HALACCIN AURE BAYAN ZINA

ASLM.malan da fatan kana lafiya kuma Allah ya kyautattama da kyakkyawan alkhairi ga bisa kokarin da kakke muna kulun, muna godiya kwarai ga wanan zauren saboda mafificiya karuwa dake ciki..

Muna so malan ka warware muna wata gardama. mutun ne da budurwarsa sai kaddara ta samesu SUKA YI ZINA har suka aifi daa guda ko biyu a tsakanin su. shin aure ya halatta tsakanisu daga bayan aihuwar da sukayi..dan Allah muna jiran amsa nagode...

(Daga wani bawan Allah).

AMSA
*****
Mafiya yawan Jamhurin Malamai sun tafi akan cewa Haramun ne Mazinata su auri junansu, ko wani dabam. Har sai bayan sun tuba, cikakkiyar tuba wacce take Qunshe da nadama abisa laifukan da suka aikata, tare da daukar niyyar cewa ba zasu saje aikatawa ba, da kuma bear n aikata wannan mummunan aikin da kuma dukkan dangoginsa. da abubuwan da zasu iya kaiwa izuwa aikatawar.

Hujjah anan ita ce Ayah ta 3 aciin Suratun Nuor, Allah madaukakin Sarki yana cewa:

"MAZINACI BA ZAI AURA BA SAI DAI MAZINACIYA KO MUSHRIKA, KUMA BABU MAI AURAR MAZINACIYA SAI DAI MAZINACI KO MUSHIRIKI, KUMA AN HARAMTA WANNAN (IRIN AUREN) ABISA MUMINAI".

Amma in dai sun tuba, sun koma ga Allah, Kuma matar tayi Istibra'i, to za'a iya daura musu aure. Sai dai kuma wadancan 'ya'yan da suka haifa ta hanyar Zina ba za'a dangantasu da shi Mijin ba. Sai dai adangantasu da Uwarsu.

Babu gado tsakaninsu da wanda yayi ma uwarsu cikin ta haifesu. Kuma 'Ya'yansu ba muharramansu bane. sai dai wadanda suke Uwa daya dasu.

WALLAHU A'ALAM.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA