GIRMAN KAI KASHI NA SHABAKWAI
GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.
Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.
TAMBAYA TA 8:
Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?
Ci gaba...
2- Mataki na biyu: Jin tsoron Allah da ganin girmansa.
Duk mutumin da yake jin tsoron Allah da ganin girmansa ba zai siffantu da girman kai da ji-ji-da-kai da taqama ba, domin jin tsoron Allah da ganin girmansa, zai sanya ma sa ya riqa karvar gaskiya, kuma ba zai kasance mai wulaqanta mutane ba.
A nan mutum zai riqa qoqarin bin umarnin Allah da Manzon sa (saw) wajen yin abin da su ka yi umarni da shi. Duk wanda ya siffantu da haka kuwa, ba zai riqa wulqanta mutane ko ya daga mu su kai ko ya nuna mu su isa ba. Domin hadisi ya tabbata daga Iyadh bn Himar (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya yi mini wahayi akan ku riqa qan-qan da kai, har ya zamanto wani bai yi alfahari akan wani ba. kuma wani bai wuce gona da iri akan wani ba." - (Muslim: 7104).
Haka kuma mai girman kai, idan ya tuba ya luzumci tsoron Allah da ganin girmansa, kuma ya dubi kyakkyawar rayuwar managartan bayin Allah abar misali musamman jagoransu kuma shugabansu Annabi Muhammad (saw) zai san girman kai ba abin yi ba ne. Domin Manzon Allah (saw) duk da kasancewar sa sama da dukkanin halittun Allah a duniya da gobe qiyama, ya fi kowa qanqanda kai (saw).
Kaxan daga misalin tawadhu'unsa (saw) shi ne:
Hadisi ya tabbata daga sayyadina Umar da Abdullahi bn Abbas Allah ya qara yarda a gare su sun ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Ka da ku kambama ni kamar yadda Nasara (kirista) su ka kambama Annabi Isa an Maryam, ni bawan Allah ne don haka ku ce min bawan Allah kuma Manzonsa." (Bukari: 3189).
Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: wata mace [mai tabin hankali] ta zo wajen Manzon Allah (saw) ya na cikin mutane ta ce ya ma'aikin Allah ina da Magana da kai, sai Manzon Allah (saw) ya ce: “Ya Babar wane! ki duba duk inda ki ke so mu zauna a cikin hanyoyin madina zan zauna na saurare ki" sai ta nemi wuri ta zauna kuma Manzon Allah (saw) ya zauna ya saurare ta har ta gama bayaninta". (Bukhari ya anbace shi Mu'allaqan hadisi na 6072, Muslim: 4293).
Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: “Haqiqa Manzon Allah (saw) ya ga Majina a jikin bangon masallaci daga sai ya sa hannunsa mai albarka ya gogeta."
Haka nan an karbo daga Anas bn Malik (ra) ya ce: “Manzon Allah (saw) ya kasance ana gayyatarsa izuwa walimar da ba a tanadi komai a cikinta ba sai gurasar sha'ir da kakiden da ya fara bashi da fumfuna kuma ya amsa gayyatar, kuma haqiqa ya bayar da jinginar sulkensa ga wani bayahude ya karbi abinci, bai samu ya biya ba har ya koma ga Allah." (Musnad u Abu Ya'ala al mausuli, hadisi (3904)
Har ila yau an karbo wani hadisi daga Anas bn Malik (ra) ya ce: "Babu wanda ya fi soyuwa a wajensu kamar Manzon Allah (saw). Ya ce sun kasance idan su ka ganshi ba sa miqewa tsaye saboda sun san ba ya son haka." (Adabul Mufrad: 946. Da sunan at-Tirmizi: 2754).
Qanqan da kansa (saw) bai tsaya ga nan ba. Barima Manzon Allah (saw) ya kasance yana taya iyalansa ayyukan gida, yana cin abinci tare da sahabbansa, yana zama tare da talakawa yana shiga kasuwa don yin ciniki ko siyayya.
Hadisi ya tabbata daga Aswad Bin Yazid (ra) ya ce: Na tambayi Nana A'ishah (R.A), Me Manzon Allah (saw) ya kasance yana yi a cikin gidansa? Sai ta ce: “Ya kasance yana taya iyalansa aiyukan gida. Idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah." - (Bukhari: 676).
Kuma hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (ra), ya ce: Manzon Allah (saw) yace: “Babu wani Annabi da Allah ya aiko face ya yi kiwon dabbobi." Sai sahabbansa suka ce: “kai ma kayi?” Sai ya ce: “Na'am! Na kasance ina kiwon dabbobi ga mutanen Makka, su na biya na wasu ‘yan sululluka.” - (Bukhari: 2262).
A wani hadisin kuma daga Abu Hurairah (ra) har ila yau ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: “Idan da za a gayyace ni walima wadda za a yi da qwaurin dabba zan amsa (gayyatar), kuma idan da za a yi mini kyautar qwaurin dabba zan amsa.” - (Bukhari: 2568).
Babban sahabin nan, kuma hadimin Manzon Allah (saw) , Anas dan Malik (ra) ya ce: “Haqiqa shi ya wuce yara, sai ya yi mu su sallama, sai ya ce: (na yi haka ne don) Manzon Allah ya kasance yana aikata hakan." - (Bukhari: 6247)
Duk wadannan hadisai da mu ka ambata, da sauransu, su na nuna mana tawadu'un sa (saw) duk da kasancewar fiyayyen halitta. To ina kuma ga wanda ya ke ba kowa ba ba annabi ba kuma Manzo ba? Lallai wannan shi ya fi kamata ya zama mai qanqan da kai domin koyi da fiyayyen halitta Annabinmu Muhammad (saw). Allah ka sa mu dace, amin.
Sai mun hadu a fitowa ta 18 da yardar Allah.
Comments
Post a Comment