manzon allah yayi gaskiya (saw)

1. Annabi S.A.W. yache: "Wanda ya karanta
Qulhuwallahu Ahad sau 10 a jere, Allah zai
Gina
masa katafaren gida achikin Aljanna".
[Sahihul
Jami'i. 6348]


2. Manzon Allah S.A.W. yache: "Wanda ya
karanta Ayatul Khursiyyu bayan kowache
Sallah
ta farilla, babu abunda zai hanashi shiga
aljanna saidai Idan
bai mutu ba. [Sahihul Jami'i]


3. Manzon Allah S.A.W. yache: "Idan mutum
yazo kwanchiyar bacci a saman shimfidarsa
toya karanta Qulya ayuhal kafirun, falalar yin
hakan shine; Idan
mutum ya mutu achikin daren bazai mutu
mushiriki ba" [Sahihul Jami'i]


4. Manzon Allah S.A.W. Yache: "Wanda ya
karanta suratul khahfi ranar juma'a Allah zai
haskaka masa da haske harzuwa wata
juma'ar
yana chikin farin ciki yana chikin
jindadi" [Sahihul jami'i]


5. Manzon Allah S.A.W. yache: "Wanda ya
haddache ayoyi goma na farkon suratul
khahfi,
Allah zai tsareshi daga fitinar
dujal" [Sahihul
Jami'i]


6. Manzon Allah S.A.W. yache: " wanda yayi
Alwalla ya kyautata ta, bayan yagama sai
yache; Ash hadu anla'ilaha ilallahu wahdahu
lasharikalahu wa'Anna Muhammadan
Abduhu
warasuluhu, Allahumma Ja'alna
minattawabina
waja'alna minal muta
dhahirina, Za'a budema mutum qofofi na
aljanna guda 8 yazabi qofar dayakeso
yashiga" [Sahihul Jami'i]


7. Abdullahi Dan Umar Yache; wata rana
mun
kasanche muna Sallah bayan Manzon Allah
S.A.W. da Annabi ya dago daga ruku'u sai
yache SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAHU sai
wani mutum a cikin sahabbai yache;
RABBANA
WALAKAL HAMDU HAMDAN KHATHIRAN
DAYYUBAN MUBARAKAN FIHI MUBARAKAN
ALAIHI KAMA YUHIBBU RABUNNA
WAYARDA.
Da akai sallama sai Manzon Allah S.A.W. ya
waiwayo yache: wanene ya fadi wannan
kalmar? Sai sahabin yache nine ya
rasulillah,
sai Annabi SAW yace; Naga mala'iku Talatin
da
'yan kai sunata Rige-Rigen (Gaggawar)
wazai
rubuta wannan aikin ya kaima
Allah" [Bukhari]

8. Annabi S.A.W. yache: "wanda yayi Raka'a
12
ta nafila tsakanin dare da rana Allah zai
gina
masa gida a cikin gidan Aljanna" [Sahihul
Jami']


9. Annabi S.A.W. yache wanda ya kiyaye
yanayin Raka'a 4 ta nafila kafin Sallar
Azahar
da kuma Raka'a hudu ta nafila bayan sallar
Azahar Allah zai
haramta masa shiga wuta" [Sahihul Jami'i]


10. Annabi S.A.W. yache: "Allah yajiqan
wanda
yayi Sallah Raka'a 4 kafin sallar
la'asar" [Sahihul Jam'i]


11. Annabi S.A.W. yace: "Wanda yake
karanta
ayoyi 10 da daddare baza'a sanyashi cikin
Gafalallu ba, wanda yake karanta ayoyi 100
da
dare za'a rubutashi cikin (Qanitina) wato
masu
bauta ga Allah, Wanda yake karanta ayoyi
dubu
kullum za'a rubutashi daga chikin masu
arzikin
lahira" [Sahihul Jami'i]


12. Manzon Allah S.A.W. Yache: "mutum
yayi
Sallar Nafila inda babu Wanda ke ganinsa
(cikin
duhu), Allah zai linka masa lada sau 25
fiyeda
kayi
a gaban jama'a suna ganinka" [Sahihul
Jami'i].
Allah ya datar damu akan gaskia yasa mu
mutu
muna masu imani. Ameen.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA