TUN KAFIN ZUWAN MUSULUMCI

1)Tun kafin zuwan Musulunci Mushirikkan
Makkah suna azumin ashura, Annabi SAW ma ya
azumce shi a Makkah ( Bukhari)



2) Da Annabi SAW yayi hijira zuwa Madinah ya
sami Yahudawa a Madinah suna azumtar shi ya
azumce shi ya umurci Musulmi su azumce shi
(Bukhari)



3) Annabi SAW yace game da azumin Ashurah
ina tsammanin Allah ya karkare zunubban
shekarar da ta wuce (Muslim)



4) Yace : idan na rayu zuwa shekara mai zuwa
zan azumci tara gawata (Muslim)



5) Azumi kawai aka sani a lokacin Annabi SAW
da Abubakar da Umar da Usman da Ali da
Muawiya Allah yayarda da su. Daga baya yan
shia suka kashe Husaini a Karbala ranar ashura
sai mutane suka kasu uku:


(a) Yan shiar da suka
kashe shi suka riki ranar ranar makoki da
bakinciki


(b) Nawasib suka rike ta ranar murna
da cika ciki


(c) Ahlussunnah suka cigaba da
azumi kamar yadda ya tabbata a lokacin Annabi
SAW.


6) Don haka duk Hadissan da sukazo gameda
falalar cika ciki basu inganta ba (Tamamul
Minnah)


7) Tara ga wata (Tasu'ah) zai kasance Lahadi
goma ga wata (Ashrah) Litinin Insha Allah (2nd nov nd 3rd nov 2014)


Allah yasa mu dace

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA