GIRMAN KAI KASHI NA SHA TAKWAS
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 8:
Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?
Ci gaba...
C. Hanyoyin magance girman kai da ji-ji-da-kai da taqama:
1- Mai yin girman kai domin asalinsa. Wannan zai tsaya ne ya kalli nasabarsa ta haqiqa, wato asalin sa digon maniyyi ne. Duk kuwa wanda asalin sa maniyyi ne to girman kai bai dace da shi ba, domin asalin nasa ba komai ba ne face qazanta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Shin ba mu halicce ku daga ruwa wulaqantacce ba? Sai mu ka sanya shi a cikin mahaifa abar kawwamewa?” - (Suratul Mursalat, aya ta 20 -21).
A wata ayar kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce: “Dan Adam ya kalli da mene ne aka halicce shi? An halicce shi ne daga wani ruwa mai tunkudowa (shi ne digon maniyyi wanda yake fitowa a lokacin saduwa)." - Suratul Dariq aya ta 5 - 6.
Wadannan ayoyi da makamantansu su na nuna mana cewa, idan yana taqama da asali ne, to asalinsa maniyyi ne wulaqantacce.kuma kowane dan Adam daga wannan asalin yake, babu mai girma sai wanda Allah ya girmama.
2- Wanda ya ke yin girman kai don ya na da dukiya:
Idan ya dubi farkon sa, zai ga ba a haife shi da arziki ba, kuma ko da mahaifansa ma su arziki ne, ai wannan arziqin ba mallakarsa ba ne. Kuma ya kalli qarshen sa; ya tuna cewa idan ya mutu ba zai tafi da komai qabari ba sai likkafani. Idan kuma ya kalli al'ummar da ta shude da kuma wadda ya ke cikinta a yanzu zai ga cewa wadanda su ka fi shi suna da yawa. Idan kuma ya qara lura zai ga akwai waxanda sun yi dukiya kuma sun mutu ba tare da sun ci amfaninta ba, ko kuma suna raye amma Allah ya tafiyar da dukiyar, ko kuma ga dukiyar amma Allah ya jarrabe su da rashin lafiya wadda ta hana su jin dadin arziqin, ko fitinanninyar mace, ko fitinannun 'ya 'ya, ko barayi, ko abokan gaba, ko dinbin bashi da yake wuyansa, ko kuwa uwa-uba rashin kwanciyar hankali, musamman a yankunan mu na Afrika; mutum idan ya fita ba ya samun nutsuwa cewa zai koma gida lafiya; saboda tsoron ko dai a kashe shi, ko a sace shi, ko a yi ma sa fashi, ba don komai ba, sai don wannan dukiyar da yake da ita.
Kuma ya kalli misalin da Allah Madaukakin Sarki ya ba mu game da Qaruna, wanda ya yi dagawa da girman kai saboda tunanin ilminsa da gogewarsa a kasuwanci su su ka bashi wannan dukiyar ba Allah ba. Sai Allah Madaukakin Sarki ya sanya qasa ta hadiye shi. Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: (Qaruna) ya ce: “Haqiqa an bani (dukiyar) ne don wani ilimi da nake da shi.
Shin bai san cewa haqiqa Allah ya halakar da wadansu qarnunnuka da suke gabaninsa wadanda sun fi shi qarfi da kuma tara dukiya ba …" - (Suratul Kasas aya ta 78)
A qarshe sai Allah ya halakar da shi, kamar yadda ya fada ya ce:
“Sai muka shafe shi da gidansa a cikin qasa, ba shi da wasu jama'a da za su taimake shi koma bayan Allah, kuma ba ya cikin wadanda ake taimakawa." - (Suratul Kasas aya ta 81)
Wani misalin kuma shi ne yadda Allah Madaukakin Sarki ya aiko iska ta qone gonar wani mai gona da ya cika baki ya yi dagawa da girman kai ga dan uwansa, yana nuna ma sa cewa shi ya fi shi dukiya, amma Allah Madaukakin Sarki ya nuna ma sa cewa shi yake da iko akan dukiyar da yake taqama da ita. Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ya kasance yana da amfanin gona, sai ya cewa abokinsa, alhali yana mai jayayya da shi ya ce: "Ni na fi ka yawan dukiya da kuma buwaya ta vangaren mabiya". - (Suratul Kahafi aya ta 34).
Wannan mutumin Allah Madaukakin Sarki ya nuna ma sa shi ba komai ba ne, kuma iko da wannan gonar a hannun Allah yake, ya yin da Allah ya tura iska ta qone masa gonar, sai ga ta a zube akan saiwowinta. Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Sai aka zagaye ‘ya’yan itatuwan na sa (da wuta suka qone) sai ya wayi gari yana tafa hannayensa (daya akan daya, yana mai sallallami) a sakamakon abin da ya kashe akan gonar, alhali tana kwance akan saiwoyinta, yana cewa: “kaico na! Dama dai ban hada Ubangijina da kowa ba." kuma bai kasance yana da wasu jamaa da za su taimake shi ba koma bayan Allah, kuma bai kasance wanda ake taimakawa ba." - (Suratul Kahfi aya ta 43).
Haqiqa wadannan misalai sun ishi mai hankali daukan izina, ya kiyayi fushin Allah Subhanahu wa Taala, tun kafin ya hadu da shi, ko kuma ya lalatar da dukiyar da yake tunqaho da ita.
Sai mun hadu a fitowa ta 19 da yardar Allah
Comments
Post a Comment