HARAMUN NE YAYI AURE

Duk wanda zaiyi aure, wajibi kafin ya fara neman aure yaje wajan malamai ya karanta, yadda aure yake, kuma yasan matsayin sa, a wajan aure, domin an kasa mutane masu bukatar aure kashi biyar,

1- Wanda ya zama wajibi yayi aure, shine wanda idan baiyi aure ba, zai fada zina ko luwadi, ko zina ko madigo ga mace,

2- Wanda aure ya zama haramun a gareshi, shine wanda, bazai iya rike auran ba, da daukar nauye- nauyan sa, da dukkan hakkin lyalai na wajibi

3, Mustahabbi yayi aure, shine wanda idan yayi aure zai kara masa kwazo wajan bin Allah, tare da kiyaye hakkin iyali

4- Makaruhi yayi aure, shine wanda, baya tsoran zina idan baiyi aure ba, kuma yin auran zai rage masa kokari wajan ibada, da neman ilmi, wannan ya shagala da ibadarsa, yafi yayi aure, kamar yadda aka sami malamai da yawa akan haka kamar Ibn taimiyya da Annawawiy.

5- Wanda ya zama halal yayi aure ,shine wanda bashi da shaawa mai karfi, koma auran bai damaishi ba, babu abinda zai samu na kari ko ragi, akan auran face, kawai yana da mata.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA