LABARINA Kashi na farko

You are under arrest, shine maganarda na faraji sunyimin lokacinda suke kokarin samin ankwar a hannuna.. Na daga kai na dubesu a tsorace hankalina ya gama tashi da naga yan sanda ne da bakaken kaya sama da goma sun zagayeni nai saurin magana bakina na rawa nace dasu me..ke..f..ar..uwa..ne? Marin da naji ya sauka a fuskata shine abinda ya dakatar dani daga maganar da nake sannan daya daga cikin yan sandan mai jajayen ido da gashin baki yace dani ba kaine muhammadu ba mai dandalin soyayya? Nai sauri na daga kaina na dubesu da naji ya ambaci dandalin soyayya sannan nace eh nine muhammadu me nayi muku kuma?? A lokacin ne mahaifiyata ta fito daga cikin daki itada kanwata liliane lokacin da sukaji hayaniya tana tashi a cikin gidan suna zuwa suka iske yan sanda sun kewayeni sun samin ankwa a hannuna bayin Allah me dana yayi muku? Kukazomin har gida kuke shirin kamashi ku tafi dashi? Yan sandan suka dubeta sannan suka dubeni lokacinda idanunana ya ciko da kwalla ina shirin fashewa da kuka nace dan Allah kumin hakuri mai nayi muku ne? Na sake tambayarsu Zakai bayani da kanka dan saurayi a gaban kuliya lokacinda aka gurfanar da kai a lokacinne zakasan kowanne aiki ka aikata wanda shine abinda yasa aka turomu tun daga adamawa mu kamaka mu tafi da kai... Dan sandan yana fadar hakan naji kaina ya sara da karfi naji zuciyata ta fara wani kwakkwaran bugu wanda yake kokarin fasamin kirjina, na dubi yan sandan a tsorace sannan na dubi mahaifiyata da kanwata naga sun tsaya suna kallon abinda yake shirin faruwa a gareni... Tun kafin na gama tunanin da nake naji daya daga cikinsu ya dakumi kuguna yana shirin yin waje dani na danyi turus ina kokarin tsayawa tun kan na tsaya naji saukar wani marin wanda saida naga wuta a idanuna sannan suka hankadani sukayi waje dani sannan suka daukeni gamida watsani cikin motar sannan suma suka hau... Na tashi zaune a cikin motar cikin karfin hali na kalli kofar gidanmu a lokacin na iske mahaifiyata da kanwata liliane suna tsaye suna kallo suna kuka a lokacin sukaja motar tasu da karfi suka fice da gudu daga unguwar... Sai a lokacin naji kalaman dan sandan yana baiyana a cikin zuciyata naji maganarsa ta karshe a gareni da cewa wai yanzu haka adamawa zasu kaini zanyi bayani acan... FARKON LABARIN safiyar wata ranar litinin safiyace dake dauke da daddadan yanayi sararin samaniya tayi kyau matuka sakamakon kyawawan gajimaren dake yawo a cikinta suna tafiya, lokaci lokaci sukan rufe hasken ranar a lokacin ne garin yake dada kyau da dadi... Lokacinne na fito daga cikin gidanmu hankalina a kwance babu abinda ke damuna sai tunanin wanne labari zanyi a dandalinda nake aiki ma'ana #DANDALIN_SOYAYYA_3 amma abin yaci tura domin yau kwakwalwata a cushe take ta kasa yimin tunanin komai sai sake sake hakan yasa dole na zaro wayata na koma karkashin wata bishiya dake jikin gidan wani makocinmu na zauna sannan na fara danna wayar tawa na nufi gunda 2go dina yake na hau... Bayan ya gama nunamin duk kan frnds dina dake online da kuma wadanda suke away sai kuma alamar wani yana nema dana zama abokinsa dan haka nayi sama dan naga ko waye a lokacin ne naga macece take nemana dana zama abokin nata sunanta BILKISA... Bayan na gama karbarta sai kawai na ganta online, tun kafin na gama nutsuwa naga sakonta yazo ta fara da yimin sallama kamar yadda kowa yakeyi. Na amsa mata sallamarta sannan na jira domin naga abinda zata sake rubutowa a gareni... Aha ana Haka zanci gaba yan'uwana idan har kuna tare dani muhammadu bin jameelu

Comments

  1. ya idab aka dauko labari ba,a gamawa

    ReplyDelete
  2. Rabiu Ibrahim Chigari2 December 2015 at 15:20

    @khady,
    ai sai kunyi comment mutabbatar kenan kuna karantwa mukeci gaba

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA