MAGANIN HANA ZINA

HANYOYI 12 DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA
AIKATA ZINA.

Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine:

1. tsayuwa abisa tafarkin Allah da gaskiya.

2. Cikakken Tsoron Allah a zuciya. Tare da
kwadayin samun Rahamarsa.

3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin
Jam’I. Tare da neman ilimin sanin Sallar.

4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman
tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe.

5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa
gareka/gareki.
Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata
wannan Kaba’irar

6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar
ma MAZINATA a lahira.

7. Tuno wa shaitan da kuma kaidinsa da yake
Qullawa domin hallakar da ‘Yan Adam.

8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba
Muharramarka ba/ko Namijin da ba
Muharraminki ba.

9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko
kuma wakoki da hotunan batsa.

10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani
saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya.

12. Addu’ar neman tsari daga munanan ayyuka,
da mummunan tunani.
“Allahumma inni a’uzu bika min Munkaratil
Akhlaaqi wal Af’aali wal Ahwa’I.”

11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da
ita:

‘Yar wani ce.
Qanwar wani ce.
Diyar wani ce.

Watarana kuma zata zama Uwar wani.

To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da
Uwarka, ko Qanwarka, ko Diyarka, ko ‘yar da ka
haifa.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA