LABARI MAI BAN AL'AJAB DAURE KA KARANTA,TABBAS ZAI AMFANE KA

Wani mutum ne yashirya yin wata tafiya.
Ya dauki matarsa da ’ya’yansa cikin
motarsa suka kama hanya. Ba su yi nisa ba suka hadu da wani mutum
tsaye a bakin hanya.Ya
daga musu hannu suka tsaya, ya nemi su
dauke shi.
Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya
ce, “Ni ne dukiya.” Nan take iyalin suka dau sowar cewa ga
abokin tafiya, maganin takaicin
duniya. Suka ce lallai a dauke shi su tafi tare.
Dama motar irin babbar Jif din nan ce mai
yalwar mazaunai, sai suka dauke shi suka
tafi. Suna yin gaba kadan sai suka tarar da wani
mutumin, shi ma a bakin hanya yana daga
musu hannu, sai maigida ya tsaya. Ya
tambaye shi: “Wane ne kai?”
Ya ce: “Ni ne sarauta da matsayi.” Iyalan
na jin haka suka ce a dauko shi, domin babu abin da yin sa zai gagari mutum a
duniya, muddin yana da sarauta da matsayi.
Shi ma suka dauke shi suka wuce.
Suna kara gaba kadan sai ga wani
mutumin tsaye a gefen hanya, shi ma ya daga
musu hannu suka tsaya. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?”
Ya ce: “Ni ne Addini.” Maigida ya waiwayi
iyalansa, sai ya ga sun yi
jugun-jugun cike da damuwa.
Tun kafin ya nemi shawararsu suka ce:
“Wannan ba abokin tafiya ba ne. Takura mana zai yi da
hukunce- hukuncensa na halal da haram, ya
hana mu
more rayuwarmu.
Ya dai jira nan gaba ma dawo mu dauke shi
bayan mun gama more jin dadin rayuwarmu.” Maigida ya
yarda da shawarar iyalansa, suka
wuce suka bar Addini nan tsaye, suna
masu isuwa da wadatar dukiya da alfarmar
sarauta da matsayi, har suka ci karfin tafiyar
daza su yi. Suna kan tafiya sai suka isa wani wurin
binciken ababen hawa, ( cheking Point ) suka
tsaya don suma a duba su.
Sojan da ke bincike yace da
maigida:
“Kai fito mu tafi, tafiyarka ta kare daga nan!” Maigida ya ce: “Kai kuwa wane ne
kai?” Ya ce: “Ni ne mala’ikan mutuwa.Ina
bincike ne a kan addini. Kai kuwa ba ka da
shi.”
Maigida ya ce: “Af, ai na baro shi a hanya.
Bari na koma na dauko shi.” Mala’ikan mutuwa ya ce: “Ai wannan
damar ta wuce ka har abada!”
Maigida ya kara cewa: “To ai ina tare
da dukiya da sarauta da matsayi da
dukkan iyalina.” Mala’ikan ya ce: “Ai duk
wadannan ba za su amfane ka da komai ba.
Addini kadai ake bukata a nan.”
Maigida ya waiga sai ya ga matarsa ta dare
mazaunin direba, ta ja mota sun yi
tafiyarsu ita da sauran iyali tare da dukiya da
sarauta da matsayi. Suka bar shi nan mala’ikan mutuwa ya tasa
keyarsa. Babu iyali! Babu
dukiya!! Babu sarauta da matsayi!!!

******************************

Don Allah dan uwana/yar uwata wanne darasi ka
dauka dangane da wannan labari?.
Ina fatan zaka ilmantu da wannan Labari kasan cewa Duniya bata jiran kowa....

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA