CIN HANCI DA RASHAWA

YAKI DA RASHAWA

Da 'Yan Jam'iyyar Adawa Buhari Yake Yaki, Inji Tanko Yakasai

Fitaccen dan siyasan nan da ke jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ake kama 'yan jam'iyyar adawa da suna yaki da rashawa a gwamnatinsa.

A jawabin da ya fitar a jiya, Dattijo Yakasai, ya kawo misali da kama tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da aka yi da kuma sauran 'yan jam'iyyar adawa da aka kama.

Ya ce babbar damuwarsa a yanzu shine yadda Buhari ke neman dawo da salon mulkin sa na soja a wannan gwamnati ta siyasa.

Ya kuma yi kira ga shugaban kasan da ya gudanar da adalci ga al'ummar Najeriya a shirin da yake na yakar rashawa. .

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA