GATA NAN GATA NAN KU

GA TA NAN, GA TA NANKU:
TAZO MUJITA:

Akwai wani mutum da ke zaune a wani gari mai suna Raqumawa tare da matarsa da 'ya'yansu su goma sha daya.

Rannan sai matarsa ta haifi da namiji, ya zama na goma sha biyu.

Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana, ya ce wa uwarsa: "Kada ma a yi wahalar rada mini suna, domin sunana dan-kutun-gayya." Ya qara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinqa hawa.

dan.jpg

Iyayen suka yi haka, jama'ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen dan-kutun-gayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da 'ya'yanta su goma sha biyu.

Sai dan-kutun-gayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isar su gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfida, suka zauna; ta kawo musu abinci mai dadi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan, ba su san cewa matar nan Dodanniya ce ba.

Suka zauna suna ta hira kamar yadda suka saba kullum. Kuma duk sadda suka yi barci a gidan, Dodanniyar kan tashe su, su tafi gida. Ashe duk wannan dabara ce take yi don su saki jiki da ita, wata rana ta cinye su. Kuma tuni ta yi tanadin manyan tukwanen dafa su, ta sha romo. To, a daren da suka je tare da dan-kutun-gayya ma, duk sauran sun yi barci in ban da shi.

Can cikin dare sai ya ji ana wasa wuqa, sai ya ce a ransa: "A'a, lafiya kuwa?" Sai ya kwanta ya yi kamar yana barci. Da aka dan jima sai ya ga Dodanniya tana sanda, har ta shiga wajen yara. Da ya ga lallai ta nufi yayyensa, sai ya yi tari da qarfi. Da ta ji tarinsa, sai ta koma da sauri.

Da aka jima, sai ta sake dawowa; shi kuwa dan-kutun-gayya ya qara yin tari, ta koma.

A zuwanta na uku ne fa da ta ji tarin dan-kutun-gayya, sai ta boye wuqar ta leqo ta ce: "Kai dan samari ba ka barci ne?" Sai ya ce: "Ai ni ba na barci in ba a kan rairayin qorama mai sanyi ba." Da ta ji haka, sai ta dauki masaki ta tafi neman rairayin qorama. Kafin ta dawo sai dan-kutun-gayya ya fito da wata 'yar batta, ya bude bakinta, ya zazzago wani magani, ya matsa kusa da wutar da ta hura, ya barbada maganin nan a cikin wutar, sai wani hayaqi ya tashi. Da 'ya'yan Dodanniya da yayyensa suka shaqi wannan hayaqi, sai barcin da suke yi ya qara nauyi.

Nan da nan dan-kutun-gayya a cikin sauri irin na hatsabiban mutane ya bi ya tube wa 'ya'yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa. Kuma ya tube wa yayyensa nasu kayan, ya sanya wa 'ya'yan Dodanniyar. Da ya gama wannan aiki sarai, sai ya kwanta, ya shiga jira.

Can sai Dodanniya ta dawo, ta kawo rairayi ta ba dan-kutun-gayya. Sai ya ce: "Yawwa Iya, na gode. Yanzu zan yi barci." Da aka jima sai Dodanniya ta dawo da wata sharbebiyar wuqarta a hannu, ta iske dan-kutun-gayya ya yi barci. Nan da nan cikin gaggawa da qeta ta bi duk 'ya'yanta ta yanke, tana zaton samarin da sukan je hira gidanta ne.

Amma ba ta yanka dan-kutun-gayya ba saboda ta ga shi qarami ne. Ta qyale shi, da nufin kiwata shi ya yi qiba. Da Dodanniya ta fita za ta fara shirin kwashe naman da take zato ta samu, sai dan-kutun-gayya ya zaro battar nan tasa ya sake barbada garin maganin nasa a kan wuta.

Kafin qifta ido, hayaqi ya murtuke daki. Cikin gaggawa ya tashi yayyensa, ya gaya musu abin da ya faru, kuma ya ce su yi maza-maza su gudu gida. Ya ce shi zai bi su da gari ya waye, kada su jira shi. Take suka sulale, suka gudu. Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo za ta fara tattara wadanda ta yanka, a zatonta 'yan uwan dan-kutun-gayya ne. Yana ganin ta sai ya kada battarsa, sai ga ragonsa ya zo ya harari Dodanniya, yana yi mata kallon raini ya ce: "To, wadannan fa 'ya'yanki ne kika yanka, ba 'yan uwana ba." Da ta lura da haka, sai ranta ya baci ta yi wani qaraji, ta yi wuf ta kai masa bara za ta cafke shi, sai ya baude. Ta sake rarumo shi, amma sai ya dare bayan ragonsa. Rago kuwa kamar ya san zancen, sai ya kama sukuwa kamar walqiya, ya tsere mata fintinkau, ya bar ta sororo a cikin baqin ciki. Dodanniya ta dauko dan magurjinta na tsafi, ta bi 'ya'yanta tana buga wa kowannensu a ka.

Nan da nan namansu ya zama na tumakai, ta soye suka cinye ita da autarta. Daga nan ta yi alqawari sai ta rama qetar da dan-kutun-gayya ya yi mata

Bayan 'yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su dan-kutun-gayya ta rikide ta zama kanya kuma ta kwatsa 'ya'ya da yawa, har sun kusa nuna. Da yaran gari suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, sai wasu daga cikinsu suka dinga kado 'ya'yan suna sha.

Har dai wata rana yara da yawa suka hau kanta suna diba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama ya samu. Sai ta umurce ta da ta wanke tukwane. Tana kuwa cikin wanke tukwane sai dan-kutun-gayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikida, ya zama dan maraqi, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, watau dai yana yi mata barna.

Yana cikin wannan barna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori dan maraqin mai yi mata barna. Da ya ga sun doshe shi sai ya qi gudu, amma da suka zo dab da shi, sai ya dan gudu ya dan matsa gaba kadan kuma ya ci gaba da barna. Yara kuma suka dan matsa kusa da shi, ya dan qara gaba kadan.

Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikida ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu. Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheqa da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru.

Shi kuwa dan-kutun-gayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: "Na kubutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu. Ni ne dan-kutun-gayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada."

Wannan abu da dan-kutun-gayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da qulla yadda za ta dauki fansa a kansa.

Ana nan sai Dodanniya ta rikida, ta zama mace kyakkyawar gaske, ta dauki wani adudu ta je cin kasuwa. Masoya suka yi ca a kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura sai wanda ya bude wannan adudun. Samari da yawa suka gwada amma duk suka kasa. Bayan 'yan kwanaki, har samari sun fid da rai, sai daya daga cikin yayyen dan-kutun-gayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta. Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada bude adudun zai bude.

Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya bude, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata.

Aka daura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa. Amma bayan 'yan kwanaki sai ta qwaqwale wa mijin ido daya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya. Dan-kutun-gayya da jin wannan aika- aikar, ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya quduri aniyar sai ya dauko fansar abin da ta yi wa yayansa.

Sai ya rikida ya zama Bafilatana, ya dauki nono, ya je gidanta talla. Da isar sa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba.

Da haka har Dodanniya ta saba da Bafilatana qwarai da gaske. Wata rana sai Bafilatana, watau dan-kumale ya zo gidan Dodanniya a fusace. Dodanniya ta tambayi Bafilatana dalilin fushinta, sai ta ce: "Wani mutum wai shi dan-kutun-gayya yake zuwa yana kashe mana shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa qarewa." Dodanniya ta ce: "Ke ba sunansa dan-kumale ba, sunansa dan-kutun-gayya.

Mugun mutum ne. Ba shanunku kadai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni 'ya'yana goma sha daya ya sa na kashe.

Kwanan nan ma na kusa makantar da dan uwansa. Kin ga idon yayansa da na qwaqule." Sai Bafilatana ta ce: "Tir da ganin idon lalatacce." Sai Dodanniya ta ce: "Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye." Bafilatana ta ce: "Kash, da idon nan zai yi wa qanena daidai da kin ba ni shi. Shekaranjiya saniya ta harbi idonsa daya ya fashe ya tsiyaye." Cikin doki da qeta Dodanniya ta ce: "Af, don wannan ai sai in ba ki." Da jin haka sai Bafilatana ta yi farat ta ce: "Ai ko na gode." Dodanniya ta qara yiwa Bafilatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masa idon, ta ce: "A nemo qwayayen kifi guda bakwai da hantar baqin kare da kiyashi guda bakwai da kaucin marke; a shanya su bushe, sai a niqa, a rinqa sa masa a gurbin idon har kwana uku.

A rana ta hudu sai a sa idon, zai zauna daram." Bafilatana, watau dan-kutun-gayya ta amshi ido, ta yi godiya. Da ta gusa kadan sai ta tube kayan Fulani, sai ga dan-kutun-gayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo ya ce: "Kin ga ni ne dan-kutun-gayya." Sai ya yi wani hatsabibanci ya bata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko'ina ba sai gida.

Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma ya zauna daram, kamar ba a taba qwaqule shi ba.

Rannan kuma sai Dodanniya ta rikida ta zama kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko'ina ba sai gidan su dan-kutun-gayya.

Da shigarta sai ta iske shi yana barci, sai ta lababa, har ta kai kusa da shimfidarsa. Sai ta yi wani karatu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama bera, sai ta dauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a quryar daki.

Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum. Ita kuma ta rikida ta zama mutum, sai ta harare shi, fuskarta murtuk, tana cike da fushi, ta ce: "dank-utun-gayya, yau fa ga ni ga ka, qaryarka ta qare." Dan-kutun-gayya bai tsorata ba kuma bai ce mata komai ba. Can da Dodanniya ta dan huta sai ta sa autarta tsaron dan-kutun-gayya; ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi.

Tafiyarta ke da wuya sai dan-kutun-gayya ya yi wa 'yar auta dabara, ya karbe kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa.

Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana kwaikwayon maganar 'yar auta, yana yi mata maraba.

Bayan wani dan lokaci kuma sai ga 'yar a cikin kayan dan-kutun-gayya tana yi mata maraba. Sai dan-kutun-gayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: "Ga munafukin nan dan-kutun-gayya yana nunawa wai shi ne ni 'yar autarki har da cewa, Sannu da zuwa inna.' Yau dai qaryarsa ta qare." Sai Dodanniya ta ce: "Lallai kam, bar ni da lalatacce!" Nan take ta yi wuf ta shaqo 'yarta, ta sa wuqa ta yanka. Tana gama yanka autarta sai dan-kutun-gayya ya buga tsalle gefe, ya kwance zannuwan da ya daura, ya dubi Dodanniyar nan ya ce: "'Yar auta kika yanka, ni ko ni ne dan-kutun-gayya gwanin gayya.

Na yi miki gayyar tawa!" Yana gama fada mata haka sai ya yi wal, ya bace.

Dodanniya ta kama 'yarta ta tube kayan jikinta, sai ta ga lallai kuwa autarta ce ta yanka. Nan take sai ta hadiyi zuciya ta mutu.

Qurunqus! Qarshen wannan tatsuniya ke nan, kuma tana dauke da darussa kamar haka:

1. Qaunar juna da son 'yan uwa kan qara wa juna danqon zumunci, kuma ya kubutar da su daga duk wani sharrin maqetaci, kamar dai yadda dan-kutun-gayya da 'yan uwansa suka tsira daga Dodanniya.

2. Haka kuma, tatsuniyar nan ta fassara mana Karin maganar nan da ke cewa, mugunta fitsarin faqo ce, wanda ya yi ta take koma mawa kansa.

Zaka iya tunani wani abu wada tatsuniyar nan ta koya mana?????

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA