DAGA SHEIKH HAMBALI YUSUF (HAFIZAHULLAH).

SABUWAR SHEKARA TA MUSULUNCI

*ADDU'AR KARSHEN SHEKARA***

Duk wanda ya karanta wannan addu'ar a yau, duk barna da tabargazarar da shedan ya sanya shi yayi cikin wannan shekarar, ta ruguje, watau an yafe mashi, in sha Allahu.

Yau Alhamis ne 29 ga watan Zulhajji shekara ta 1435, yau ne rana ta karshe a wannan shekarar ta musulunci.

In sha Allahu gobe Juma'a ne 1 ga Muharram na Shekara ta 1436.
Ya kamata duk musulmi ya kula, ya gane wannan lissafi na shekarar musulunci shine ya
samo asali tun daga Annabi SAW, kuma dashi Annabi SAW ya bada umurnin a rika lissafi ba wancan na miladiyya watau na turawa da ake amfani dashi ba.

Akwai addu'ar da ake yi ranar karshe ta shekara,
da kuma rana ta farkon shekara. A duba MUJARRABATUL DAIRABIYL KABIYR, Ta'alifin Asshaikh Ahmad Addairabiy, za'aga cikakken bayanin.

Ga addu'o'in kamar haka:

*ADDU'AR KARSHEN SHEKARA***

Zaka ce: "Bismillahir Rahmanir Rahim. Sallallahu Ala Sayyidina Muhammadin Wa'ala Alihi Wasahbihi Wasallim. Allahumma Ma Amiltu fiy Hazihis Sanatu Mimma Nahaitaniy Anhu, Falam
Atub Minhu, Walam Tardahu, Wanasiytuhu Walam Tansahu, Wahalimta Alayya Ba'ada Qudratuka Ala Uquubatiy, Wada'autaniy Ilattaubati Ba'ada Jara'atiy Ala Ma'asiyatika, Fa'inniy Astagfiruka, Fagfirliy Bifadlika. Wama Amiltu Fiyha Mimma Tardahu, Wawa'adataniy
Alaihis Sawabu, Fa'as'aluka Allahumma Ya Kariymu Ya ZalJalali Wal'Ikrami, An Tataqabbalahu Minniy, Wala Taqada'u Raja'iy Minka Ya Kariymu. Wasallallahu Ala Sayyidina Muhammadin Wa Ala Alihi Wasahbihi Wasallim".

(FASSARA):-
"Ya Allah! Duk abinda na aikata a wannan shekarar, cikin abubuwan da ka haneni a kansu, kuma ban tuba daga garesu ba,
sannan baka yardam mani dasu ba, kuma ni na manta su amma kai baka manta su ba, kuma kayi hakuri dani bayan kana da ikon azabtar dani, ka ma kirani zuwa ga tuba bayan fadawata ga sabonka, to ina rokonka gafara, ka gafarta mani da falalarka. Kuma abubuwan da na aikata
cikinta daga wadanda ka yarda dasu, kuma kayi mani alkawarin lada, to ina rokonka ya Allah! Ya Mai Karimci! Ya Ma'abuci girma da Daukaka! Ka karbesu daga gareni, kada ka yanke gurina daga gareka ya Mai Karimci".

To da ka karanta ta, Shedan zaya ce, "duk wahalar da mukayi tare da (wannan bawa) tsawon shekara, yanzu ya bata ta cikin sa'a guda.

Don haka duk wanda Allah ya nufe shi da ganin wannan posting, to ya daure ya karanta wannan addu'ar a yau, domin amfanin kansa.
Kuma ya taimaka yayi sharing posting din don wasu su gani suma su amfana, kuma a taimaka a sanar da wadanda basu gani ba don Allah, domin
al'ummar Annabi SAW su samu gafarar zunubban da suka aikata cikin wannan shekarar.

Allahumma Salli Ala Sayyidina Muhammadin Wasallim.

Allah ka gafarta mana dukkan miyagun ayyukan da muka aikata cikin wannan shekara, ka kuma amshi dukkan ayyukan kwarai wadanda muka aikata cikin ta don albarkar Annabi SAW amin

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA