ASSALIN KARIN MAGANAR GOBARAR TITI A JOS

An taba yin wata mace a Jos, wai ita Titi. Wata rana Titi ba ta gida sai gobara ta tashi. Kayan Titi duk suka kone kurmus. Ita kuma mai fuskar jama'a ce, don haka mutane da yawa suka zo mata jaje. Wanda kuma duk ya zo sai ya dan kawo wani abu ya ba ta. Da aka gama jaje sai Titi ta ga abin da ta samu ya zarce wanda gobarar ta cinye mata. Sai ta ce "Ai ni wannan gobarar gaba ta kai ni". Daga nan aka samu in mutum ya rasa wani abu amma rashin ya kawo masa samun abin da ya fi shi, to sai ya ce "Ai ni gaba ta kai ni; gobarar Titi a Jos".

");border:0px;padding:2px;margin:2px;">
A Jiye Comment Don't mamaki kuma kaiya tambaya

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA