GIRMAN KAI KASHI NA SHA TARA

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

Wallafar: Shaikh Abdulwahhāb Abdullah.

TAMBAYA TA 8:

Wadanne hanyoyi mutumin da yake da girman kai ko jiji da kai ko taqama ko alfahari zai bi don rabuwa da su?

Ci gaba...

3 - Mai girman kai don ya na da ilimi: Duk wanda yake girman kai don ilimin da Allah ya bashi, kuma yake son Allah ya raba shi da wannan girman kan, sai ya kalli abubuwa kamar haka:

Abu na farko sai ya kalli cewa abin da bai sani ba ya fi abin da ya sani yawa, kuma akwai daruruwan mutane da su ka fishi ilimi nesa ba kusa ba. Kuma ya kalli misalin Annabi Musa (as), a lokacin da aka tambaye shi wane ne mafi ilimi a ban qasa? Sai ya ce: “ni ne." kuma Ya fadi haka ne saboda ya na da yaqini cewashi Annabi ne Mursali, a lokacinsa babu wanda ya ke da sani kamrsa. Amma duk da haka sai da Allah Madaukakin Sarki ya jarrabe shi, ya umarce shi da ya je mahadar koguna biyu inda a nan ne ya hadu da Khadir. Haqiqa yadda qissarsu ta kasance, akwai izina ga duk mai hankali da Allah ya ba shi ilimi akan kada ya dogara da abinda ya sani sai dai ya maida Ilimi zuwa ga Allah.

Abu na biyu shi ne; mai ilimi ya kalli tsawatarwar da Allah Madaukakin Sarki ya yi akan girman kai, kuma ya dubi narkon da Allah ya tanada don ma su wannan hali da jan kunnen da ya yi akai. Kuma mai girman kai da taqama don ilimi ya kalli qarshensa, domin akwai ranar mutuwa, imma ya yi kyakkyawan qarshe ya sami babban rabo, ko kuma ya yi mummunan qarshe, ya tabe, ya yi asara. Haqiqa kyakkyawan qarshe yana tabbata ne ga masu kiyaye dokokin Allah. Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “Haqiqa kyakkyawan qarshe ya tabbata ga ma su taqawa." - (Suratul Kasas, aya ta 83).

Kuma mai ilimi ko wane iri ne ya kalli cewa shi fa abin misali ne a gurin wasu, abin da yake aikatawa shi wasu za su kwaiqwaya, kuma Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ya sunnanta wa mutane wata mummunar hanya; laifinsa yana kansa da kuma laifin wanda ya yi aiki da ita bayan sa, ba tare da an tauye mu su komai a cikin laifinsu ba." - (Muslim) 1017).

Don haka, lallai wadanda Allah ya ba su ilimi, su ji tsoron Allah, su kiyayi wannan mummunar dabia don kada iliminsu ya zamanto musu asara duniya da lahira. Allah ya kiyaye mu baki daya.

4- Mai yin girman kai don mulki ko wata sarauta da Allah ya ba shi:

In har yana son magance wannan, sai ya kalli wadanda yake mulkarsu, akwai wadanda sun fi shi ilimi, wadansu sun fi shi hikima, wadansu sun fi shi qarfi, wadansu sun fi shi kyawun halitta, wadansu sun fi shi dukiya, uwa uba wadansu sun fi shi tsoron Allah da riqo da addini.

Ashe Ubangiji Madaukakin Sarki da ya ba shi wannan mulkin ba don ya fi kowa ba ne, sai dai kawai don ya jarrabe shi, a cikin rayuwarsa ya ga yadda zai yi.

Har ila yau, ya yi izina da lura, akwai wadanda sun fi shi jin mulki da jin sarauta, sun fi shi iko, amma yanzu su na cikin kabari sai abin da suka aikata, da shi za a saka musu. Ya tuna ranar da za a sa shi a cikin likkafani a binne shi a qarqashin qasa, ya ruve ya zama abincin tsutsa.

Idan ya yi izina da wadannan abubuwa da su ka gabata sai ya tuba zuwa ga Allah (swt), ya yi nadamar abin da ya aikata a baya tun kafin ajali ya zo ma sa. Ko Allah ya jarrabe shi kafin mutuwa a kwace mulkin a wulaqanta shi a kulle shi a kurkuku da abinda ya yi kama da haka, Allah Maxaukakin Sarki ya ce: Ka ce: "Ya Allah mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda ka ga dama, kuma kana qwace mulki daga wanda ka ga dama, kuma kana daukaka wanda ka ga dama, kuma kana qasqantar da wanda ka ga dama. Dukkanin alheri a hannunka yake. Haqiqa kai ne mai iko akan dukkan komai."

Allah ya kare mu daga sharrin girman kai.

5- Mai yin girman kai don Allah ya ba shi qarfi na gangar jiki: Lallai wannan ya sani cewa: duk qarfin sa ba zai buwayi Allah ba, kuma ba zai tsinana ma sa komai ba, kamar yadda qarfi bai tsinanawa Adawa da Samudawa komai ba.

Mai wannan hali ya sani cewa Allah ne ya ba shi wannan qarfin, kuma idan ya so zai karbe shi lokaci daya kamar yadda ake ganin misali a gurin marasa lafiya da tsofaffi. Kuma mutum zai gane cewa qarfinsa ba komai ba ne idan ya kalli manyan dabbobi wadanda sun fi shi qarfi, amma Allah ya dora mutum akansu. Kuma ya kalli qananan qwari wadanda kan addabe shi duk da qarfin na sa. Kamar sauro ko cinnaka su cije shi, ko quda ya shigar ma sa maqogwaro, ko kiyashi ya shigar ma sa kunne. Ba tare da qarfin na sa ya amfana ma sa komai wajen hana su ba.

Yin wannan tunanin zai taimakawa mai girman kai ya daina in Allah ya yarda. Allah ya fahimtar da mu baki daya.

Sai mun hadu a fitowa ta 20 da yardar Allah.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA