GIRMAN KAI KASHI NA ASHIRIN DA DAYA
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 8:
Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?
Ci gaba...
8 - Mai yin girman kai don kyawun halitta:
Mai irin wannan hali ya sani cewa; duk kyawun halittar da mutum yake da shi Allah zai iya kawar da shi a duk sanda ya so; ko dai sakamakon tsufa, ko wani dalili na daban. Sau nawa mai taqama da kyawun halitta zai yi hatsari ko gobara ta rutsa da shi, sai ya wayi gari nakasasshe? Ko tauyayye? Wani kunnen sa ya cire ko ya qone? Wani hancinsa ya cire ko ya qone? Wani fatarsa ta salube ko ta tauye?
Qaramin misali da ya ishi mai girman kai izina shi ne yadda cikin mutum yake qunshe da qazanta, hancinsa majina, kullun sai ya shiga bayan gida aqalla sau daya ko sau biyu. Irin wannan shi ne har kyawun siffarsa zai sanya shi ya yi fito na fito da Allah? Yana yiwa bayinsa dagawa?
Sau nawa za ka sami mace da ake misali da ita a wajen kyau, yau da gobe; tsufa da halin rayuwa sun tafiyar da kyan? Sau nawa mutumin da yake alfahari da kyau, amma Allah ya jarrabe shi da wata cuta ko rashin lafiya har sai sun gusar da kyansa? Idan duk haka bata faru ba, akwai mutuwa da rubewa a cikin qabari.
Haqiqa tsoron Allah da bin dokokinsa su ne mafita ga dukkanin mai son haduwa da Allah lafiya.
9 - Mai yin girman kai don yawan ibada. Haqiqa wannan ya fi kowa wauta domin ba shi da tabbas shin Ubangijinsa da yake yi wa ibadar ya karba ko bai karba ba? Kuma ya yarda da shi ko bai yarda da shi ba? Domin idan Allah bai karbi wannan ibadar ba, to ya yi asara guda biyu; asara ta rashin karbar ibadarsa da asara ta laifin girman kai da alfaharin da ya kasance yana yi.
Idan kuwa ya yi ibadarsa don Allah kuma ya qanqan da kai, sai Allah Madaukakin Sarki ya saka masa tun a nan duniya; Allah ya ba shi rayuwa mai kyau da aminci, kuma a gobe qiyama Allah ya sanya shi a aljannarsa. Allah ka sa mu dace, amin.
Sai mun hadu a fitowa ta 22 da yardar Allah.
Comments
Post a Comment