Posts

Showing posts from November, 2015

Glo Twin Bash Gives You N1200 Worth of Airtime+Data For Recharging N200 Data

Glo Twin Bash Gives You N1200 Worth of Airtime+Data For Recharging N200 Data Glorecently launch this services and it is called TwinBash. According to them, any subscriber who do any of the below will be rewarded with the benefits attached below. Benefits of Twin Bash ==>Any subscriber who recharges N200 data will get 200 MB of data worth N800, another N200 airtime to call or send sms to any network and N200 airtime to call 10 friends and family. The subscriber will therefore get N1,200 value for a data recharge of N200 and the recharge is valid for four days. ==>If you recharges withN500 data plan, you’ll get500 MB of data,N500airtime to call or send sms to any network and N500 airtime to call 10 friends and family, adding that this is valid for 10 days. ==>Every subscriber who recharges withN1,000for data will get1GB of data.The subscriber will also receive N1,000 free airtime to call or send sms to any network andN1000free airtime to call 10 friends and family, adding that t...

YININKA BAKON KA NE DON HAKA KA KYAUTATA MASA

YININKA BAKON KA NE DON HAKA KA KYAUTATA MASA ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺒﺼﺮﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﻳﺎﺑﻦ ﺁﺩﻡ، ﺇﻧﻤﺎ ﺃﻧﺖ ﺃﻳﺎﻡ، ﺇﺫﺍ ﺫﻫﺐ ﻳﻮﻡ ﺫﻫﺐ ﺑﻌﻀﻚ . HASANUL BASARI ya na cewa:Ya kai dan Adam! Lallai kai kamar ranaku ne, idan yini daya ya gushe wani sashen ka ya wuce. Ma'ana idan ko wane yinin mutum ya wuce ya na 'kara kusantar kabari kenan. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ : ﻳﺎﺑﻦ ﺁﺩﻡ، ﻧﻬﺎﺭﻙ ﺿﻴﻔﻚ ﻓﺄﺣﺴﻦ ﺇﻟﻴﻪ؛ ﻓﺈﻧﻚ ﺇﻥ ﺃﺣﺴﻨﺖ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﺭﺗﺤﻞ ﺑﺤﻤﺪﻙ، ﻭﺇﻥ ﺃﺳﺄﺕ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﺭﺗﺤﻞ ﺑﺬﻣﻚ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻟﻴﻠﺘﻚ . Ya 'kara ce wa:Ya kai dan Adam! yininka bakon ka ne saboda haka ka kyautata masa. idan ka kyautata masa zai tafi yana mai gode maka, idan kuma ka muzanta masa zai tafi yana sukan ka. Haka zalika daren ka. ﻭﻗﺎﻝ : ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ : ﺃﻣﺎ ﺍﻷﻣﺲ ﻓﻘﺪ ﺫﻫﺐ ﺑﻤﺎ ﻓﻴﻪ، ﻭﺃﻣﺎ ﻏﺪﺍ ﻓﻠﻌﻠﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻛﻪ، ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻠﻚ ﻓﺎﻋﻤﻞ ﻓﻴﻪ . Kuma ya ce: Duniya dai abu uke ne kawai, ma'ana kwanaki uke ce kawai. Idan ka ga jiya toh ya tafi da abinda ke cikinsa, amma gobe; wata 'kila ba za ka riskesa ba, amma yau da ka ke cikin sa, na ka ne don haka ka yi aiki acikinsa. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ...

LABARIN WANI DAN FULANI DA FENTI

LABARIN DANFULANI. Wani bafullatani ne ya ga wani gida an yi masa farin fenti yana ta sheki, sai ya zauna ya fashe da kuka, akayi akayi yayi shiru yaki. Da kyar aka samu ya daina kukan.... .Sai aka tambaye shi, wai bawan Allah mai ya saka kukan ne? sai ya ce shi wallah I wulaqancin mutanen birni ne ya ishe shi. Yanzun su rasa da abinda zasu yi fenti sai da KINDIRMO!!!!!(NONO)

I MISS YOU CODE

I MISS YOU CODE FOR FACEBOOK [[240717402719790]] [[492341467525278]]

KADAN DAGA TARIHIN UMAR MUKHTAR

Image
A Lokacin Da Turawan Mulkin Mallaka Na Kasar Italiya Za Su Kashe Mujaddadi Kuma Mujahidi Sheikh Omar Mukhtar(R) Akan 'Kin Sallama Musu Da Yayi, Akan Mamayar Da Suka Yiwa Kasarsa Libya. Sun Ba Shi Umarni Da Yayi Kalamai Na 'Karshe a Rayuwarsa(Kafin Su Rataye Shi), Sun Zaci Zai Roqe Su Da Su Yi Masa Rai(Kar Su Kashe Shi), Cikin Mamaki Sai Ya Fuskance Su Suka Ji Ya Ce: "Daga ALLAH Mu Ke, Kuma Gare Sa Za Mu Koma". Sheikh Omar Mukhtar(R) Tsayayyen 'Dan Gwagwarmaya Ne Da Yayi Yaqi Tuquru Da Mamayar Zalunci Da Turawan Italiya Suka Yiwa Kasarsa Libya, Daga 'Karshe Turawan Na Italiya Sun Rataye Sheikh Omar Mukhtar a Bainar Jama'a(Magoya Bayansa) Wanda Yayi Sanadiyar Shahadarsa a Shekarar 1931. YA SALAAM! ALLAH YA BA MU ALBARKAR MASU ALBARKA AMEEEEEN.

BAMBANACIN MATAN DA DANA YANZU

BAMBAMCI TSAKANIN MATAN DA, DANA YANZU MATAR DA:- Larai debo min takalma na to mai gidana gashi ta durkusa. MATAR YANZU:- My horney kawomin takalmana kash derling dan tsaya ingama kallon wannan sindin Jira. MATAR DA:- Barka da zuwa mai gida, ya aiki/ kasuwa, abincin ka an gama, muje kai wanka nasan ka gaji, sannu da zuwa. MATAN YANZU :- Pls daga zuwan ka zaka dameni na kawo maka ruwa, kaje frigde ka dauka ga shinkafa nan ka dumama, matarka ce ni ba yar aiki ba MATAR DA:- Mai gida ka daina damuwa da wannan TALAUCIN, ALLAH zai fitar damu kaji baban gadaz, kada ka damu, gashi muna ci, muna sha kada ka damu MATAR YANZU:- Kaga malam na gaji da wannan baqin talaucin. kaike nan kullum complain baka da kudi kawai ka sauwaqe mun na tafi gida Abokanan ka sunyi gida a GRA mu muna nan SHEKA da zama. MATAR DA:- Mai gida ya yan mu uku fa kacal, baka ganin mu qara haihuwa tunda kaga ya ya RAHMA ne daga ALLAH?? MATAR YANZU:- Kaga baban abba, ni na gaji da ya yan nan, ya ya biyu sun ishe ni, bazai yiyu...

YADDA MARIGAYI ABUBAKAR AUDU YA RASU:

YADDA MARIGAYI ABUBAKAR AUDU YA RASU: Marigayi Prince Abubakar Audu, dan takarar gwamnan jihar Kogi karkashin tutar jamiyyar APC a zaben da aka gudanar jiya Asabat. Allah ya karbi rayuwarsa ne a wannan rana. Bayanai daga Iyalan marigayin na nuna cewa: Marigayin ya fara Aman Jini ne a ranar Juma‘a da Daddare. Wadda suka bayyana hakan da Alaka da hawan jini. “Marigayi Abubakar Audu ya tashi wayewar garin jiya Asabat ne cikin rashin jin dadi. Amma Likitansa ya bashi wasu maganunuwa, wadda hakan har ta sanya masa zuwa wajen kada kuri‘arsa na zaben gwamnan jihar a mahaifarsa dake Ogbonicha. Bayan dawowarsa gida a jiya Asabat din, ya cigaba da yin Aman, inda lamarin yayi kamari gabannin wayewar garin wannan rana ta Lahadi. Bayanai dai sunce Marigayi Prince Abubakar Audu, ya rasune tunda misalin karfe 5am na safiyar wannan rana, kafin hukumar zabe ta fara tattara sakamakon zaben da aka gudanar jiya Asabat. Marigayi Abubakar Audu ya mulki jihar Kogi tsakanin Shekarar 1999 zuwa 2003. Hukumar Za...

ALLAH MAI IKO

LABARI MAI BAN MAMAKI MAI BAN AL'AJABI Anyi Wanj Makeri Wanda Duk Yadda Karfe Yayi Zafi, Yayi Jawur Cikin Wuta Amma Shi Hannu Yake Sawa Ya Dauko Karfen. Hakan Yasa Aka Tambayi Makerin Miyasa Bayajin Zafin Wuta??? Sai Makerin Yace "Akwai Wata Kyakkyawar Mata, Wadda Mijinta Ya Rasu Ya Barta Da Marayu. Wata Rana Sai Matarnan Tazo GurinSa Tace Masa, Ya Taimaka Mata Da Abinda Zasuci Ita Da 'ya 'yanta. Sai Makerin Yace Sai Idan Zata Yarda Yayi Fasiqanci Da Ita. Matar Taqi Yarda Sai Yace Bazai Bata Kome Ba. Matar Ta Tafi Tasha Yawo Bata Samu Abinda Zataci Ba. Sai Takoma Gurin Makeri Tace Ta Yarda Yayi Duk Abinda YakeSo Da Ita, Idan Zai Bata Abincin. Makeri Yakaita Gida, Ya Shiga Daki Da Ita. Babu Mai GaninSu, Yana Neman Ya Fada Mata Saitace Kaji Tsoron Allah Kadda Ka Aikata Wannan Mugun Aiki Dani. Hakan Yasa Imani Ya Ratsa ZuciyarSa, Ya Fasa Zinar Da Ita, YA KUMA BATA ISASHSHEN ABINCIN DAZATACI ITA DA 'YA 'YANTA. Sai Matar Tayi Masa Addu'a Tace "Allah Ya Raba...

YADDA AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A KAN IDO NA

Image
YADDA AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A KAN IDO NA, Inji Direban Sardauna Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne ya zan ta da Wakili Jaridar Leadership yadda aka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa akan idonsa. Ya shaidawa Jaridar cewar zan iya mantawa da komai, amma banda yadda sojoji suka kashe Sardaun da iyalin sa a gaban ido na a 15 ga watan Janairun 1966. Yasir Ramadan Gwale Ne Ya Fassara Daga Jaridar Leadership Ta Yau Leadership: Kana gidan Firimiya a ranar 15 ga watan Janairun 1966. Me zaka iya tunawa da ya faru a wannan ranar? Sarkin-Mota: Ga wadan da suke zaune a Kaduna zasu shaida yadda sojoji suke yin atisaye a makarantar Kafital dake unguwar Malali a garin Kaduna, duk lokacin da za ayi wani biki a hukumance. Amma a lokacin da ake shirin yiwa Sir Abubakar Tafawa Balewa Prime minister da Firimiya juyin mulki a 15 ga Janairun 1966 mun ga sojoji suna yin atisaye ba tare da wani biki ya gabata ba na hukuma. A ranar Juma'a 14 ga watan Janairun 19...

MTN BONANZA

Samu kyautar dubu Hamsin (50,000) a layinka Gami da kyautar message dubu da Dari biyar(1500) Hadi da kyautar 3gb duka kyauta a layinka Na MTN Nigeria. kawai yi comment da email dinka zantura maka hanyar da zaka bi ka samu wannan garabasa Babu wata wahala.

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI A KODA YAUSHE

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI A KODA YAUSHE: 1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' shaaidan zai bar gidan! 2- Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu dan Adam yana son labari. 3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna 6acin ranka. 4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya. 5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta. Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka dauka a matsayin abinda ya shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka. 6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada. 7- Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu) 8- Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka. 9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku. 10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi ma...

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH. 1. Abubakar Sadeeq (RA) 2. Umar Ibn Khattab (RA) 3. Usman Ibn Affan (RA) 4. Aliyu Ibn Abi Talib (RA) 5. Talha (RA) 6. Az-Zubair (RA) 7. Abdurrahman Ibn Awf (RA) 8. Sa’d (RA) 9. Sa’eed (RA) 10. Abu Ubaida (RA). Ya ALLAH don isar Annabi (S.A.W) ALLAH kasadamu da rabonka nashiga aljannah.

WASU TAMBAYOYI

TAMBAYA: shin mece ce nasabar Manzon Allah (S.A.W)?? AMSA: Manzon Allah shine muhammadu, dan Abdullahi, dan Abdulmudallabi, dan hashim, dan abdul-Munaf, dan kusayyi, dan kilabi, Nasabarsa (S.A.W) tana saduwa, ga Annabi Isma'il dan Annabi Ibrahim Alaihimus-salam. TAMBAYA: Mece nasabar mahaifiyar Sa (S.A.W)?? AMSA: Mahaifiyarsa (S.A.W) ita ce Nana Aminatu 'yar Wahabi, dan Abdul-Munafi, dan Zuhurata, dan kilabi. TAMBAYA: Ta ina nasabar mahaifinsa take haduwa (S.A.W)?? AMSA: Nasabar mahaifinsa (S.A.W) tana haduwa ta wajen kakanSa na biyar (5), wato Kilabi. TAMBAYA: Yaushe mahaifinsa yayi wafati?? AMSA: Mahaifinsa (S.A.W) yayi wafati yana cikin mahaifiyarsa wato kafin a haifeshi cikinsa yana watanni biyu (2) (S.A.W). TAMBAYA: Yaushe mahaifiyarsa tayi wafati?? AMSA: Mahaifiyarsa tayi wafati yana da shekaru shida (6) an binneta a Abawa'i. TAMBAYA: Wacce rana aka haifi Manzon Allah (S.A.W)?? AMSA: An haifi Annabi (S.A.W) Ranar Liitinin. TAMBAYA: Wecce ranar yayi wafati, kuma a wacc...

KANAWA SUN FARA SAI DA BABU

Wani dan fulani ne yaje kano yaga yara suna ta sayen sweetcamfo (alewar larabawa) sai abin ya bashi sha'awa sai ya bada kudinsa a bashi,koda aka bashi ya saka ta (alewar) a bakinsa kun san yadda take sai ta narke ya neme ta ya rasa ! Sai yaji zaki ,budar bakinsa sai yace '' SHEGU KANAWA SUN FARA SAIDA BABU'

BOM YA TASHI A KASUWAR WAYOYI TA JIHAR KANO

Image
Yadda Mata 'Yan Kunar Bakin Wake Guda Biyu Suka Tada Bam Din Da Ya Tashi A Kasuwar Wayoyi A Jihar Kano. Bamabamai biyun da suka ta shi a kasuwar wayoyi ta Farm Centre da ke birnin jihar Kano a yau, bincike ya nuna cewa wasu mata 'yan kunar bakin wake ne guda biyu suka yi sanadiyar tashinsu. Wani da lamarin ya auku a gabansa ya fadi cewa bam na farko ya tashi ne a tsakiyar kasuwa, yayin da kuma na biyun ya tashi a bakin kofar shigar kasuwar. Shi ma wani ganau ba jiyau ba, ya fadawa majiyarmu cewa yana daga cikin wadanda suka hana yarinyar shiga cikin kasuwar, wanda hakan ya sa ta tashi bam din a bakin kofar kasuwar. An yi ta ganin 'yan kasuwa na ta diban gawarwaki da wadanda suka samu rauni zuwa a asibiti a motocin jama'ar da suka bayar da gudummawa. Kwamishin 'yan sandan jihar Kano, Muhammadu Katsina ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya fadawa manema labarai cewa wasu mata 'ya kunar bakin wake ne guda biyu suka yi sanadiyar tashin bamabamai biyun a kasuwar. Sannan...

LABARIN WANI MAI ARZIKI

LABARIN WANI MAI ARZIKI Watarana Annabi Musa (as) yana zaune sai wani yaro yazo ya sameshi yace "Ya Annabin Allah, ina so ka roka min Ubangijinka ya bani arziki da dukiya". Sai Annabi Musa (as) yace masa "Zaka rayu shekara Sittin ne aduniya. Shin Kafi son Ubangiji ya baka arzikin nan acikin shekaru 30 na farkon rayuwarka ne, Ko kuwa a shekaru 30 na Qarshen rayuwarka?" Sai yaron nan yaje ya rika tunani yana hangen Qarshen rayuwarsa, kuma yana kallon farkonta. Daga karshe dai sai ya dawo yace ma Annabi Musa (as) "Na Zabi abani arzikin nan acikin shekaru Talatin da Farkon rayuwata". Wannan saurayin ya manta da cewa idan ya tsufa zai hadu da jinya da raunin Jiki irin na tsufa.. Shikenan Annabi Musa (AS) ya roka masa Allah akan wannan bukatar. Kuma Allah ya amsa masa. Nan da nan sai gashi ya fara tara arziki da dukiya Har ya girma ya zama Hamshakin mai kudi. Amma fa duk da haka ya kasance yana bu'de ma sauran mutane hanyoyin arziki, Yana taimakon Mutane yan...

DARENKA NA FARKO ACIKIN QABARINK

DARENKA NA FARKO ACIKIN QABARINK 'Dan uwa, duk abinda zaka karanta din nan babu tatsuniya ko kokwanto acikinsa. An tattaro bayanin ne daga Sahihan Hadisai na Manzon Allah (saww) wadanda Manyan Malamai suna tattaro acikin litattafansu. Darenka na farko acikin Qabarinka shine dare mafi razani da firgitarwa daga cikin dukkan darare.. Hakika tun lokacin da suka zo suka binneka, Idan sun ajiyeka agefen Qabarinka, Shi kansa Qabarin zai yi magana dakai. Zai tambayeka shin Mai kake gani acikinsa?? Zaka ce masa ai babu komai. Shi kuma zai ce maka, to duk abinda ka gani na alkhairi ko Sharri, to kaine kazo da abinka!!! Idan kai mutumin banza ne mai bin son zuciyarsa, mai biyewa Sha'awarsa, To shaitan ya riga yasan ya gama dakai. Don haka zai zo gefen Qabarinka yana yi maka dariyar Mugunta.. Idan kuwa ka zamanto mutumin Kirki mai tsoron Allah, mai Halayen Kirki, To tun daga mutuwarka shaitan zai rika tsula kuka da eehu wai saboda bai samu damar dulmiyar dakai cikin hallaka ba. Idan sun ga...

Facebook Arrow Code

Sanya wannan kod din cikin comment box naka don ganin hoton kibiyoyi Iri Iri. [[186743958201911]] [[186744031535237]] [[186744098201897]][[186744281535212]] [[186744371535203]] [[186744464868527]][[186744541535186]] [[186744604868513]] [[186744668201840]] [[186744711535169]]

MAI AYA TA MUTU

Image
Allah ya yi wa fitacciyar 'yar wasan kwaikwayon Hausa, Hajiya Hafsatu Sharada wacce aka fi sani da Mai Aya, rasuwa....

GIRMAN KAI KASHI NA ASHIRIN DA DAYA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? Ci gaba... 8 - Mai yin girman kai don kyawun halitta: Mai irin wannan hali ya sani cewa; duk kyawun halittar da mutum yake da shi Allah zai iya kawar da shi a duk sanda ya so; ko dai sakamakon tsufa, ko wani dalili na daban. Sau nawa mai taqama da kyawun halitta zai yi hatsari ko gobara ta rutsa da shi, sai ya wayi gari nakasasshe? Ko tauyayye? Wani kunnen sa ya cire ko ya qone? Wani hancinsa ya cire ko ya qone? Wani fatarsa ta salube ko ta tauye? Qaramin misali da ya ishi mai girman kai izina shi ne yadda cikin mutum yake qunshe da qazanta, hancinsa majina, kullun sai ya shiga bayan gida aqalla sau daya ko sau biyu. Irin wannan shi ne har kyawun siffarsa zai sanya shi ya yi fito na fito da Allah? Yana yiwa bayinsa dagawa? Sau nawa za ka sami mace da ake misali da ita a wajen...

ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI : Duniya ta riga ta aureka dan uwa;

ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI : Duniya ta riga ta aureka dan uwa; 1. Idan ya zamto baka jiran sallah saidai sallah ta jiraka. 2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur’anin ka ba (wai bakada lokaci). 3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka sabawa ubangijinka. 4. Idan ya zamto kullum tunaninka yadda zakayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi. 5. Idan ya zamto baka karbar nasiha. 6. Idan ya zamto babu rayuwar da take birgeka sai rayuwar mawaka da ‘yan kwallo da makada. 7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa’azi ko karatun al-qur’ani. 8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheri sai watarana. 9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin addininka sai dai na neman duniya (boko). 10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon bai Qareka da komai ba. Allah (swt) Ya yafe mana zunuban mu manya da qanana. Amin

FARASHIN MAN FETUR A NIGERIA

FARASHIN MAN FETUR A NIGERIA Shin yaya farashin man fetur yake a gidan mai da kuma wurin yan cuwa cuwa (YAN BUNBURUTU) a jahohin Ku kanan hokumomin Ku da kuma kauyi kanku. Kwanakin baya a munyi wannan bincike a tenuwar (tenure ) Goodlock administration inda muka gano cewa legas da kadun da kuma Kano su suka fi kowace jaha tsadar man fetur. Shin yaya farshin man fetur din ya kasance a wannan tenuwa da muke ganin tafi kowace saukin komai.

BALARABAN KAUYE DA DAMO

LABARIN WANI BALARABEN KAUYE Wani Balaraben Qauye ya farauto Damo (alligator) ya shigo gari sai yaga Manzon Allah (s.a.w) tare da wasu Jama'a yana yi musu wa'azi. Da yaga haka sai ya tambayi mutane "Wannan mutumin fa? wanene?". Sai akace masa "AI ANNABI NE". Saboda haka sai Balaraben Qauyen nan ya rika keta tsakanin jama'a, har sai da yazo ya tsaya agaban Manzon Allah (s.a.w). Sannan yace: "Na rantse da lata da uzza (sunayen gumakansa ne) babu mutumin da na tsaneshi fiye da kai, Ba don kar mutanena su washeni ba, da sai na kasheka". Sayyiduna Umar bn Khattab (r.a) zai zare takobi ya kasheshi sai Manzon Allah (s.a.w) ya hanashi. Balaraben Qauyen nan ya fito da damonsa (yankakke) daga cikin jakarsa, ya jefar agaban Manzon Allah (s.a.w) sannan yace:. "Na rantse da lata da uzza ba zan bada gaskiya gareka ba, har sai wannan yankakken damon yayi Imani dakai". Sai Manzon Allah (s.a.w) yace "YA KAI DAMO!!". Sai Damon ya amsa acikin ...

LOKACIN SANYI

HUKUNCE HUKUNCEN LOKACIN SANYI !!! Magabata na Kwarai sun kasance suna Murna da shigowar lokacin sanyi, Saboda Dare yana tsawaita, Yini kuma yana gajarcewa, Hakan yana basu isheshen lokacin Sallar Dare da kuma Azumtar Yini. Manzon Allah(SAW) yace: “Azumi cikin Sanyi, Ganima ce Sassanya” Ahmad Albani ya inganta. Abdullahi Bn Mas’ud yana cewa : “Maraba da shigowar Hunturu, Albarka za ta sauka, Dare zai tsawaita, Yini zai gajarce don Azumi” Cikin Abubuwan da ake so ko ya halatta lokacin sanyi: 1. Gaggauta yin Sallah. Manzon Allah (SAW) idan Lokacin Sanyi ya shigo yana Gaggauta Sallah. Adabul Mufrad. 2. Kashe wuta Musamman in za a kwanta don lokaci ne na Gobara. Manzon Allah yace: ” Wannan Wutar Abokiyar gabarku ce, in zaku kwanta ku Kashe ta” 3. In sanyi ya tsananta za a iya hada Salloli, Hakama Jam’i zai iya faduwa akan Masallaci. “Manzon Allah (SAW)ya kasance yana sawa a yi kiran Sallah a cikin daren da ake tsananin Sanyi da kowa yayi Sallah agidansa” Ibn Maja. 4. Halaccin shafa a kan H...

YADDA AKE GYARA KEYPAT NA WAYA

YADDA AKE GYARA KEYPAT NA WAYA IDAN YA DAINAYI Nasan kasan kome ake nufi da keyfat wato shi keypat sune madannun waya wato wadda ake amfani dasu wajen danne danne kamar sa number wato su keypat sune jigon waya sabo da idan bbusu babu waya sabo da haka da zarar ya lalace to ga yadda zaka gyarashi: da farko ka since wayarka sannan kaje gin keypat din daya lalace saika samu feti kadansa agun sannan ka dannemo reza saika dan kankare shikkenan saika rufe wayarka sannan kasa b3 ka kunna wayar saika dannan madannun daka gyara zakaga ta gyaru shikkenan ka gama.

GIRMAN KAI KASHI NA ASHIRIN

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? Ci gaba... 6 - Masu yin girman kai don yawan mabiya: Haqiqa ma su girman kai don yawan mabiya ko magoya baya a cikin wani alamari su sani cewa ba su ne suke da mallakar zuciyar magoya bayan nasu ba, don haka Allah zai iya juya zukatansu su yi mu su tawaye a ko da yaushe, domin shi ne yake juya su yadda ya ga dama. Dalili kuwa shi ne hadisin da ya tabbata daga Abu Hurairah (ra), ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa idan Allah Madaukakin Sarki ya so bawansa, sai ya kira Mala’ika Jibrilu ya ce: Haqiqa ni ina son wane, kai ma ka so shi. Sai Mala’ika Jibrilu ya so shi, sannan sai ya yi shela a cikin sama ya ce: Haqiqa Allah yana son wane, ku ma ku so shi. Sai Malaikun da ke sama su so shi, sannan sai a sanya ma sa karbuwa a ban qasa. Idan kuma Allah ya qi bawansa, sai ya kira ...

GATA NAN GATA NAN KU

Image
GA TA NAN, GA TA NANKU: TAZO MUJITA: Akwai wani mutum da ke zaune a wani gari mai suna Raqumawa tare da matarsa da 'ya'yansu su goma sha daya. Rannan sai matarsa ta haifi da namiji, ya zama na goma sha biyu. Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana, ya ce wa uwarsa: "Kada ma a yi wahalar rada mini suna, domin sunana dan-kutun-gayya." Ya qara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinqa hawa. Iyayen suka yi haka, jama'ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen dan-kutun-gayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da 'ya'yanta su goma sha biyu. Sai dan-kutun-gayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isar su gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfida, suka zauna; ta kawo musu abinci mai dadi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan, ba su san cewa matar nan...

KYAKYAWAN KARSHE KASHI NA DAYA

Dukkan yabo da godiya da kirari da jinjina sun tabbata ga Allah Ta'ala, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga ManzonSa, Alayensa da Sahabbansa da mutanen gidansa da wanda suka biyo bayansu da kyautatawa. Bayan haka, 'Yan uwa ko shakka babu, yana daga cikin Rahamar Allah Ta'ala Ya kasance bawa ya dace da kyakkyawar karshe a rayuwarsa. Da haka ne ya sanya na ga dacewar in janyo hankalin kaina da sauran' yan uwana Musulmi domin fatan dacewa da wannan tagomashi. MENE NE KYAKKYAWAN KARSHE?: Kyakkyawan karshe, shi ne ya kasance Allah Ta'ala Ya datar da Bawa kafin mutuwar shi ya zamto ya nisanci dukkan wani abu da yake fusata Allah, da tuba daga zunubai da sabo, sannan ya zamto Bawa ya fuskanci ayyukan da'a da ayyuka na alheri, sannan ya zamto Allah Ta'ala Ya karbi rayuwar Mutum a haka. Daga cikin abin da yake nuni akan abin da muka ambata, shi ne hadisin da ya inganta daga Anas Bn Malik, Allah Ta'ala Ya kara yarda a ga...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TARA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? Ci gaba... 3 - Mai girman kai don ya na da ilimi: Duk wanda yake girman kai don ilimin da Allah ya bashi, kuma yake son Allah ya raba shi da wannan girman kan, sai ya kalli abubuwa kamar haka: Abu na farko sai ya kalli cewa abin da bai sani ba ya fi abin da ya sani yawa, kuma akwai daruruwan mutane da su ka fishi ilimi nesa ba kusa ba. Kuma ya kalli misalin Annabi Musa (as), a lokacin da aka tambaye shi wane ne mafi ilimi a ban qasa? Sai ya ce: “ni ne." kuma Ya fadi haka ne saboda ya na da yaqini cewashi Annabi ne Mursali, a lokacinsa babu wanda ya ke da sani kamrsa. Amma duk da haka sai da Allah Madaukakin Sarki ya jarrabe shi, ya umarce shi da ya je mahadar koguna biyu inda a nan ne ya hadu da Khadir. Haqiqa yadda qissarsu ta kasance, akwai izina ga duk mai hankali da ...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA TAKWAS

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? Ci gaba... C. Hanyoyin magance girman kai da ji-ji-da-kai da taqama: 1- Mai yin girman kai domin asalinsa. Wannan zai tsaya ne ya kalli nasabarsa ta haqiqa, wato asalin sa digon maniyyi ne. Duk kuwa wanda asalin sa maniyyi ne to girman kai bai dace da shi ba, domin asalin nasa ba komai ba ne face qazanta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Shin ba mu halicce ku daga ruwa wulaqantacce ba? Sai mu ka sanya shi a cikin mahaifa abar kawwamewa?” - (Suratul Mursalat, aya ta 20 -21). A wata ayar kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Dan Adam ya kalli da mene ne aka halicce shi? An halicce shi ne daga wani ruwa mai tunkudowa (shi ne digon maniyyi wanda yake fitowa a lokacin saduwa)." - Suratul Dariq aya ta 5 - 6. Wadannan ayoyi da makamantansu su na nuna mana cewa, idan yana taqama da ...

GIRMAN KAI KASHI NA SHABAKWAI

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? Ci gaba... 2- Mataki na biyu: Jin tsoron Allah da ganin girmansa. Duk mutumin da yake jin tsoron Allah da ganin girmansa ba zai siffantu da girman kai da ji-ji-da-kai da taqama ba, domin jin tsoron Allah da ganin girmansa, zai sanya ma sa ya riqa karvar gaskiya, kuma ba zai kasance mai wulaqanta mutane ba. A nan mutum zai riqa qoqarin bin umarnin Allah da Manzon sa (saw) wajen yin abin da su ka yi umarni da shi. Duk wanda ya siffantu da haka kuwa, ba zai riqa wulqanta mutane ko ya daga mu su kai ko ya nuna mu su isa ba. Domin hadisi ya tabbata daga Iyadh bn Himar (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya yi mini wahayi akan ku riqa qan-qan da kai, har ya zamanto wani bai yi alfahari akan wani ba. kuma wani bai wuce gona da iri akan wani ba."...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA SHIDA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 8: Waxanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su? AMSA: Haqiqa hanyoyin magance wadannan cututtuka sun danganci abin da ya sabbabawa mai su dabi'antuwa da su. Matakan da za su taimakawa wajen rabuwa da su su ne kamar haka: 1- Mataki na farko: Mutum ya san iyakacin kansa da kuma gazawarsa. A nan mutum mai girman kai zai kalli kansa a matsayinsa na xan Adam, wanda a da babu shi, sai Allah ya samar da shi, kuma ya tsara halittar sa a yadda ya ga dama, kuma ya ba shi daga abin da ya so, kuma a qarshe zai mutu babu makawa. Mutum zai kalli gazawarsa a matsyinsa na dan Adam mai gangar jiki wanda ba ya iya rayuwa sai ta hanyar numfashi da Allah ya hore ma sa da ci abinci da sha da yin bawali da bayan gida. Kuma cuta tana iya samun sa a lokacin da ba ya so. Sannan ya dubi gazawar sa ta bangaren gani da ji da sauran al'amura d...

GIRMAN KAI KASHI NA SHABIYAR

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 6: Wane irin narko Ubangiji (swt) ya tanadawa ma su girman kai da ji-ji-da-kai da nuna taqama? Ci gaba... B) Uqubar da Allah ya ke yi wa masu girman kai a ranar lahira. i) Allah yana wulaqantar da ma su girman kai a ranar Al-qiyama, domin hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Za a tashi ma su girman kai da ma su taqama ranar alqiyama, an mayar da halittarsu kamar qwayar komaiya, mutane su na tattaka su, saboda qasqancin su a gurin Allah.” (Attawadu'u wal khumul na Ibn Abiddunya, Hadisi na 225) ii) Qarshen makomar mai girman kai ita ce wuta: Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Lallai wadanda su ke girman kai ga barin bauta mini da sannu za su shiga Jahannama su na qasqantattu." - (Suratul Gafir aya ta 60). A wata ayar kuma, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Za a ce: ku shiga qofofin Jahannama kuna ma su dauwama a cikinta. Tir da mazaunin masu girma...

DUNIYAR NAN

MISALI: wani mutum ne yana zaune da iyalansa, mata daya da 'ya'ya 6, cikin jin dadi da walwala. Saboda a gaskiya yana samun kudi, ga shi kuma ba kankamo ba ne, ana cikin rayuwar jin dadi. Ran nan sai duniya ta yi masa juyin waina, daman kwallon mangwaro ce. Daga nan rayuwa ta tsananta har ta kai ga abin da za a ci ma sai an yi titikwati. Hausawa sun ce: idan zamani ya riski man shanu ko an toya shi ba za iyi kamshi ba. Haka mutumin ya dinga wahala da ka ganshi ko dayan cikin iyalansa kasan suna karba a jika. Ran nan an kwana an tashi ba abin da a kasa a bakin salati. Da sassafe shi da uwargidan suka fita kwakuduba. Yana tsaye bayan hantsi ya keto sai ya hangi mai kwalba garwa sai wani tunani ya keto masa, kowa ya tuna da bara bai ji dadin bana ba, ya tuno da gwangwanayen da suka dun ga shan madara, bournvita, milo, kifin gwangwani da sauransu lokacin duniya na yi musu tafi, ba yanzu ba da duniya ta juya tana yi musu gwalo ba. Ya kira dan gwangwan suka je gida ya debo masa ya sa...

LABARIN BAFFULATANI

Wani bafulatani ne yana aiki a gonar sa sai motar yan siyasa tayi accident kusa da gonar sa. Da ya qarasa wurin sai ya tarar ko motsi basa yi. Sai ya yanke shawarar ya haka rami ya binne su. Ya binne biyu daga ciki sannan ya koma kan dayan. Da yaga xaa binne shi sai yace bai mutu ba fa amma fafur bafulatani yaqi kulawa yaje kawai ya binne shi. Tirkashi.. can sai wasu mutane suka zo tambayar masu mota da suka yi accident sai bafulatani yace eh ya gansu sun mutu ya binne su amma daya yayi masa magana yace bai mutu ba amma duk da haka na binne shi saboda kasan dan siyasa da karya zai iya mutuwa ma yace bai mutu ba. Shin ya gaskiyar Dan Fulani take.

GIRMAN KAI KASHI NA SHA HUDU

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 6: Wane irin narko Ubangiji (swt) ya tanadawa ma su girman kai da ji-ji-da-kai da nuna taqama? AMSA: Haqiqa ayoyi ma su yawa da hadisai ingantattu sun bayayyana irin uqubar da Allah Madaukakin Sarki ya tanadawa ma su girman kai tun a nan duniya da kuma ranar tashin qiyama. A) Uqubar da Allah ya ke yi wa masu girman kai a duniya: i) Allah Madaukakin Sarki ba ya datar da ma su girman kai da shiriya musamman girman kai da ya hadu da kafurci, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Da sannu zan kautar da wadanda su ke girman kai a ban qasa ba tare da wani haqqi ba daga barin ayoyi na. Kuma ko da sun ga kowacce irin aya ba za su yi imani da ita ba. Kuma idan su ka ga tafarkin shiriya, ba za su riqe shi tafarkin shiriya ba. Idan kuma su ka ga tafarkin bata sai su riqe shi a matsayin tafarki. Abin da ya sa domin su sun qaryata ayoyi na, kuma sun kasance rafkanannu daga barinsu." - (Suratul Aaraf...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA UKU

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA BIYAR 5: Wadanne dalilai ne su ke nuna haramcin girman kai? AMSA: Haqiqa dalilai da su ke nuna haramcin girman kai su na da yawa, amma ga kadan daga cikin su: Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa shi Allah ba ya son ma su girman kai.” - Sauratun Nahli, aya ta 23. Kuma Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa Allah ba ya son duk wani mai taqama da jiji da kai, mai alfahari.” - Suratul Lukuman aya ta 8. A wata ayar kuma ya ce: “Haqiqa Allah ba ya son ma su girman kai da alfahari.” - Suratul Qasas aya ta 76. Hadisi kuma ya tabbata daga Iyad bin Himar (rain), daga Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya yi mini wahayi akan ku riqa qanqan da kan ku, ta yadda wani ba zai yi wa wani alfahari ba, kuma wani ba zai wuce gona da iri akan wani ba.” - (Muslim: 7104, bugun Darul Fikir). Akwai kuma ayoyi da hadisai da su ke nuni akan narko da uquba ko sakamakon ma su girman k...

facebook flower code

[[491536427542626]] [[487972157899053]] [[487981821231420]] [[487979211231681]] [[493969730632629]]

CIN HANCI DA RASHAWA

YAKI DA RASHAWA Da 'Yan Jam'iyyar Adawa Buhari Yake Yaki, Inji Tanko Yakasai Fitaccen dan siyasan nan da ke jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ake kama 'yan jam'iyyar adawa da suna yaki da rashawa a gwamnatinsa. A jawabin da ya fitar a jiya, Dattijo Yakasai, ya kawo misali da kama tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da aka yi da kuma sauran 'yan jam'iyyar adawa da aka kama. Ya ce babbar damuwarsa a yanzu shine yadda Buhari ke neman dawo da salon mulkin sa na soja a wannan gwamnati ta siyasa. Ya kuma yi kira ga shugaban kasan da ya gudanar da adalci ga al'ummar Najeriya a shirin da yake na yakar rashawa. .

Matar mahauci

Matar Mahauci ta kai shi kara gaban Alkali, aka aika masa sammaci ya zo. Da ya iso sai Alkali, ya sa Dan wanka ya tambayi matar akan me take karar mijinta, sai matar ta ce, 'Ni ba wani abu ya dame ni da shi ba illa rashin wanka.' Aka ce wa Mahauci "to kai kaji. Matarka ta ce ba ka wanka" Mahauci yayi shiru, can sai ya ce 'To gafarta Malam na sawwake mata ta je ta auri kwado, ni kuma na je in nemi akuya. In kece yazakiyi

ANKO JI KUNYA

Wani mutum ya je gidan abokinsa aka kawo musu abinci suna ci. Can sai bakon ya ce, "kai Wane kai kam ka yi sa'a". Ya ce "Wace irin sa'a?, ya ce "Matarka ta iya abinci". Wancan ya yi dariya ya ce "Taka fa?" Sai bakon yace, "Ni tawa me za a yi da irin girkinta. "Sai in hada kayan cefanena mai tsada in kawo mata, sai ta dauka ta kwaba shi ta kwaba, ta kwaba.." yana cikin fadin haka sai yaji motsin takalma. Ya daga kai haka sai ya ga ashe matarsa ce ta leko gidan bai saniba; sai ya ce "ya ko yi dadi". Shin maizaka kira wannan mutum yi comment

ASSALIN KARIN MAGANAR GOBARAR TITI A JOS

An taba yin wata mace a Jos, wai ita Titi. Wata rana Titi ba ta gida sai gobara ta tashi. Kayan Titi duk suka kone kurmus. Ita kuma mai fuskar jama'a ce, don haka mutane da yawa suka zo mata jaje. Wanda kuma duk ya zo sai ya dan kawo wani abu ya ba ta. Da aka gama jaje sai Titi ta ga abin da ta samu ya zarce wanda gobarar ta cinye mata. Sai ta ce "Ai ni wannan gobarar gaba ta kai ni". Daga nan aka samu in mutum ya rasa wani abu amma rashin ya kawo masa samun abin da ya fi shi, to sai ya ce "Ai ni gaba ta kai ni; gobarar Titi a Jos". ");border:0px;padding:2px;margin:2px;"> A Jiye Comment Don't mamaki kuma kaiya tambaya

DUkka Biyun

Wani mutum yana kwance ba shi da lafiya, da aka gama abinci sai aka ce Wane wa takila ba zai iya cin tuwo ba, a tambaye shi ko ya fi son a dama masa kunu? Da aka tambaye shi sai ya miko hannunsa yana kada yatsunsa biyu, da kyar yana nishi, ya ce 'Ayi duka biyun'.

SATA CIKIN ZAGINKA.

Wani yaro ne yayi aure ya tare acikin gidansu wato inda iyayenshi suke, ana xaune lfy rannan fada ya hadashi da matarshi, da ransa ya baci sai ya dauki tabarma ya nufi soron gidansu wai xaikwana. To dama ba wuta asoron yana kwanciya sai ya buga tsaki yace kai "allah ya tsinewa mata amma banda uwata" sai yaji ance "SATA CIKI" nima takaicinta ne ya koroni nan.". Ashe babansa ne shima yaji axava ya gudo xauren. Hmmm Mata ku dinga raga wa maza.

Yan shaye shaye.

Wani dan shaye -shaye ne mamansa ta rasu sai yazo ya fadawa abokansa en shaye- shaye sai suka yanke shawaran suje suyi Ta' aziyyar mahaifiyar Abokinsu Suna zuwa sai aka wakil ta babbansu domin yayi addu ' a kawai Gogan naka sai yafara Ya dubi dama da hagu Mutane ne Jingim Sai yace"Na nan Sannunku na nanma Sannun ku ashe Su umma anketa qasa To Allah yaji kanta Allah Yamata Ehya ne Yane .. .!! Qurhuwallahu 3- 3 Fatiha Only 1 Ranar rabon Gado I will come back Eyato baba zomu sulale . Kawai suka Fita kunji manya fah

Gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwan rufe kwalejin Hassan Ibrahim Gwarzo a dalilin fasikanci da dalibai maza sukeyi wa junansu.

Gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwan rufe kwalejin Hassan Ibrahim Gwarzo a dalilin fasikanci da dalibai maza sukeyi wa junansu. Mataimakin gwamnan jihar Hafiz Abubakar yace bayan hakan kuma gwamnatin ta nada wata kwamiti domin gano mene ainihin abinda ya faru a makarantan. Ana zargin daliban makarantan maza dayin luwadi a tsakaninsu inda har abin yafito yasa wadansu iyaye suke ta cire'ya'yansu a makarantan. Allah ya kauta. Amin .

HANYOYI 26 DON KYAUTATWA IYAYE

HANYOYI 26 DOMIN ZAMAN LAFIYA DA IYAYE 1. Ka ajiye wayarka yayin da Iyayenka suke yi maka magana. Kar ya zamanto suna yi maka magana, kai kuma kana danne-danne awayarka. (Browsing ko Chatting). - Wannan Rainin wayo kenan. 2. Ka rika neman shawara awajensu. Kuma idan sun baka shawara ka rika dauka kana amfani da ita. Koda akan neman aurenka ne- Girmamawa kenan. 3. Kar ka rika tsoma baki acikin maganarsu, har sai idan sunyi maka izini. Kuma duk zancen da zakayi dasu, wajibi ne kayi amfani da zababbun kalmomi na Musamman. 4. Ko da an samu rashin fahimtar Juna atsakaninka dasu, kar ka yarda su fahimci ranka ya baci, ballantana har ka furta musu wata mummunar kalma wacce zata Sosa musu rai. 5. Ka rika yaba musu abisa dukkan abinda sukayi maka komai kankantarsa. Koda addu'a sukayi maka, to lallai ka tsaya kayi musu godiya abisa wannan. 6. Ka rika girmama 'Yan uwansu ab okansu. Ka rika ziyartarsu kana Kyautata alakarka dasu. Domin girmamasu kamar girmama Mahaifan naka ne. 7. Duk lokac...

GIRMAN KAI KASHI NA SHA BIYU

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA. Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah. TAMBAYA TA 4: Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai? Ci gaba... 9- Kyawun Halitta: Kyawun halitta baiwa ce da Allah (swt) ya kan baiwa wanda ya ga dama daga cikin bayinSa, kamar yadda ya baiwa Annabi Yusuf (as) da sauran su. Wadansu mutane, maimakon su gode wa Allah (swt) da ya yi mu su wannan baiwar sai su butulce ma sa ta hanyar yin girman kai da jin isa da wulaqanta mutane, bari ma, har da yiwa wadansu gori da kushe halittar da Allah (swt) ya yi mu su. Kamar yadda ake samu daga wadansu matasa da 'yan mata wadanda su ke qafafa da girman kai, da wulaqanta abokanansu da qawayensu, don irin kyawun da Allah ya ba su, wasu ma wannan ya kan kai su ga shiga gasar saruniyar kyau, ko tallan kamfanununka, ko fina-finai da waqe-waqen batsa, daga nan kuma sai su shiga karuwanci su halakar da kansu, a qarshe kuma su zo suna nadama a lokacin da nadama ba za ta yi musu amfani ba....

DUNIYA KENAN

Magana kamar magani ce idan ta yi yawa sai ta sa cuta. Jita-jita maketata ne suke shirya ta, wawaye ne suka yada ta, maras sani ne yake aiki da ita. Mugun aboki kamar inwa ne sai kana cikin haske kake ganin sa. Duk yadda takardar kudi ta lalace kudi ce, takardar nama kuwa ko an shafa mata mai banza ce. Gaskiya mabudin nasara ce, hakuri mabudin ni'ima ne, ilimi kuwa mabudin arziki ne. Duniya dakin jarabawa ce, kowa da alkalaminsa da takardarsa, amma kowa da lokacin da aka dibar masa, idan ya kare nan take za a kwace takarda a kai ta wajen maki da tantancewa. Kada ka damu da abinda wani ya rubuta ko yake rubutawa. Kai dai shiga taitayinka, kowa tasa ke fisshe shi. Rayuwa da mutuwa sun yi kama da juna. A ranar da ka zo duniya ka taho tsirara sai an yi maka wanka a tufata ka. Haka ma idan ka mutu sai an tsiraice ka, a wanke ka, sannan a suturta ka. A lokacin da ka shigo duniya ba ka iya tafiya sai dai a dauke ka. Haka ranar mutuwa ba ka san ma ana taulahi da kai ba. Ka shigo duniya kan...