GIRMAN KAI KASHI NA SHA UKU
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA BIYAR 5:
Wadanne dalilai ne su ke nuna haramcin girman kai?
AMSA:
Haqiqa dalilai da su ke nuna haramcin girman kai su na da yawa, amma ga kadan daga cikin su:
Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa shi Allah ba ya son ma su girman kai.” - Sauratun Nahli, aya ta 23.
Kuma Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa Allah ba ya son duk wani mai taqama da jiji da kai, mai alfahari.” - Suratul Lukuman aya ta 8.
A wata ayar kuma ya ce: “Haqiqa Allah ba ya son ma su girman kai da alfahari.” - Suratul Qasas aya ta 76.
Hadisi kuma ya tabbata daga Iyad bin Himar (rain), daga Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya yi mini wahayi akan ku riqa qanqan da kan ku, ta yadda wani ba zai yi wa wani alfahari ba, kuma wani ba zai wuce gona da iri akan wani ba.” - (Muslim: 7104, bugun Darul Fikir).
Akwai kuma ayoyi da hadisai da su ke nuni akan narko da uquba ko sakamakon ma su girman kai wanda wannan yake qara nuna haramcinsa.
Sai mun hadu a fitowa ta 14 da yardar Allah.
° ° °
Comments
Post a Comment