GIRMAN KAI KASHI NA SHA BIYU

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 4:

Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?

Ci gaba...

9- Kyawun Halitta:

Kyawun halitta baiwa ce da Allah (swt) ya kan baiwa wanda ya ga dama daga cikin bayinSa, kamar yadda ya baiwa Annabi Yusuf (as) da sauran su.

Wadansu mutane, maimakon su gode wa Allah (swt) da ya yi mu su wannan baiwar sai su butulce ma sa ta hanyar yin girman kai da jin isa da wulaqanta mutane, bari ma, har da yiwa wadansu gori da kushe halittar da Allah (swt) ya yi mu su. Kamar yadda ake samu daga wadansu matasa da 'yan mata wadanda su ke qafafa da girman kai, da wulaqanta abokanansu da qawayensu, don irin kyawun da Allah ya ba su, wasu ma wannan ya kan kai su ga shiga gasar saruniyar kyau, ko tallan kamfanununka, ko fina-finai da waqe-waqen batsa, daga nan kuma sai su shiga karuwanci su halakar da kansu, a qarshe kuma su zo suna nadama a lokacin da nadama ba za ta yi musu amfani ba.

Wadannan su ne abubuwa guda tara a dunqule wadanda su ka fi shahara wajen sanya girman kai da taqama da alfahari. Allah ya fishe mu fadawa cikin sharrin su.

Sai mun hadu a fitowa ta 13 da yardar Allah.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA