LABARIN WANI MUTUM DA MUTUWA TA RISKESHI

Wani daga cikin magabata, wanda ma shiba
musulmi bane.

Dayazo mutuwa yasa aka kira masa manyan
sojojinsa sai yace musu, yanason su cikamar
wasu wasiyoyi gudu uku, idan mai yanke kauna ta
daukeshi.

Wasiyoyin kuwa sune kamar haka:

1. Likitocin da sukafi kowa kwareya a fadin
kasarsa, su yakeso sudauki akwatin gawarsa
sufito da'ita bainar jama'a kafin aje a binneshi.

2. Dukkan abin daya mallaka na kudi dana zinari
ko azurfa, yanason a tattarasu a watsasu a hanyar
daza'a bi da gawarsa zuwa makabarta.

3. Hannayensa kuma yace yanason a barsu a
wajen akwatin suna Lilo inda kowa dake wajen
zai iya gani.

Wani daga cikin sojojin nasa sai yayi mamakin
wannan abun saiya tambayeshi karin bayani shi
kuma sai yace:

1. Inason likitoci su dauki gawatane domin na
nunawa mutane cewa yayinda mutuwa tazo ko da
likitocin da sukafi kowa kwarewane, baza su iya
warkadda mutum ba.

2. Inason a watsa dukiyata akan hanyane domin
mutane susan cewa duk abinda aka samu a
duniya, a duniya ake barinsa.

3. Inason abar hannayena suna rito ta wajene
domin mutane su gane cewa munzo duniya
hannu empty haka kuma zamu koma hannunmu
empty babu komai, bayan dukkan abinda muka
mallaka na dukiya da sauran kayayyakin duniya
bayan mungama cinye dukkan kwanakinmu a
duniya, kuma wannan shine lokaci.
Lokaci shine makiyinmu ba mutuwaba.

To masu karatu kunjifa kafiri ma kenan yanayi
tunani irin wannan, balantana mu Musulmai,
masuyin Sallah.

Ya Allah Kasa muyi amfani da lokutanmu wajen
neman lahira bana duniya kadaiba.

Allah ka jiqanmu ka gafarta mana.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA