GIRMAN KAI KASHI NA SHA SHIDA
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 8:
Waxanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?
AMSA:
Haqiqa hanyoyin magance wadannan cututtuka sun danganci abin da ya sabbabawa mai su dabi'antuwa da su. Matakan da za su taimakawa wajen rabuwa da su su ne kamar haka:
1- Mataki na farko: Mutum ya san iyakacin kansa da kuma gazawarsa.
A nan mutum mai girman kai zai kalli kansa a matsayinsa na xan Adam, wanda a da babu shi, sai Allah ya samar da shi, kuma ya tsara halittar sa a yadda ya ga dama, kuma ya ba shi daga abin da ya so, kuma a qarshe zai mutu babu makawa. Mutum zai kalli gazawarsa a matsyinsa na dan Adam mai gangar jiki wanda ba ya iya rayuwa sai ta hanyar numfashi da Allah ya hore ma sa da ci abinci da sha da yin bawali da bayan gida. Kuma cuta tana iya samun sa a lokacin da ba ya so. Sannan ya dubi gazawar sa ta bangaren gani da ji da sauran al'amura da yake da su kamar qarfi da mulki da kuma dukiya. Idan ya kalli wadannan da idon basira zai ga dukkaninsu taqaitattu ne.
A gefe guda kuma sai ya dubi girman Allah da isar sa da qasaitar sa da mulkinSa da yadda komai yake qarqashin ikonSa, da yadda ya tabar da ma su girman kan da su ka gabace shi da makamantansu ba tare da sun gagare shi ba.
Kamar Adawa da Samudawa da Fir'auna da Qaruna da sauran dagutai ma su girman kai a ban qasa.
Wannan zai sanya mai girman kai ya gane cewa shi ba komai ba ne, wadanda su ka fi shi ma sun gama tunqahon su, Allah ya yi maganinsu, saboda duniya budurwar wawa ce. Wannan zai qara nuna ma sa cewa girman kai da ji-ji-da-kai ba su cancance shi ba.
Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Shin lokaci bai zo wa dan Adam ba, wanda ya kasance ba komai ba ne? Haqiqa Mu Mun halicci dan Adam daga digon maniyyi kwababbe (maniyin namiji da qwan mace), sai mu ka sanya shi ya zaman to mai ji, da gani." - (Suratul Insan 1-2)
Wannan ayar ta nuna yadda dan Adam ya kasance a matsayin babu shi a wani lokaci a baya, amma aka samar da shi daga digon maniyyi, sannan kuma aka sanya ma sa ji da gani da lafiya, kuma kamar haka ne wata rana zai zamanto babu shi, kuma duk abin da yake taqama da shi zai iya rasa shi, ko ya mutu ya bar shi, kuma zai koma ga Allah Madaukakin Sarki ya sami sakamakon abin da ya aikata.
Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Sannan Allah zai matar da shi sai a bunne shi, sannan zai tashe shi a lokacin da ya so." - (suratu Abasa, aya ta 21-22)
Sai mun hadu a fitowa ta 17 da yardar Allah.
Comments
Post a Comment