GIRMAN KAI KASHI NA ASHIRIN

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

Ci gaba...

6 - Masu yin girman kai don yawan mabiya: Haqiqa ma su girman kai don yawan mabiya ko magoya baya a cikin wani alamari su sani cewa ba su ne suke da mallakar zuciyar magoya bayan nasu ba, don haka Allah zai iya juya zukatansu su yi mu su tawaye a ko da yaushe, domin shi ne yake juya su yadda ya ga dama.

Dalili kuwa shi ne hadisin da ya tabbata daga Abu Hurairah (ra), ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa idan Allah Madaukakin Sarki ya so bawansa, sai ya kira Mala’ika Jibrilu ya ce: Haqiqa ni ina son wane, kai ma ka so shi. Sai Mala’ika Jibrilu ya so shi, sannan sai ya yi shela a cikin sama ya ce:

Haqiqa Allah yana son wane, ku ma ku so shi. Sai Malaikun da ke sama su so shi, sannan sai a sanya ma sa karbuwa a ban qasa. Idan kuma Allah ya qi bawansa, sai ya kira Malaika Jibrilu ya ce: Haqiqa ina qin wane, kai ma ka qi shi. Sai Malaika Jibrilu ya qi shi, sannan sai ya yi kira a cikin sama ya ce: haqiqa Allah yana qin wane, ku ma ku qi shi. Sai Malaiku da ke sama su qi shi, sannan sai a sanya masa baqin jini a bayan qasa." - (Bukhari: 7485).

Haqiqa wannan na nuni akan cewa idan Allah ya so ya rushe yawan mabiyan mutum, musamman wanda yake yin girman kai don yawan mabiya, sai ya sanya masa baqin jini, sai mutane su tsane shi, kuma komai kudin sa, komai iliminsa, komai mulkinsa, sai su juya masa baya. Haqiqa misalai ma su yawa sun kasance akan wasu ma su mulki da Allah ya janye mu su yawan mabiya, sai mabiyan su su ka dawo su na yaqar su, su na qoqarin kawar da su daga kan mulkin da suke taqama da shi.

Wannan shi ne abin da ya kamata mutumin da Allah ya ba shi yawan mabiya ya kalla. Sannan ya sani idan Allah ya ga dama yakan jarrabi mutum da yawan mabiya tun a nan duniya, kuma koda kuwa akan daidai yake, sai mabiyan su zamanto masa fitina da qiyayya. Sau nawa ne mutumin da Allah ya bashi magoya baya daga baya Allah ya jarrabeshi magoya bayan su ka juya ma sa baya? mutanen da suke taruwa a qofar gidansa su ka daina taruwa? Kuma wadanda su ka mori shi su ka juya ma sa baya? Hatta iyalansa su ka nemi saki ba tare da wani daliliba, yayansa kuma su ka daina mutunta shi saboda a yanzu ba shi da komai? Haqiqa wannan babban darasi ne ga duk mai daukar izina. Allah ya kare mu baki daya.

7- Mai yin girman kai da alfahari don fasahar harshe da Allah ya ba shi.

Wannan inda ya yi izina zaiga sau nawa mutanen da Allah ya basu fasaha da zalaqa; amma daga baya Allah ya jarrabe su da wasu cututtuka wadanda har ta kai ba sa iya magana, kamar hawan jini ko shanyewar tsagin jiki, ko sakamakon hatsari ko rikicewar kwakwalwa? Sannan kuma ya yi duba ga wadanda tun asali Allah bai ba su ikon yin magana ba, kamar kurame da bebaye; zai fahimci lallai ganin damar Allah ne da ya bashi wannan fasahar, kuma idan ya so sai ya jarrabeshi ya wayi gari ba zai iya magana ba ballantana ya nuna fasahar kamar yadda ya jarrabi wasunsa. Kuma ya sani akwai wadanda Allah ya fifita su akan sa wajen fasahar harshe da matsayi, amma ba su yi irin halin sa ba, face godiya ga Allah Madaukakin Sarki.

Sai mun hadu a fitowa ta 21 da yardar Allah. °

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA