DARENKA NA FARKO ACIKIN QABARINK

DARENKA NA FARKO ACIKIN QABARINK

'Dan uwa, duk abinda zaka karanta din nan babu tatsuniya ko kokwanto acikinsa.

An tattaro bayanin ne daga Sahihan Hadisai na Manzon Allah (saww) wadanda Manyan Malamai suna tattaro acikin litattafansu.

Darenka na farko acikin Qabarinka shine dare mafi razani da firgitarwa daga cikin dukkan darare.. Hakika tun lokacin da suka zo suka binneka, Idan sun ajiyeka agefen Qabarinka, Shi kansa Qabarin zai yi magana dakai.

Zai tambayeka shin Mai kake gani acikinsa?? Zaka ce masa ai babu komai. Shi kuma zai ce maka, to duk abinda ka gani na alkhairi ko Sharri, to kaine kazo da abinka!!! Idan kai mutumin banza ne mai bin son zuciyarsa, mai biyewa Sha'awarsa, To shaitan ya riga yasan ya gama dakai. Don haka zai zo gefen Qabarinka yana yi maka dariyar Mugunta..

Idan kuwa ka zamanto mutumin Kirki mai tsoron Allah, mai Halayen Kirki, To tun daga mutuwarka shaitan zai rika tsula kuka da eehu wai saboda bai samu damar dulmiyar dakai cikin hallaka ba. Idan sun gama binneka, Allah zai dawo maka da ruhinka cikin jikinka.

Nan take zaka rika jin maganganun 'Yan uwanka amma babu damar ka amsa musu. Kana jin takun takalminsu amma babu damar ka tashi ka bisu!!! Idan kai Mumini ne cikakke, Nan take zaka ga wasu Mala'iku farare masu kyawawan kamanni zasu shigo har cikin Qabarinka. Zasu yi maka sallama sannan su zaunar dakai su tambayeka :

"WANENE UBANGIJINKA? MENENE ADDININKA? KUMA MAI ZAKA CE GAME DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW)

- Zasu nuna maka siffarsa" Zaka basu cikakkiyar amsa: "Allah ne Ubangijina, Musulunci ne addinina. Kuma Annabi Muhammadu (saww) Shine Manzona nayi imani dashi. Shine ya isar min da sakon Ubangiji".

Nan take Mala'ikun zasuyi maka kyawawan kalamai. Za'a nuna maka gidanka na Aljannah kuma za'a bude maka wata Kofa wacce ta nan ne ni'imomin cikinta zasu rika shigo maka har zuwa ranar tashin Alqiyamah.

Idan kuma Kafiri ne ko Munafiki (Mai imani abaki, amma zuciyarsa babu Soyayyar Ma'aiki saww) Ko kuma mai bin son zuciyarsa, awannan lokacin zai ga wasu Mala'iku Baqaqe Wuluk masu mummunar kamanni..

Zasu shigo har cikin Qabarinsa, su tasheshi su zaunar dashi Sannan su tambayeshi

"WANENE UBANGIJINKA, MENENE ADDININKA, KUMA MAI ZAKA CE DANGANE DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW)"

Zai ce "Aah!! Aah!! Ban sani ba! Ban sani ba!!" Sai Mala'iku su fara Jibgarsa da wata irin gudumar Baqin Qarfe wacce ba zata misaltu ba..

Idan ya kwarara Eehu sai dukkan halittu sunji shi.

in banda mutane da Aljanu!!! 'Wannan ranar tana nan zuwa garemu baki daya. Dani dakai, Dake, daku, duk Sai mutuwa ta riskemu..

Kuma sai munyi kwanciyar Qabari.. Kuma sai an tambayemu akan ayyukanmu..

Shin sau nawa kake tuna wannan ranar a kullum?? Shin kana yin tanadi domin zuwanta?? Ko kuma tanadin gyaran duniyarka kawai kakeyi?? Ni dai na duba cikin ayyukana ban ga wani abinda zan doshi Allah dashi ba.. Sai dai Son Allah da Manzonsa (saww). Ya Allah afuwarka muke kwadayi.. Rahamarka muke roko, Falalarka na muke sa rai..

Ya Allah ka gafarta mana ka gafarta ma Iyayenmu da Malumanmu da iyalanmu da dukkan Musulmai maza da mata.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA