HUKUNCIN GAISAWA DA MATAR DA BA MUHARRAMA GAREKA BA.
alamu alaikum malam barka da himmah Allahu (S W A) ya kara ma hazakah. Dan Allah malam muna neman sani game da sallama wato ( السلام عليكم ) tsakanin mata da maza musamman ma matan aure ko ya halitta namiji yayi wa macce ta aure sallama wacce take ba muharraminshi ba? ko kuma mace ta aure tayiwa wani namiji sallma wanda yake ba muharaminta ba, Malam dan Allah kayi hakuri in da hali ka amsa muna wannan tambayar
AMSA
****
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Hakika Malam Muhammad kayi tambaya mai muhimmanci. Kuma insha Allahu zamu amsa maka gwargwadon abinda Allah ya sanar damu.
Da farko zamu fara tambayar kanmu:
MENENE MATSAYIN ITA KANTA SALLAMAR?
Ita dai sallama atsakanin Musulmai, Abu ne mai mutukar muhimmanci wanda Allah da Manzonsa yayi umurni da ita.
Allah (swt) yana cewa:
"IDAN AKA GAISHEKU DA WATA GAISUWA, TO KUMA KU (AMSA) GAiSUWAR DA WACCE TAFI KYAWU DAGA GARETA, KO KUMA KU MAYAR DA ITA".
(Suratun Nisa'I ayah ta 86).
Sayyiduna Abu Huraira (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"Ba zaku shiga Aljannah ba har sai kunyi (Hakikanin) Imani. Kuma ba zakuyi (Hakikar) Imani ba, har sai kun Qaunaci Junanku.
Shin In baku labarin wani abu wanda idan kuka aikatashi zaku so Junanku?
SHINE KU WATSA SALLAMA ATSAKANINKU".
(Aduba Sahihu Muslim Hadisi na 54).
Idan muka duba zamu ga cewar wannan Umurni ya shafi dukkan Muminai Maza da mata gaba daya.
Ma'ana: Namiji zai iya gaisar da Maza, ko kuma Matarsa ko Matan da suke Muharramansa. Hakanan itama Mace zata iya gaisar da Mijinta, ko kuma duk wani Namiji wanda ya zamto Muharraminta. (Wato wanda shari'a ta hana ya aureta).
Daga cikin wadannan da muka lissafta, Duk wanda akayi masa sallama, to wajibi ne gareshi ya maida sallamar.
Amma dangane da gaisuwa ko mayar da gaisuwa tsakanin mutanen da ba Muharraman Junansu ba, to akwai hukunce hukunce na musamman wadanda suka shafi wannan.
1. MALIKIYYAH : An tambayi Imamu Malik (rah) dangane da yin sallama ga Mata, ko kuma mayar da sallama garesu idan sunyi, sai yace: IDAN TSOHUWAR MACE CE, TO YIN HAKA BA MAKROUHI BANE. AMMA IDAN YARINYA CE (Wacce akwai sha'awa tare da ita) TO GASKIYA NI INA QIN HAKA (wato Makruhi ne awajensa).
Acikin Sharhin da yayi ma littafin MUWATTA' MALIK, Imam Zarqnni ya warware wannan Maganar ta Imamu Malik. Yace ya fadi karhancin ne saboda tsoron fitinar da zata iya afkuwa yayin da Shi Namijin yaji muryar macen yayin da zata mayar masa da sallama.
Acikin AADABUSH-SHAR'IYYAH juzu'I na 1 shafi na 370, Ibnul MuFlihi yace:
"Ibnul Mansour ya tambayi Imamu Ahmad bn Hanbal (rah) dangane da halarcin Amsa sallama ko yinta ga Mace, Sai Imamu Ahmad yace "Eh babu laifi idan Matar tsohuwa ce.
Hakanan Salih bn Ahmad bn Hanbal ('Dan gidan Imamu Ahmad din ne) yace: Na tambayi babana Shin ya halatta Namiji yayi ma Mace sallama, wacce ba muharramarsa ba?"
Sai yace "Eh idan matar tsohuwa ce, ya halatta. Amma idan ba tsohuwa bace, to bai halatta ayi mata sallama ba. Domin yin hakan zai janyo ta bude bakinta ta mayar da sallamar, kuma za'a iya fitinuwa da muryarta.
Daga bangaren Shafi'iyyah, Imam Nawawy ma ya kawo irin wannan bayanin cewa bai halatta ayi ma mace yarinya sallama ba. (Sai dai in babu wata fitinar da ake tunanin zata afku ta dalilkin hakan).
Aduba AL AZKAR shafi na 407.
Amma idan Matan suna da yawa, kuma ba'a Tsoron Fitina daga kowaccensu, to mutum zai iya yi musu sallama. Aboda hadisin da Imam Abu Dawud ya ruwaito daga Sayyidah Asma'u bnt Yazeed (ra).
Tace Manzon Allah (saww) yakan Wuce ta kusa da taronsu (Na mata) kuma yakan yi musu sallama.
(Sunanu Abi Dawud hadisi na 5204).
A takaice dai Makruhi ne yin sallama ga matan da ba Muharramanka ba. Sai dai in tsohuwa ce, ko kuma baka tsoron afkuwar wani abu azuciyarka, ko Zuciyarta ta dalilin hakan.
Hakanan ko tayi maka sallama ba zaka amsa ba, indai kana tsoron afkuwar fitina.
Wallahu a'alam.

Comments
Post a Comment