KYAKYAWAN KARSHE KASHI NA DAYA

Dukkan yabo da godiya da kirari da jinjina sun tabbata ga Allah Ta'ala, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga ManzonSa, Alayensa da Sahabbansa da mutanen gidansa da wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

Bayan haka, 'Yan uwa ko shakka babu, yana daga cikin Rahamar Allah Ta'ala Ya kasance bawa ya dace da kyakkyawar karshe a rayuwarsa.

Da haka ne ya sanya na ga dacewar in janyo hankalin kaina da sauran' yan uwana Musulmi domin fatan dacewa da wannan tagomashi.

MENE NE KYAKKYAWAN KARSHE?: Kyakkyawan karshe, shi ne ya kasance Allah Ta'ala Ya datar da Bawa kafin mutuwar shi ya zamto ya nisanci dukkan wani abu da yake fusata Allah, da tuba daga zunubai da sabo, sannan ya zamto Bawa ya fuskanci ayyukan da'a da ayyuka na alheri, sannan ya zamto Allah Ta'ala Ya karbi rayuwar Mutum a haka.

Daga cikin abin da yake nuni akan abin da muka ambata, shi ne hadisin da ya inganta daga Anas Bn Malik, Allah Ta'ala Ya kara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, ya ce: "Idan Allah Ta'ala Ya na nufin bawanSa da alheri, sai ya yi aiki da shi" sai suka ce: ta yaya (Allah) Zai yi aiki da shi?, sai ya ce: "Zai datar da shi da ayyuka nagari kafin mutuwarsa".

Imamu Ahmad ne ya ruwaito 11625 da Imamut Tirmizy 2142 sannan Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy ya inganta a cikin Silsilatus Sahihah 1334.

Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Idan Allah Mai Girma da Daukaka Yana nufin Bawa da alheri, sai ya dogar da shi" sai aka ce ya zai dogar da shi?, sai ya ce: "Allah Mai Girma da Daukaka zai bude masa aiki na alheri wanda zai rinka yi kafin mutuwarsa, sannan a dauki ransa yana wannan aiki". Imamu Ahmad ya ruwaito 17330 kuma Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy ya inganta a cikin Silsilatus Sahihah 1114.

Kyakkyawan karshe yana da alamomi...

Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA