MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.
Allah ya bamu ikon kiyayewa.


1- Shirka da kashe-kashenta


2- kisan kai


3 - Tsafi


4- Wasa da sallah


5- Hana zakka


6- Sabawa iyaye


7- Cin riba


8- Cin dukiyar marayu


9- yiwa Annabi saw karya


10- Karya Azumi da gangan


11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.


12- Yin Zina


13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.


14- Shan giya da sarrafata


15- Girman kai da takama da jiji da kai


16- Shedar Zur


17- Luwadi da mdigo


18- Yin kage ga muminai


19- Satar dukiya daga baitul mali


20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.


21- Sata, da sane.


22- Fashi da makami


23- Rantsuwar karya


24- Yawan karya


25- Wanda ya kashe kansa da gangan


26- Mugun Alkali,


27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi
da maza


28- Masu auran kisan wuta


29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir


30- Rashin tsarki daga fitsari.


31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili


32- Munafinci


33- Ha'inci


34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani


35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi,.


36- Karyata kaddara


37- magulmaci


38- Mai yawan laantar mutane


39- mayaudari


40- Gasgata bokaye da yan tsibbu


41- Mace mai tsiwa ga mijinta


42- Rashin sada zumunta


43- Sassaka gumaka


44- Annamimanci


45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi)


46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.


47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.


48- Kafurta mutane,babu dalilin daga sharia


49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.


50- Zagin waliyai da bayin Allah malamai.


51- Jan tufafi a kasa,


52- Sanya tufafin alhariri,


53- Yanka dabba da sunan wani. ba Allah ba.


54- Wanda ya shiga iyakar kasar wani, ko
gonar sa ko filinsa.


55- Zagin sahabbai.


56- Mace mai karin gashi.da zane, da yin
wushirya da aske gashin gira.


57- Kiran Mutane zuwa ga bata, ko koyar da barna.


58- Wanda yake yiwa dan uwansa barazana da
makami.


59- Mai daukan rahoton musulmi yana kaiwa
makiyansu.


60- Tauye mudu


61- Jayyaya da musu mara amfani a cikin addini


62- Mutumin da baya jingina kansa ga iyayansa.


63- fidda tsammani daga Rahmar Allah.


64- Camfi


65 - Shan ruwa ko abinci a kofin zinarai.


66- Gaba da juna


67- Butulci


68-Caca


69- Keta alfarmar haramin Macca da Madina.


70 - Cin Zarfin makoci.


ALLAH YA TSARE MU.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA