BOM YA TASHI A KASUWAR WAYOYI TA JIHAR KANO
Yadda Mata 'Yan Kunar Bakin Wake Guda Biyu Suka Tada Bam Din Da Ya Tashi A Kasuwar Wayoyi A Jihar Kano.
Bamabamai biyun da suka ta shi a kasuwar wayoyi ta Farm Centre da ke birnin jihar Kano a yau, bincike ya nuna cewa wasu mata 'yan kunar bakin wake ne guda biyu suka yi sanadiyar tashinsu.
Wani da lamarin ya auku a gabansa ya fadi cewa bam na farko ya tashi ne a tsakiyar kasuwa, yayin da kuma na biyun ya tashi a bakin kofar shigar kasuwar.
Shi ma wani ganau ba jiyau ba, ya fadawa majiyarmu cewa yana daga cikin wadanda suka hana yarinyar shiga cikin kasuwar, wanda hakan ya sa ta tashi bam din a bakin kofar kasuwar.
An yi ta ganin 'yan kasuwa na ta diban gawarwaki da wadanda suka samu rauni zuwa a asibiti a motocin jama'ar da suka bayar da gudummawa. Kwamishin 'yan sandan jihar Kano, Muhammadu Katsina ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya fadawa manema labarai cewa wasu mata 'ya kunar bakin wake ne guda biyu suka yi sanadiyar tashin bamabamai biyun a kasuwar. Sannan kuma ya kara da cewa mutane 11 ne suka rasa ransu, yayin da kuma 50 suka samu rauni.
Allah Kayi mana Maganin Abunda yafi karfin mu
Ya allah kakawo mana karshen wannan bala'i
Ameen
ReplyDelete