KAFIN KA YANKEWA MUTUM HUKUNCI YA KAMATA KAYI NAZARI KAN MAGANARSA KO KAI WAYE.
Wata Rana Sayyidina Umar (rta) Ya Fito Daga Masallaci Sai Yaga Wani Mutum A Zaune Gefen Masallachi.
Sai Yai Mai Sallama Yace: Bawan Allah ko zaka iya gaya min yadda ka tashi a Rayuwarka?
Sai Wannan Bawan Allah Yace wa Sayyidina Umar Na Tashi Ina Son Fitina Kuma Ina Kin Gaskiya Kuma Ina Sallah Ba Tare Da Arwala Ba Kuma Ina Da Abinda Allah Baidashi.
Rufe Bakinsa Ke Da Wuya Sai Sayyidina Umar Ya Zaro Takobi Yace Sai Ya Kashe Shi Suna Wannan Hali Sai ga Sayyidina Aliyu Ya Biyo Wurin Sai Ya tambayi Sayyidina Umar ko meke faruwa? Sai Sayyidina Umar yaGaya Masa, Sai Sayyidina Aliyu Yayi Murmushi Yace: To Ai Koni Na Tashi Ina Son Fitina Kuma Ina Kin Gaskiya Kuma Ina Sallah Batare Da Alwala Ba Kuma Ina Da Abin Da Allah Bai Dashi.
Sai Sayyidina Umar Yace To Ina Jinka me Wannan ke nufi?
Sai Sayyidina Aliyu Yace Abinda Yake Nufi Da Ya Tashi Yana Son Fitina Shine, Umar hala ka mance Allah Yace "Lallai Dukiyoyinku da Diyan Ku Fitina Ne?" Kuma Kaga Ni Ina Son 'Ya'ya Da Dukiya Kuma Kaga Fitina Ce Saboda Haka Ina Son Fitina.
Sai Sayyidina Umar (rta) Yace To Naji Saura Na Biyun.
Sai Sayyidina Aliyu Yace Cewar Da Yayi Ina Kin Gaskiya Ka Mance Allah (swt) Yace "Magagin Mutuwa Zai Zo Da Gaskiya" To Yana Nufin Yana Kin Mutuwa.
Sai Sayyidina Umar Yace Toh Naji Ai Akwai Wasu Koda Yaci Wadannan To Ai Bazai Ci Sauran ba.
Sai Sayyidina Aliyu (rta) Yace Cewar Da Yayi Yana Sallah Batare Da Alwala Ba To Yana Nufin Yana Salati Ga Annabi Muhammad "SAW" Ba Tare Da Alwala Ba.
Sai Sayyidina Umar (rta) Yace To Ai Ko Yaci Wadannan Ba Zai Ci Na Karshe Ba.
Sai Sayyidina Aliyu (rta) Yace To Ai Duk Ma Yafi Sauki, Sai Yace Cewar Da Yayi Yana Da Abinda Allah Bai Dashi Ya Umar Halan Ka Mance Allah Baida 'ya'ya Kuma Baida Mata Kaga Kuma Shi Yana Da Mata Da Kuma Diya Kaga Kenan Yana Da Abin Da Allah Bai Dashi Koh?
Nan Take Sai Sayyidina Umar Ya Sake Shi Ya Wuce Yace Sadaqata (yayi gaskiya).
Wannan Yana nuna mana mu rika taka tsantsan kan lamurra, Idan wani Yayi wata magana da ta shige ma duhu koda akan akan Facebook ne, kaga Rubutun da baka fahimtaba, to kayi tambaya kada kai tsaye ka Yanke Hukunci ko kahau mutum da zagi.
Ya Allah ya kara yarda a garesu da su da dukkannin Sahabbai da Iyalan Gidan Manzon Allah "SAW"
Ya Allah ka kara tsira da Aminci ga Shugaban Mu Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu "SAW"
Ya Allah ka samu a ceton Annabi "SAW"

Comments
Post a Comment