YININKA BAKON KA NE DON HAKA KA KYAUTATA MASA
YININKA BAKON KA NE DON HAKA KA KYAUTATA MASA
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺒﺼﺮﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﻳﺎﺑﻦ ﺁﺩﻡ، ﺇﻧﻤﺎ ﺃﻧﺖ ﺃﻳﺎﻡ، ﺇﺫﺍ ﺫﻫﺐ ﻳﻮﻡ ﺫﻫﺐ ﺑﻌﻀﻚ .
HASANUL BASARI ya na cewa:Ya kai dan Adam! Lallai kai kamar ranaku ne, idan yini daya ya gushe wani sashen ka ya wuce. Ma'ana idan ko wane yinin mutum ya wuce ya na 'kara kusantar kabari kenan.
ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ : ﻳﺎﺑﻦ ﺁﺩﻡ، ﻧﻬﺎﺭﻙ ﺿﻴﻔﻚ ﻓﺄﺣﺴﻦ ﺇﻟﻴﻪ؛ ﻓﺈﻧﻚ ﺇﻥ ﺃﺣﺴﻨﺖ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﺭﺗﺤﻞ ﺑﺤﻤﺪﻙ، ﻭﺇﻥ ﺃﺳﺄﺕ ﺇﻟﻴﻪ <>ﺍﺭﺗﺤﻞ ﺑﺬﻣﻚ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻟﻴﻠﺘﻚ .
Ya 'kara ce wa:Ya kai dan Adam! yininka bakon ka ne saboda haka ka kyautata masa. idan ka kyautata masa zai tafi yana mai gode maka, idan kuma ka muzanta masa zai tafi yana sukan ka. Haka zalika daren ka.
ﻭﻗﺎﻝ : ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ : ﺃﻣﺎ ﺍﻷﻣﺲ ﻓﻘﺪ ﺫﻫﺐ ﺑﻤﺎ ﻓﻴﻪ، ﻭﺃﻣﺎ ﻏﺪﺍ ﻓﻠﻌﻠﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻛﻪ، ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻠﻚ
ﻓﺎﻋﻤﻞ ﻓﻴﻪ . Kuma ya ce: Duniya dai abu uke ne kawai, ma'ana kwanaki uke ce kawai. Idan ka ga jiya toh ya tafi da abinda ke cikinsa, amma gobe; wata 'kila ba za ka riskesa ba, amma yau da ka ke cikin sa, na ka ne don haka ka yi aiki acikinsa.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﻣﺎ ﻧﺪﻣﺖ ﻋﻠﻰ ﺷﻲﺀ ﻧﺪﻣﻲ ﻋﻠﻰ ﻳﻮﻡ ﻏﺮﺑﺖ ﺷﻤﺴﻪ، ﻧﻘﺺ ﻓﻴﻪ ﺃﺟﻠﻲ <>ﻭﻟﻢ ﻳﺰﺩﺩ ﻓﻴﻪ ﻋﻤﻠﻲ .
Sahabi ABDULLAHI BN MAS'UD ya na cewa: Ban ta ba yin wata nadama ba sama da nadamar da na ke yi idan rana ta fadi, kuma ajalina ya ragu, kuma aikin alkhairina be karu ba a wannan ranar.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﺇﺿﺎﻋﺔ ﺍﻟﻮﻗﺖ ﺃﺷﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﺕ؛ ﻷﻥ ﺇﺿﺎﻋﺔ ﺍﻟﻮﻗﺖ ﺗﻘﻄﻌﻚ ﻋﻦ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺍﻟﺪﺍﺭ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻭﺍﻟﻤﻮﺕ ﻳﻘﻄﻌﻚ ﻋﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﺃﻫﻠﻬﺎ .
IBNUL QAYYUM ya ke cewa: 'Bata lokaci a banza ya fi tsanani akan mutuwa, domin 'bata lokaci a banza ya na yanke ganawar ka da Allah da gidan karshe. Ita mutuwa kawai tana yanke tsakaninka da duniya ne da ababen cikinta.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺴﺮﻱ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﻐﻠﺲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﺇﻥ ﺍﻏﺘﻤﻤﺖ ﺑﻤﺎ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ ﻣﺎﻟﻚ، ﻓﺎﺑﻚ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ
ﻋﻤﺮﻙ . SIRRIYU BN MUGALLIS yana cewa: Idan damuwa ya dauke ka game da abinda ya ke ragye maka dukiyarka, toh ka yi kuka akan abinda ke ragye maka kwanaki ko shekarun ka.
Don haka kuka ya kamata mu rinqa yi a ranar zagayowar haihuwar mu ba murna ba, domin shekara daya ya ragu a cikin kwanakin da Allah ya diba mana.
Kuma kamata yayi mu zauna mu tunano zunubban sai mu tuba ma Allah tuba na gaskiya. Kuma mu daura niyyar gyara halayen mu da kyautata Ibadun mu, hakika babu mai yin haka sai mai hankali da tunani.
Allah yasa mu yi amfani da lokaxcin mu, kafin rashinsa.
Comments
Post a Comment