DUNIYAR NAN

MISALI: wani mutum ne yana zaune da iyalansa, mata daya da 'ya'ya 6, cikin jin dadi da walwala.

Saboda a gaskiya yana samun kudi, ga shi kuma ba kankamo ba ne, ana cikin rayuwar jin dadi. Ran nan sai duniya ta yi masa juyin waina, daman kwallon mangwaro ce.

Daga nan rayuwa ta tsananta har ta kai ga abin da za a ci ma sai an yi titikwati.

Hausawa sun ce: idan zamani ya riski man shanu ko an toya shi ba za iyi kamshi ba. Haka mutumin ya dinga wahala da ka ganshi ko dayan cikin iyalansa kasan suna karba a jika. Ran nan an kwana an tashi ba abin da a kasa a bakin salati.

Da sassafe shi da uwargidan suka fita kwakuduba. Yana tsaye bayan hantsi ya keto sai ya hangi mai kwalba garwa sai wani tunani ya keto masa, kowa ya tuna da bara bai ji dadin bana ba, ya tuno da gwangwanayen da suka dun ga shan madara, bournvita, milo, kifin gwangwani da sauransu lokacin duniya na yi musu tafi, ba yanzu ba da duniya ta juya tana yi musu gwalo ba. Ya kira dan gwangwan suka je gida ya debo masa ya saya ya biya shi. Cikin sauri ya sayo ma yara abinci suka kama karyawa, can sai ga uwar ta dawo ta yi farin cikin ganin sun sami abinci.

Ta tambayi maigidan yadda aka yi, ya kwashe labari ya fada mata, mhm! Kun san me ya faru?

Ai nan take matarnan ta saka hannu aka tayi ta rusa ihu, da mijin ya tambaye ta lafiya?

Da kyar ta daure ta fada masa cewar a ciki gwangwanayen na akwai wanda ta yi ajiyar 147,000.

TO IDAN KAINE ME ZAKA CE MATA?

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA