Jihar Jigawa Zata Goyi Bayan Shugaba Jonathan A 2015- Walin Dutse

A firar da yayi da wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari, Alhaji Bashir Dalhatu, Walin Dutse yace ya gana da shugaba Jonathan kuma zasu goyi bayansa domin ya nunawa jihar da mutanenta kauna.

Alhaji Bashir Dalhatu yace ya fadawa shugaban kasa cewa ya ziyarci jihar kaman sau hudu ke nan tunda ya kama mulki abun da ya nuna cewa yana kaunar jihar.

Duk lokancin da ya zo jihar yana yi masu alkawura kuma yana cikasu. Ya yiwa jihar ayyuka. Misali ya gina makarantu da jami'a da tituna da bunkasa ayyukan harkokin noma da kuma sabon filin saukar jiragen sama da ma wasu abubuwa da dama dake kara inganta jihar.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA