abin Al’ajabi: Tsuntsuwa Ta Rikide Zuwa Wata Mata

Wani abin al’ajabi ya auku a garin Oshodi da ke jihar Lagos a yau Juma’a, yayin da wata tsuntsuwa ta rikide zuwa wata mata bayan ta fado daga sama.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka bayyana, tsuntsuwar ta fado daga sama ne sakamakon karo da wayar wutar lanatarki da ta yi a sama, inda daga bisani ta rikide zuwa wata mata mai matsaikacin shekaru.

Majiyar ta kara da cewa bayan matar ta rikide zuwa mutum, ta bayyana yadda ta kashe mijinta.

Wani ganau ba jiyau ba mai sauna David Gear, wanda ya rawaito labbarin al’ajabin a shafinsa na Twitter, ya fadi cewa “Tsuntsuwa ta rikide zuwa wata mata a garin Oshodi dake jihar Lagos a yanzu a ranar yau da misalign karfe daya na rana. Ta fado ne sakamakon karon da ta yi da wayar wutar lantarki. Da alamar mayya ce matar, kamar yadda bayyananta suka nuna, domin ta fadi cewa har mijinta sai da ta kashe”.

Bincike ya nuna cewa jami’an ‘yan sanda ne suka ceci matar daga barazanar dukan kawo wukar da jama’ar da ke wajen da lamarin ya auku suka so yi mata, sakamakon irin kalaman nadamar da ta dinga yi bayan ta rikide zuwa mace.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA