan baiyi aure ba, zai fada zina ko luwadi, ko zina ko madigo ga mace, 2- Wanda aure ya zama haramun a gareshi, shine wanda, bazai iya rike auran ba, da daukar nauye- nauyan sa, da dukkan hakkin lyalai na wajibi 3, Mustahabbi yayi aure, shine wanda idan yayi aure zai kara masa kwazo wajan bin Allah, tare da kiyaye hakkin iyali 4- Makaruhi yayi aure, shine wanda, baya tsoran zina idan baiyi aure ba, kuma yin auran zai rage masa kokari wajan ibada, da neman ilmi, wannan ya shagala da ibadarsa, yafi yayi aure, kamar yadda aka sami malamai da yawa akan haka kamar Ibn taimiyya da Annawawiy. 5- Wanda ya zama halal yayi aure ,shine wanda bashi da shaawa mai karfi, koma auran bai damaishi ba, babu abinda zai samu na kari ko ragi, akan auran face, kawai yana ...

manzon allah yayi gaskiya (saw)

1. Annabi S.A.W. yache: "Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad sau 10 a jere, Allah zai Gina masa katafaren gida achikin Aljanna". [Sahihul Jami'i. 6348] 2. Manzon Allah S.A.W. yache: "Wanda ya karanta Ayatul Khursiyyu bayan kowache Sallah ta farilla, babu abunda zai hanashi shiga aljanna saidai Idan bai mutu ba. [Sahihul Jami'i] 3. Manzon Allah S.A.W. yache: "Idan mutum yazo kwanchiyar bacci a saman shimfidarsa toya karanta Qulya ayuhal kafirun, falalar yin hakan shine; Idan mutum ya mutu achikin daren bazai mutu mushiriki ba" [Sahihul Jami'i] 4. Manzon Allah S.A.W. Yache: "Wanda ya karanta suratul khahfi ranar juma'a Allah zai haskaka masa da haske harzuwa wata juma'ar yana chikin farin ciki yana chikin jindadi" [Sahihul jami'i] 5. Manzon Allah S.A.W. yache: "Wanda ya haddache ayoyi goma na farkon suratul khahfi, Allah zai tsareshi daga fitinar dujal" [Sahihul Jami'i] 6. Manzon Allah S.A.W. yache: " wanda yayi...

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu. Allah ya bamu ikon kiyayewa. 1- Shirka da kashe-kashenta 2- kisan kai 3 - Tsafi 4- Wasa da sallah 5- Hana zakka 6- Sabawa iyaye 7- Cin riba 8- Cin dukiyar marayu 9- yiwa Annabi saw karya 10- Karya Azumi da gangan 11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini. 12- Yin Zina 13- Shugaba mai hainci ga talakawansa. 14- Shan giya da sarrafata 15- Girman kai da takama da jiji da kai 16- Shedar Zur 17- Luwadi da mdigo 18- Yin kage ga muminai 19- Satar dukiya daga baitul mali 20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba. 21- Sata, da sane. 22- Fashi da makami 23- Rantsuwar karya 24- Yawan karya 25- Wanda ya kashe kansa da gangan 26- Mugun Alkali, 27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi da maza 28- Masu auran kisan wuta 29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir 30- Rashin tsarki daga fitsari. 31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili 32- Munafinci 33- H...

SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI DA ILLOLIN SU!!!

KWAYA ko MAGANI shine duk abinda idan ya shiga jikin dan Adan yake kawo chanjin yanayi cikin kwakwalwa ko jikinsa ta kowani fanni, misali kota hanya sha ne, shafawa ne, shaqawa ne kokuma ta yin allura. MIYAGUN SHAYE SHAYEN: - Shan maganin da doka ta hana amfani dashi. - Shan Magani berkete batare da izinin likita ba. - Wuce umurnin likita wajen shan kwayoyi. - Shan abubuwan da addinin Musulunci ya haramta. DALILAN DA SUKE SA JAMA'A SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI; 1) Jahilci 2) Matsalolin Rayuwa 3) Al'adu 4) Hada hadan siyasa 5) Hurda da abokan banza 6) Sakacin iyaye wajen tsawata wa yara 7) Yanayin wurin zama 8) Aikin karfi (leburanci) 9) Samun kwayoyin cikin sauqi Da sauran su.... WASU DAGA CIKIN MIYAGUN KWAYOYIN DA AKAFI AMFANI DASU; 1) Tabar wiwi (Indian Hemp) 2) Sholisho 3) Hodar Aljanu (cocaine) 4) D5 (Valium, Diazepam, Exol 5) 5) Taramol (tramadol) 6) Kashin kadangare 7) Afarci kasa (pemoline Tablet) 8) Hodar Iblis (heroine) 9) Maganin mura da akesha ba bisa ka'ida ba k...

INGANTACCIYAR ADDU'A WACCE AKE KARANTA MARA LAFIYA LOKACIN DA AKAJE DUBASHI.

Assalamu Alaikum Malam wacce adu'ace manzon Allah tsira da aminci su tabbata agareshi yayi umarni da akaranta ga mutumin da bashi da lafiya ??? (Daga Abubakar Hamza). AMSA ----- DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. An kar6o daga Abbas (R.A) yace: Annabi (s.a.w) yace: Babu wani mutum musulmi da zaije gaishe da wani Musulmi maraya lafiya, wanda ajalinsa baizo ba yace: ''AS'ALULLAHAL AZEEM RABBAL ARSHIL AZEEM AN YASHFIYAKA'' ««fassara»» Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma yabaka lafiya. Na rantse da Allah babu wanda zai karantawa mara lafiya wannan addu'ar face sai Allah (s.w.t) yabashi sauki saidai idan cutar ajalice.

SABON TSARIN Blackberry AKAN ANDROID DA LAYIN ETISALAT NG

Ga wanda yake da android kuma yake da etisalat, to ga tsarin amfani da tsarin BB akan android, kuma kayi amfani da surf na etisalat akan android. Domin morar wannan garabasa, sai kayi amfani da wannan settings din. Act Name: etisalat Wap APN: blackberry.net IP ADDRESS: 010.071.170.005 PORT:8080 Ba'a bukatar Username da Password, wato kabar wurin blank. APN TYPE select Default amma banda MMS. AUTHENTICATIVE: not select. DOMIN SIYAN BB BUNDLES AKAN ANDROID. BB Social 499 2*1# N400 BB Social 499 2*2# N100 BB Complete 499 3*1# N500. BB Complete 499 3*2# N100. BIS 499 6# N1000 BIS 499 5# N250.

abin Al’ajabi: Tsuntsuwa Ta Rikide Zuwa Wata Mata

Wani abin al’ajabi ya auku a garin Oshodi da ke jihar Lagos a yau Juma’a, yayin da wata tsuntsuwa ta rikide zuwa wata mata bayan ta fado daga sama. Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka bayyana, tsuntsuwar ta fado daga sama ne sakamakon karo da wayar wutar lanatarki da ta yi a sama, inda daga bisani ta rikide zuwa wata mata mai matsaikacin shekaru. Majiyar ta kara da cewa bayan matar ta rikide zuwa mutum, ta bayyana yadda ta kashe mijinta. Wani ganau ba jiyau ba mai sauna David Gear, wanda ya rawaito labbarin al’ajabin a shafinsa na Twitter, ya fadi cewa “Tsuntsuwa ta rikide zuwa wata mata a garin Oshodi dake jihar Lagos a yanzu a ranar yau da misalign karfe daya na rana. Ta fado ne sakamakon karon da ta yi da wayar wutar lantarki. Da alamar mayya ce matar, kamar yadda bayyananta suka nuna, domin ta fadi cewa har mijinta sai da ta kashe”. Bincike ya nuna cewa jami’an ‘yan sanda ne suka ceci matar daga barazanar dukan kawo wukar da jama’ar da ke wajen da lamarin ya auku suka so yi mata, sa...

cikin wadannan mutum 4 wa zaka ba yar'ka?

1-kana hospital rai a hannun ALLAH, akace 'kodarka' ta lalace sai an chanja maka,, sai ya taimaka ya baka 'kodarsa' 1 aka saka ma 2-kana gidan haya aka koreka, kana fitowa sai ya baka katon gida kyauta, kuma duk abinda kake bukata akwai a gdan 3-an koreka daka wajen aiki, ya baka kudi N5,000,000 KYAUTA yace kaje kayi kasuwanci 4- BARAYI, sun daureka a cikin motarka kuma sunsa bomb a jikinka, sannan yazo ya kashe dukkansu sannan ya ceci rayuwarka Sai kuma gashi dukkansu sunce douhgter dinka suke so su aura Kuma gashi 1 ce da kai, Yanxu wa zaka bawa a cikinsu????

YADDA ZAKA TUNKARI MACE DA MAGANAR SOYAYYA.

RANAR FARKON HADUWA. Dazaran kaga macen da kakeso ko kuma ka dade kana sonta amma karasa yadda zakayi to kada kayi kasa a guiwa kawai kabi wadannan matakan insha Allah zakai nasara. Kada ka tsaida ita inda taron mutane yake domin bazata baka damar yin magana da ita ba, ka kasance mai tsabta sannan ka koyi dressing kafin ka tunkareka hakan zaisa ka burgeta ta samu kwarin gwiwar amsar soyayyarka. Idan kasamu damar gani fitowarta zataje wani wuri sai kabita sannu sannu a baya ammafa ka gyara takunka yadda ko juyowa tayi bazata gane cewa ita kakebi ba, idan kaga ankai wani nitsatsan wuri inda babu hayaniya, sai kayi mata sallama na tabbata zata amsamaka sannan kuma zata tsaya taji mi kakeson ka fada mata Saurayi..... Assalamu alaikum. Zata kalleka da gefen ido, sannan ta amsamaka. Wa alaikassalam. saurayi:.. Don Allah idan bazaki damuba inaso kidan bani minti biyu daga cikin lokacinki. Zatayi maka musu ta fada maka cewa Gaskiya sauri nake banason 6ata lokaci. To kada kadamu, Saurayi:... Do...

HIKAYAR LAILA MAJNUN

Mun tsaya a inda Qais wanda ake yiwa lakabi da “Majnun lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawaLaila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gusheba har saida akayi masa lakabi da “majnun wato (mahaukaci) ! Zanci gaba. Duk dacewa itama Laila tana matukar son Qais wato (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutanma harda yi masa wulaqanci, bayan yin amfani da mallakeshi datayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun acikin wani baiti nasa yace: “Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane ?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I. Daganan Qai yace, saina kasa mallakar idona saida hawaye ya zubo cikin sauri yajiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah yayafe mata laifinta duk d...

HIKAYAR LAILA MAJNUN

------2------ Cigaba....... Mun tsaya a inda wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar Banu Umaiyya, katsam yayi ido hudu daLaila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta. Daga wannan rana Soyayyar Laila tahana Wird yayi bacci a wannan dare ! Cikin yan kwanaki kadan Iyayen Wird suka sauka a gidansu Laila domin neman aurenta ga dansu Wird. A wannan rana da Iyayen Wird sukaje ga mahaifin Lailasaid a suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar ! Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan hakane Mahaifin Laila yakira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana ! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai yayi mata barazanar cewar zai yankata idan har bata amince da auren Wird ba ! ...

S.A.W

Salatin Allah da amincinsa su tabbata abisa Shugaban bayin Allah, Rahamar Allah, Hujjar Allah abisa dukkan halitta, wato Manzonmu, Shugabanmu, Macecinmu, Annabinmu MUHAMMADU. Tare da Iyalan gidansa tsarkaka, da Sahabbansa Madaukaka.... Albarkacin wannan salatin, Ya Allah ka sadamu da dukkan alkhairan da kake saukar ma bayinka acikin wannan watan, kuma ka amshi dukkan rokonmu, ka sanya mu asahun gaba na Manyan Masoyan Annabinka (s.a.w).

NIKAM INA DA YAN MATA DAYAWA AMMA KO WACE NA TASHI RUBUTA MATA TEX TO DA FARKON SUNANTA NAKE GASU KAMAR

Harafin farko na sunanta shine zanyi amfani dashi wajen furta kalmar soyayya gareta!!! > HAFSAT: Hawayen sonki na kwarara daga idanuwana idan har banji sanyayyiyar muryar kiba. > KØÙLTHÖÜM: Kece kika zamo magani ga duk wasu zaratan zakakan muyagun cutattuka da suka addabi Ruhina na tsawon lokuta. >UMMIZEE ZEE: Uziri baya kasancewa gareni, Domin hukumar dake aiki karkashin Ruhina bazata amince da rashin ganin kiba a duk harbawar Dakika ta Agogo. > YUSURA: Ya ma'abociyar Hankali da tunani, ma'abociyar kyawun asali, babu daga wata fuska danake gani na dauwama cikin farin ciki face furkarki. > AISHA: A bangaren Raina shima abin babu sauki, domin kuwa baya saurarawa wajen kara zurfafa kaunarki. > KHADIJAT: Kece sarauniya mai gudanar da mulki a cikin zuciyata. > FATIMA: Furran kaunarki yayi yadon flower a cikin zuciyata. > HASSANA: Hasken Annurin kaunarki yakan haskaka dausayin Ruhina, ayayinda duhu kan gaggawar fucewa. > MIMA: Murmushinki yana kawata Numfa...

wayo haha

IN KECE YA XAKIYI???? Wata budurwa ce mai shegen jijji da kai, wata rana ita da qawayenta guda biyu suka je gidan iyayen saurayin da za ta aura, bayan sun gama fira ita da saurayinta har dare yayi, sai iyayen saurayin suka ce gaskiya baxa su tafi da darennan ba sai dai su kwana a dakin qannen saurayinta mata, ga shi kuma gidansu akwai nisa daga gidan saurayin, haka suka yarda su kwana a gidan, toh ka san halin qananan yara musamman idan suka ga baqi, sai wata yarinya daga cikin qannen mijin ta ce ita a kusa da aunty xa ta kwana, sai budurwar tace toh ai ba komai,.... Can da dare yayi sai budurwar ta fara mafarkin ga ta nan ta xama kaza tana ta yin qwai, ta yi qwayaye har guda uku, tana cikin yin na hudun sai ta ji qawarta tana ta dukan jikinta tana cewa ''Salamatu meye haka??? Kina ta yin kashin kwance a gidan mutanen duk room dinnan nishinki ake ji, har kin bata wa qanwar usman (saurayin) jiki ga ta can ta ruga wajen mummynta tana kuka'' in ke ce ya xakiyi??? In kuma k...