GIRMAN KAI KASHI NA SHA HUDU
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 6:
Wane irin narko Ubangiji (swt) ya tanadawa ma su girman kai da ji-ji-da-kai da nuna taqama?
AMSA:
Haqiqa ayoyi ma su yawa da hadisai ingantattu sun bayayyana irin uqubar da Allah Madaukakin Sarki ya tanadawa ma su girman kai tun a nan duniya da kuma ranar tashin qiyama.
A) Uqubar da Allah ya ke yi wa masu girman kai a duniya:
i) Allah Madaukakin Sarki ba ya datar da ma su girman kai da shiriya musamman girman kai da ya hadu da kafurci, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Da sannu zan kautar da wadanda su ke girman kai a ban qasa ba tare da wani haqqi ba daga barin ayoyi na. Kuma ko da sun ga kowacce irin aya ba za su yi imani da ita ba. Kuma idan su ka ga tafarkin shiriya, ba za su riqe shi tafarkin shiriya ba. Idan kuma su ka ga tafarkin bata sai su riqe shi a matsayin tafarki. Abin da ya sa domin su sun qaryata ayoyi na, kuma sun kasance rafkanannu daga barinsu." - (Suratul Aaraf aya ta 146).
A wata ayar kuma Ubangiji Maxaukakin Sarki ya ce: “Kuma haka ne, Allah yake toshe zuciyar duk wani mai girman kai, mai dagawa (daga barin gaskiya da shiriya). - Suratul Aaraf aya ta 12-13
ii) Allah yana kama ma su girman kai da uquba ta zahiri tun anan duniya. Misalai akan haka su na da yawa, ga kadan daga cikin su:
Misali na daya:
A lokacin da Iblis ya yi girman kai a bisa yiwa Annabi Adam (as) Sujjada, sai Allah ya yi fushi da shi, ya kore shi daga Al-jannah.
Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Allah ya ce: mene ne ya hana ka baka yi sujjada ba a ya yin da na umarce ka? Sai ya ce: ni na fi shi; ni ka halicce ni ne daga wuta, shi kuma ka halicce shi ne daga yunbu. Sai Ubangiji ya ce: ka sauka daga cikinta (aljanna), bai kamace ka ka yi girman kai a cikin ta ba. Ka fita daga ciki, haqiqa kana daga cikin qasqantattu.” - (Suratul Aaraf aya ta 12-13).
Wannan ayar ta nuna an kori Iblis daga rahamar Allah an wulaqanta shi, kuma ya tabe ya yi asara tun daga nan duniya kafin a je lahira, to haka ma duk ma duk mai girman kai idan bai tuba ba, za a kore shi daga rahamar Allah kuma a qasqantar da shi tun daga nan duniya kafin a je lahira. Allah ka tsare mu.
Misali na biyu:
Hadisi ya tabbata daga Salamtu Bn Akwa’i (rain) ya ce: Haqiqa wani mutum ya ci abinci a gaban Manzon Allah (saw) da hannunsa na hagu, sai Manzon Allah (saw) ya ce ma sa: “ka ci da damanka." Sai ya ce: “ba zan iya ba.” Sai Manzon Allah (saw) ya ce: “ba za ka iya din ba.” Salamatu ya ce: “babu abin da ya hana shi sai girman kai. Daga wannan lokaci bai qara iya daga hannunsa zuwa bakinsa ba." - (Musulim: 2021.
Kaga shi ma wannan Allah ya yi ma sa uquba da kasa daga hannunsa sakamakon girman kan da ya yi.
Misali na uku:
Baban Al-qasim (saw) ya ce: ya yin da wani mutum yake tafiya, yana sanye da tufafi sama da qasa (riga da kwarjalle ko riga da wando), yana jiji da kansa, ya taje gashin sa, ya na nuna isa da qasaita saboda girman kai, sai Allah ya nutsar da shi a cikin qasa, yana ci gaba da yin qasa har zuwa tashin qiyama.” - (Bukhari: 5789, Muslim: 2088).
Duk wadannan misalan su na nuna uquba da tabewa da mai girman kai ya ke haduwa da su tun a nan duniya kafin lahira in har bai tuba ba.
iii) Masu girman kai su na kasancewa a cikin fushin Allah tun daga nan duniya har su hadu da Allah ranar alqiyama. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (rain) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: mutane hudu Allah Madaukakin Sarki yana fushi da su, dan kasuwa mai yawan rantsuwa, da talaka mai girman kai da tsoho mazinaci da shugaba azzalumi." - (Hadisi ne Sahihi, Sunanun Nasai: 2567).
Haka kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Umar (ra) ya ce: Na ji Manzon Allah (saw) yana cewa: “Babu wani mutum da zai kambama kansa da jiji da kai, ko yake taqama a cikin tafiyarsa, face ya hadu da Allah alhali yana mai fushi da shi." - (Hakim ne ya rawaito shi, kuma Hafiz Ibn Hajar a cikin Bulugul Maram, hadisi na 1553 ya ce mazajen Isnadinsa nagartattu ne).
Sai mun hadu a fitowa ta 15 da yardar Allah.
* *
Comments
Post a Comment