WASU MAZAN ZAMANI DA HALAYENSU

1. Akwai Dangata wanda bai damu da bin karantarwar addini ba, Sannan bai dauki Iyayen matarsa abakin komai ba.


Nasa iyayen ma, Sai abinda yake so suke yi masa. Kuma idan sukayi rikici da matarsa, Iyayensa sukan goya masa baya ALWAYS.


2. Akwai kuma wanda yana da kokarin kula da iyalinsa daidai gwargwado. Sai dai kuma Akwai fada!! babu sassauci. Idan ya fara masifa, gara ma kiyi shuru ki saurara.


3. Akwai Kuma KAZGE wanda bai iya komai na addini ba, Sai girman kai awajensa kamar Sarki!!


Sallah ma bata dameshi ba, Sak yaga dama yakeyi. Kuma idan kikayi masa nasiha sai yace miki "KABARINKI DABAN, NAWA MA DABAN".


4. Akwai SOLOLO wanda shi bashi da wani ra'ayi nasa na kansa. Sai abinda abokansa suka gaya masa. Yawancin sirrin gidansa ma, sai ya kwashe ya kai dandalin abokansa ya baje koli..


5. Akwai kuma MAI HALIN MATA, wato Gulma, Qananan maganganu, Annamimanci, duk halayensa ne. Yawancin irinsu basu damu da tsafta ba, kuma basu cika shiga mutane ba.


6. Akwai kuma GIZO wanda bashi da aiki sai Qarya. Yayi ma matarsa Qarya, yayi ma iyayensa Qarya, yayi ma abokansa Qarya... Yawancin irin wadannan zaka ga Matansu ma haka suke.


7. Akwai MAI FUSKAR SHANU... yana fara'a awaje, Amma da zarar ya nufo gida sai ya hade fuskarsa.. Yana shigowa sai kaji gida yayi TSIT!! Matansa da 'ya'yansa kowa ya razana..


8. Akwai kuma RAKUMI wanda Matarsa ta gida take juyashi kamar waina.. Kuma baya fushi sai da fushinta. Wanda duk matar da ta aureshi sai ta zama kamar Baiwar Matarsa Uwargida.


9. Akwai MATSOLO wanda shi ba 'a sanin Sirrinsa. ga Kwauro awajensa. babu isashen Kudin cefane, kuma ga Mita da hancini sai kace Sauro... wannan ba kowacce mace ce take iya zama dashi ba. Domin kuwq ba'a iya burgeshi. komai kikayi masa sai ya kushe.


10. Akwai kuma na kirki wanda yasan abinda yakeyi, Kuma yana iyakar kokarinsa wajen kare hakkin iyalansa.. - Wannan shine wanda Mata suka fi wahalar dashi.

Comments

Popular posts from this blog

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

FARILLAN SALLAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH