ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI : Duniya ta riga ta aureka dan uwa;
ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI : Duniya ta riga ta aureka dan uwa;
1. Idan ya zamto baka jiran sallah saidai sallah ta jiraka.
2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur’anin ka ba (wai bakada lokaci).
3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka sabawa ubangijinka.
4. Idan ya zamto kullum tunaninka yadda zakayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi.
5. Idan ya zamto baka karbar nasiha.
6. Idan ya zamto babu rayuwar da take birgeka sai rayuwar mawaka da ‘yan kwallo da makada.
7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa’azi ko karatun al-qur’ani.
8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheri sai watarana.
9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin addininka sai dai na neman duniya (boko).
10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon bai Qareka da komai ba.
Allah (swt) Ya yafe mana zunuban mu manya da qanana. Amin
Comments
Post a Comment