WASU TAMBAYOYI

TAMBAYA: shin mece ce nasabar Manzon Allah (S.A.W)??

AMSA: Manzon Allah shine muhammadu, dan Abdullahi, dan Abdulmudallabi, dan hashim, dan abdul-Munaf, dan kusayyi, dan kilabi, Nasabarsa (S.A.W) tana saduwa, ga Annabi Isma'il dan Annabi Ibrahim Alaihimus-salam.

TAMBAYA: Mece nasabar mahaifiyar Sa (S.A.W)??

AMSA: Mahaifiyarsa (S.A.W) ita ce Nana Aminatu 'yar Wahabi, dan Abdul-Munafi, dan Zuhurata, dan kilabi.

TAMBAYA: Ta ina nasabar mahaifinsa take haduwa (S.A.W)??

AMSA: Nasabar mahaifinsa (S.A.W) tana haduwa ta wajen kakanSa na biyar (5), wato Kilabi.

TAMBAYA: Yaushe mahaifinsa yayi wafati??

AMSA: Mahaifinsa (S.A.W) yayi wafati yana cikin mahaifiyarsa wato kafin a haifeshi cikinsa yana watanni biyu (2) (S.A.W).

TAMBAYA: Yaushe mahaifiyarsa tayi wafati??

AMSA: Mahaifiyarsa tayi wafati yana da shekaru shida (6) an binneta a Abawa'i.

TAMBAYA: Wacce rana aka haifi Manzon Allah (S.A.W)??

AMSA: An haifi Annabi (S.A.W) Ranar Liitinin.

TAMBAYA: Wecce ranar yayi wafati, kuma a wacce shekara??

AMSA: Yayi wafati ranar Litinin sha-uku (13) ga watan Rabi'ul Auwal, a shekara ta goma sha daya (11) bayan hijira.

TAMBAYA: Wane ne khalifan farko bayan wafatin Annabi (S.A.W)??

AMSA: Sayyidina Abubakar (R.T.A.).

TAMBAYA: Wane ne Sayyidina Abubakar??

AMSA: shi ne mutum na farko da ya fara bada gaskiya da Annabi (S.A.W) a maza manya shine abokin Manzon Allah na kut-da-kut da suka yi hijira, shine khalifansa. Shine mahaifin amaryarsa da yafi so, wato Nana Aisha (RTA) Allah shi ne masani.

TAMBAYA: Wace ce Nana Aisha??

AMSA: Ita ce 'yar Sayyidana Abubakar, Amaryar Manzon Allah (S.A.W).

TAMBAYA: Mene ne takaitaccen tarihinta Nana Aisha??

AMSA: Nana Aisha, ita ce mai gaskiya, diyar mai gaskiya wato Abubakar, ana yi mata alkunya da uwar Abdullahi, wato Abdullahi ibn zubair dan Asama'u, yar uwarta, domin ita bata taba haihuwaba, amma a rayuwarta an ce ta taba yin aure.

-Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana mutukar kaunar ta, ita ce kawai matar da ya aura tana budurwa, Malamai sun hadu a kan cewa duk duniyar nan matan da suka fi kowacce daraja a wajen Allah da Manzon (S.A.W). Aisha ce ta biyu (2), ko ta uku(3) wato daga Nana Fadimatu, sai Nana Khadija, sai kuma ita Nana Aisha, daga nan sai Nana Maryam, mahaifiyar Annabi Isa (AS) sai kuma Asiya matar Fir'auna, idan kuma a cikin iya matan Manzon Allah ne, to daga Nana Khadija, sai Nana Aisha, sai Nana Zainab Bintu jahshin, sai Nana Hafsatu bintu Umar bin khattab, sai ummu salama, sai kuma ragowar matan manzon Allah (S.A.W). -Nana Aisha ta kasance matar Manzon Allah ta biyu(2) a duniya daga mutuwar Nana khadija ita ya aura, ko da yake bai tare da ita ba a wannan lokaci ba, sai bayan an koma Madina.

Ya aure ta (S.A.W) tana da shekaru 6 ko 7, ya kuma tare da ita Nana tana da shekaru 8 ko 9 ko 10, a wadansu rawayoyi amma allah ne masani.

ZAMU CIGABA DA IZININ ALLH

YA ALLAH ABUN DA MUAKA RUBUTA DAI DAI ALLAH KABAMU LADAN ABUN ABUN D MUKAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MANA AMIN YA ALLHA

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA