UWA-UWACE WALLAHI

Wata rana wani yaro ya tafi makaranta
to dab da
za'a tashe su sai aka fara ruwan sama,
shi kuma
yaron yana jin yunwa idan ya tsaya be
san sanda
za'a gama wannan ruwan-ba.

Ya dan tsagaita ya jira kadan yaga
ruwannan babu
alamar tsayawa, kawai sai ya kutso kai
ya taho gida
da gudu.

Yana zuwa gida ya shiga cikin daki,
nan ya tarar da
yayar-sa, da yayyen-sa maza guda 2
da baban-sa
da babar-sa a zaune a daki suna cin
abincin rana.

Kawai ya shigo cikin daki kayan
jikinsa a jike.

Babansu ne ya fara yi masa magana
da tsawa;

~--► "Wawa, me yasa baka tafi da
Lema ba?
"Umbrella"
Sannan babban yayansu;

~--► Mtsewww! Yai tsaki se kaje
mura ta kama-ka.
Sannan yayarsa;

~--► To me yasa baka tsaya an gama
ruwanba?
Sannan dayan yayan nasa;

~--► Dallacan tsaya daga bakin kofa
kar ka jika
kafet "Carpet"
Nan take se yaron ya fashe da kuka...

Babarsa ce kawai bata hantareshi ba ta
dauko
tsumma ta goggoge masa fuskarsa, ta
bashi wasu
kayan ya saka.

Kayi alfahari da mahaifiyarka.

Jama'a a dinga yiwa uwa ladabi da
biyayya.

Allah ya taimaki UWA.
Allah ya taimaki UWA.
Allah ya taimaki UWA

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA